BABI NA 26

304 18 0
                                    

[8/25, 12:49 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!!

BY Mmn Hanif

61

***Babu kunya ko tsoron Allah haka inna ta wanke k'afa ta tafi gidan hajiya wanda rabon ta da zuwa gidan harta manta dama can d'in datake zuwan tatace take kawota tunda Hawwa tasoma cika ta da kudi ta dauke kafar ta saidai su hadu da hajiya a taro shima tana ya tsina ta dage hanci a haka take gaishe su wani zubin ma su dasuke gaba da ita su suke farai mata sannu, kiri kiri tanunawa hajiya tafi zumunci da yan uwanta Wanda suke uwa daya, sabanin hajiya da suke uba daya, duk wani iya shegen datake hajiya kallon ta kawai take don tasan dai ramun k'arya kurarene.

To yau din datazo gidan hajiyan tana cika tana batsewa a dole itaga mai ya kuma anbataran diyar ta, tunda hajiya taga take taken ta tayi banza da ita tama shiga sabgar gaban ta tana kai komo tsakanin tsakar gida da dakin da Nafisa ke ciki, batasan dama hajiyan a ciki take da ita don takaita makura, dama ga laifin datayi mata na rashin zuwa duba Nafisa wacce tayita hidima da Hawwa a lokacin da take nata laulayin koma badan wannan ba ai tayiwa hajiya kara   a matsayin ta yar uwar ta, duk bata duba wannan tazo ba sai yau da rashin mutunci ya kawo ta,

Aikuwa bata bar gidan ba saida hajiya ta wanketa tas duk abubuwan da takeyi wanda bata zaci hajiyan ta sansu ba saida hajiyan ta zaiyano mata su yau kuma ta hana Nafisa futowa ta gaidata hakanan tabar gidan guiwar ta asage tareda mamakin hajiya don bata zaci hajiya zatai mata wannan cin mutunci ba.
[8/25, 2:30 PM] Mamanhaneef: ***Haka nan taja kafa ta Isa gida takira Hawwa ta shaida mata irin cin mutuncin da hajiya tai mata karshe ma tace karta kuma zuwa gidan hajiya itama bazata kara zuwa ba ai zumincin ba dolene ayi da itaba babu ita babu hajiya tunda tanuna mata bare yafi d'an uwa,

Bonono wai rufe kofa da b'arawo.

A b'angaren Hawwa kuwa? Tak'ara kaimi wajen janye Hankalin Dr don taci Alwashin ko Nafisa tadawo bazata bari tajanye Dr daga hannun taba saidai kowa tasa ta fishsheshi, to wani hanzari ba gudu ba kuma a yau sai  Hawwan ta tashi da wani irin ciwon ciki mai azabar zafin gaske har saida tafuta hayyacin ta Dr ya kwashe ta sukai asibiti daga kaeshe akabata magunguna wanda tun a asibitin data sha taji saukin ciwon cikin,tun daga wannan ranar tashiga yin ciwon cikin a tsartsaye ganin tanada magani ko kadan bata damu ba, daga baya ma sai takejin kasan marar ta nai mata ciwo kadan- kadan amma wannan saita dangan tashi da ciwon mara tana zatan ko al'adace zata zo mata,

Duk wannan ciwuwukan bai hanawa Hawwa shan magungunan ta ba bai kuma hanata faranta ran Dr ba koda kuwa tanajin ciwon haka take daurewa duk Dan ta daukewa Dr hankali karyaje gidan hajiya gurin Nafisa,

Wata sabuwa inji Dan caca, a yau kuma Hawwa tashitai da wani azabanban kaikayi wanda ya xarce nada don wancen inta Sosa tanajin dadi wannan kuma data sosa sai kuraje su feso data Sosa kurjin saiya fashe yakama ruwa, hankalin ta yayi matuk'ar tashi gashi Anty Nafisa bata nan don haka ta dafa ganyen magarya da zafin sa tashiga ciki wai a tunanin ta da zafin saiyafi dusashe mata kurajen da suka fashe suke mata axabar radadi,

Tana ihun azabar ciwo tareda zafin ruwan haka ta tura jikin ta ta zauna har ruwan ya huce sannan ta tashi dubawar da zatai taga kafatanin k'urajen sunyi jajur fatar gurin tasalu be gawani jini bak'ik'irin da yake futowa ta k'asan ta, take gaban ta yafad'i tadafe kirjin ta tareda cewa" Nashiga uku,

Batareda b'ata lokaci ba takira wayar Dr a lokacin yana asibiti jin kukan datake ne ya d'aga Hankalin sa yabaro asibitin yazo gidan tunkan ta gamai masa bayanin ya rufeta da Fad'a k'arshe dai ya d'auke ta yakaita  wani prvt asibiti na wata likitan mata wacce ta tab'a dubata tun sanda tayi b'ari na biyu,

Nan likitan tashiga bincikar matsalar ta har saida ta gayyato abokan aikin ta har su uku don su taimaka mata wajen gano matsalar meke damun Hawwa?  Cikin ikon Allah suka gano illar dataiwa kanta don ciwon sanyi yaci k'arfin ta yagama lalata k'asan ta tareda taimakon cuse cusen magungunan data dingayi tareda wanda tadinga bankawa cikin ta su sakai sanadin lalatata gaba d'aya,

Da likitan tanaiwa Dr bayani saida yakusan fad'uwa k'asa don matukar firgici, donshi baitaba cin karo da mace irin Hawwa ba, kina zaune ciwo nacin jikinki amma bazakiyi magana ba sai Abu yaci yacin ye? Nan dai suka taru Sunai masa bayanin a dole saidai ayi mata aiki don mstsalar tashafi har cikin marar ta ba iya waje bane kaf d'inta talalace ciki da waje don haka tana bukatar taimakon gaggawa, nan dai Dr yasa hannu suka tsayar da ranar da zaayi mata aikin haka Dr yafutar da kudade ba Kadan ba don anan asubitin aka kwantar da ita don akwai kulawar da zasu fara bata kan suyi mata aikin,

Innan ta tana zaune sai ganin Dr tayi yazo mata da mummunan labari hakanan ta hada yan kayan ta, tatafi jinyar ta don cikin yan uwanta babu wanda yaje kan Hawwan don itama babu wanda takewa kara cikin su sai Kanada abun hannu ne Abu zai sameka inna taje dubiya ko jaje Amma in bakada arziki baka isheta kallo ba, don haka tarasa wanda zaimata jinyar Hawwan  sai ita tahada kaya ta tafi dama batayi tunanin Hajiya zata ba donko ba Nafisa hajiyan bazata ba don bata manta karan su na rannan ba.

Haka dai akayiwa Hawwa aikin cikin Saa wahala kuwa Hawwa ta dorar da ita wanda  kwatanta tama bazai yuwu ba, Dr kuwa? Ya tsaya tsayin daka don ganin sunbi dokar likita kamar yanda aka shimfid'a musu,, to wani hanzari babu gudu ba kwanan Hawwa biyar da yin aikin tasoma zubar da wanne irin ruwa mai d'an karen wari gashi kore fatau, wannan lamari yatada hankalin likitocin don basu tab'a aikin daya basu matsala irin wannan ba, Nan suka dukufa wajen bincike don su gano matsalar to karancin kayan aiki yasa suka gagara,.

Don haka Dr ya dauketa daga nan ya maidata babban asibitin koyar wa na Malam Aminu Kano, Manyan likito ci sun rufa akan ta Cikin ikon Allah aka sake wanni aikin Hawwa saida ta gwammace mutuwar ta da wannan bak'ar azabar, Haka nan akaci gaba da jinyar ta ba laifi tana samun sauki don jikin ta haryayi dan dama dama, , ranar da zaa sallamo ta kuma sai ta tashi da ciwon ciki tafad daya cikin ta ya kumbura suntum aiki yakomo baya,
[8/25, 4:40 PM] Mamanhaneef: 62

***Iya tashin hankali sungan shi don kuka wiwi inna tayishi harta gaji Hawwa kuwa? Azabar ciwo yasata sai sambatu take, tsananin tausayin ta yasa Dr yafara tunanin ko futa waje zaiyi da ita, nan likito cin suka shawarce shi da yad'an jinkir ta akuma bincikar ta ko Allah zaisa agano tak'amaimai Abinda ke da munta, don a zaton su sungama da waccen matsalar yanzu kuma saiga wannan ta bullo, don haka babu b'ata lokaci suka rufa akan ta kasancewar da kayan aiki ga kuma kwararun likitoci batare da b'ata lokaci ba suka gano musabbabin kunburin cikin ta Ashe mahaifar tace ta lalace musabbabin lalacewar ta tace basu gano ba, duk wannan ciwon cikin da mugunyar ruwan duk mahaifarce sai yanzu Allah yabasu ikon gano wa, gefe d'aya kuma ga d'anyen aiki a jikin ta wanda mugunyar dake futa daga mahaifar tata tana futa ta k'asan ta shiyake b'ata musu aikin wanda a yanzu ma basuda tabbas akan sa.

To Hawwa dai tana cikin wahala don haka yan uwa da abokan arziki saidai muyi mata fatan samun lafiya,(kalubale gareku mata masu dabia irin ta Hawwa, gani ga wane dai ya ishi wane tsoron Allah)

FEENAT!!! Where stories live. Discover now