BABI NA 15

262 20 0
                                    

FEENAT!!!

BY MAMNHANEEF

2016

39

***Nafesa kuwa bata karabi takan wayar ba taci gaba da girkin ta takammala ta zuba a fulas ta jere su cikin tire harda lemon yayan itacuwa masu kara lafiya data tace masa, saida takoma daki ta zuro hijabi sannan tanufi dakin saukar bakin sa Wanda yake yada zango acan duk rana irin wannan da ranar da babu futa kasuwa sabida bakin dake kai kawo duk ranar daya ke gida, wasu abokan kasuwanci ne wasu kuma yan maulane yynda wasu kuma sunzo Neman taimako ne.

ta kofar data bulla tacikin gidan tabiyo saida aka bata umarnin shigowa tukan sannan ta tura kofar tashiga da Sallama kanta sunkiye don ganin ba Abban tane kadai ba a dakin, da faraar sa ya tarbeta ya dago hannu sama ya tari tiren hannun ta yana fadin"Har kinyi me?sannu da kokari yar gidan Abban ta, Murmushi tayi kan tace"harna gama Abba yayi dd sosai Inkaci sai kunnan ka yacire don dadi Abba, gaba dai sukai murmushi yayin da ta juya tana gaishe da bakin Abbanna ta, Kasan cewar bamai kurilla bace yasa Sam bata gane suwaye a girin ba,

mikewar da zatai ta juya danta fita ta kofar waje ta karbi sakon ta gurin mai gadin su sai kawai ganin mutum tayi a zaune ya tsura mata ido aikwa  sukai ido hudu da Dr Ismail Wanda tun shigowar ta yazuba mata ido yana sauke ajiyar zuciya baisamu nutsuwar zuci ba saida yagan ta sannan yaji ransa Yy masa dadi barema dayaga fararen hakoran ta a waje a yayinda take zolayar Abban ta. da squri ta janye idon ta dg cikin nasa gaban ta yana faduwa, tayi saurin barin falon cikin sassarfa.

gaban ta har yanzu faduwa yake tsigar jikin ta kuwa sai tashi take, wani Abu taji yana fuzgar ta tamkar wacce akaiwa Allura, kwayar idon sa kuwa itake dawo mata kmr har yanzu kallon juna suke, da wannan tunanin tashige dakin ta takwanta tareda nitsewa cikin bargo tana tambayar kanta shin waima meyakawo Dr gurin Abban ta?Wannan tambayar ita tafi tsaya mata a karshema ta watsar da lamarun illa kallon da Dr Ismail yayi mata yaki kankaruwa cikin idonta da zarar ta tuna tsigar jikin ta zata tashi, harbatasan tunawa.

A daran ranar ne takoma gurin Abban ta tana tambayar sa waime Dr Ismail yazoyi gurin sa? Batare dq bata lokaci ba kai tsaye yabata amsa"sunzo Neman irine agurin Mu"Neman iri kuma Abba?"eh sunxo neman auren ki nikuma nayi na am da bukatar su natura su gurin Baffan Ku( Babban wan hajiya Hajara momyn ta Wanda yake zaune a unguwar hotoro shima kasuwancin yakawoshi kano dg baya yakwaso iyalansa sukadawo garin kano, kar mai karatu ya manta Alh Abdalla da haj Hajara abokan wasane auren xuminci sukai) jitai kmr guduma Abban ta yabuga mata cikin rawar murya tace"Abba nifa bamuyi wannan mganar dashiba asalima wata mgnar soyaiya bata taba hadani dashi ba ni rabon da nasashi a idona ma namanta kawai sqiyazo Yy mgana kai tsaye? kumani Abba saina gama karatu zanfara soyaiya balle kuma aure.

ko ajikin sa hannu ma yasa ya dauko cake din dake gaban sa yace"aidama shi lamarin aure ko babu soyaiya anayin sa mutanen dama saidai kawai kiga ankaiwa mutum amarya batare da tasanshi koshi yasan taba ai indai akasamu kyawun hali da kuma rufin asiri ko bakai istihara ba sai kawai kiga anyi auren, balle ma wasu suna son juna muskilan ci da Jan aji yakesawa suyi nauyin baki wajen furtawa sai kuma anyi auren kijisu shuru makatau wannan su ake kira da muskilan masoya wayan da gulma tayiwa,aibai karasa ba ta tuntsire da dariya mao hadeda kuka, shima dariyar yake mata".                     40.                                    """" Tasan da ita yake shiyasa tayi saurin kawar da mgnar da cewa"Abba nayi istiharar ai kuma ni" shuru tayi takasa karasawa shikuwa murmushin manya yayi kan yace"karki batawa kanki lokaci Nafisa, Abinda nakeso dake kiyi kokarin gyara tsakanin ki Dr Ismail amma mganar bakyason sa waye waye duk bata tasoba ni banga abinda ismail yayi miki da zafi haka ba, dahar zaki dinga kokarin yakice shi takarfin tsiya bayan yariga yaginu cikin ranki karya kike inkika ce babu shi cikin ranki, tunda kikaki dawowa kifada mini abinda kikagani ko kikaji a ranki akansa bayan kinyi istihara nasan abinda Allah ya nunamin kema shi kika gani, Nafisa zakija dayin Allah ne?Cikin sanyin jiki ta girgiza" ahto to abinda nakeso dake kije ki roki Allah ya dai daita tsakanin ku kuma ki gode masa da irin baiwar da yayi miki karki zama butulu shekara da shekaru muna adduar zabin Allah a gareki yanzu kuma Allah ya qmshi adduar zakiyi wasa da damar ki? Yajima yanai mata nasiha duk jikin ta yayi sanyi bai bartaba saida ya wanke laifin Dr ismail tas na cikin ranta,

FEENAT!!! Where stories live. Discover now