BABI NA 23

397 26 0
                                    

[8/19, 7:17 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!

BY MAMANHANIF

2016

54.

Hauwa tadawo d'akin ta tareda sabon shirin ta yayin da wani sabon zaman lafiya yakuma wanzuwa a gidan, sunkoma kamar yanda suke ada, kama girki aikin gida su suke zagewa suyishi don Dr bai aminta da ajye 'yar aiki ba,

Watan Hawwa biyu da dawowa takuma samun wani cikin amma wannan karon bamai laulayi bane don haka ko girkin da kanta take ba kamar na farko ba da komai saidai ayi mata,

Haka nan suka cigaba da tattalin cikin dake jikin Hawwa, cikin ikon Allah duk kulawar da take samu bai hana cikin zubewa ba, a takaice dai Hawwa tayi b'arin ciki d'an wata uku, ranar da Abjn yafaru daga Dr har Feenat suna asibiti saijin mummunan sak'o sukai a bakin mai gadi wanda yayowa Dr waya yake fad'amasa halin da matar sa ke ciki, wanda shima ihun ta yake jiyowa daga cikin gidan ya shiga ya tardata tana malele kuwa a tsakar falo,

Kansu iso gidan har tayi b'arin cikin wanda sam baiyiwa Dr dadi ba, karshema kasa motsawa yy daga inda yake sai Nafisa ce ta taimaketa tareda bata taimakon da tasan tana buk'ata.

Bayan wata uku.

Zuwa yanzu Hawwa takuma yin wani cikin wanda tun samuwar cikin Dr ya kaita gurin wata babbar likita wacce k'awace gurin Nafisa ta binciki lafiyar ta tareda Abinda ke cikin nata, ta tabbatar musu da komai lafiya dad'in ma lafiya lau take Allah ne ya aiko musu da b'arin,

Nafisa kuwa? Tayi matukar mamaki da Dr ya iya d'aukar Hawwa yakaita wani gurin don neman lafiya bayan yasan itama ba baya bace ta wannan fannin, ko a fuska bata nuna taji Haushin hakan ba don tasan duk daran da dewa akwai ranar dazai gane kuskuren sa,

A yau ne kausar Tsohuwar Aminiyar ta takawo mata ziyara, kusan yini tayi a gidan ita kad'aice wacce tasan wasu daga cikin matsalolin Nafisa don haka da zata taho tun daga gidan ta tayo mata tsarabar kayan d'aa duk da tasan halin mutuniyar ta ba lallai tayi naam da suba,

Ilai kuwa tana bata tsarabar tasaki dariya harda tuntsirawa saima ta maidata sauna a gurin, cikin jin haushi tace"amma dai Nafisa kin iya mannawa mutum inbazaki shaba aisaiki fad'amin amma ni wannan dariyar taki ita tafi bani haushi wlh, nan ta tsaya da dariyar kan tace" yi hak'uri kawata bawai kin karba nayi ba sanin kine kona amsa babu Abinda zanyi dasu gwara ki juya da Abinki wata ran zai miki amfani,najuma ina fad'amiki kausar bana buk'atar k'arin lafiya, na yarda da kaina na Aminta da baiwar da Allah yayi mini, ta katseta" amma dai ba laifi kikai ba inkin kara dasu" Eh banyi laifi ba kuma bance miki hakanan nake zaune ba, ina gyara lafiya ta da Abubuwan da zasu taimaki jikina su karamin kuzari da jini da dai sauran su, Aidan kina bukatar ni ima aiba saikin yi shaye shaye da cuse cuse ba, kinga inkika rike kwai da lipton?Madarar shanu? Madara ta ruwa? Zuma da dabino? Kinga fruits sunfi komai karawa mace ruwan jikin ta,Miski da dai sauran su? To sun isheki karin d'aa ga kuma lafiya da zasu kara miki, basai kinta wahal da kanki kina wahal da mijin ki ba,nan dai suka cigaba da hirar su data dangan ci wannan b'angaren.

A b'angaren Hawwa kuwa? Itakam takara kaimi wajen faranta ran mijin ta, a yau ma bakuwa tayi wacce ta sauke ta a falon su na had'aka, a lokacin Nafisa na kicin tana hadawa Dr girki na musamman wanda tasan yana mutuk'ar so, duk hirar da suke da bakuwar ta tanajin su, yayin da su basusan tana kicin ba don sanda tashiga kicin din Hawwa na d'akin ta,

Bakuwar tata ba wata bace face hajiya Atine kawar innan ta,nan suka cigaba da hirar su bayan ta bata sakon da sukai a waya zata kawo mata, nan tashiga duba kayan tacika da farin cikin ganin su don dama kwana biyu kayan gurin ta sunyi kasa,

Hajiyan ta duba tareda cewa" incedai ko kin had'omin da wannan bakin maganin na roba mai tsinke wanda yake zuwa da takarda da turare?wani murmushi tayi taji hanyar cin kud'i tasamu tace"ca zakimin saka kishiya kuka koba mai tsadar nan ba wanda kika siya tun farkon auren ki? Eh shine hajiya gsky yanada kyau har zance ki kuma kawo min sainaji kuma kin kirashi da wani suna, sunan sa saka kishiya kuka? Dariya tayi kan tace" kwarai kuwa" to nidai na hkr dashi don bazan saka Anty Nafisa kuka ba, mtssw taja tsaki na nawa kuma? Tunfa kina Amarya kika sayeshi sai yanzu kuma kice kaza da kaza? Aiba kukan zaki sata shabe shabe, Abin nufi duk wani Abu dazatayi don mijin ta tofa tayi Abanza kece kawai a gaban goshin sa, inhar kina amfani da saka kishiya kuka to tazama bora,ita dashi saidai kallo kaya jemata to dolece badan.... ba,

FEENAT!!! Where stories live. Discover now