BABI NA 13

290 19 0
                                    

[8/4, 6:17 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!

BY Mamanhaneef

2016

32

***Hmm Alh ya sauke numfashi kan ya dubi Ismail Wanda ke shirin barin falon yace"Ismail kabar ganin inabin ka ta lallami kanacin Albarka cin Kamal ne tareda girman son da Maryama takema ka amma badan wannan ba kai baka isa kayimim jayaiya ba don in fitsara ce kowama ya iyata kai bakasan komai akan taba, juyowa Yy yakuma duban Alh da kyau a ransa kuwa cayai"anya kwa mutumin nan kalau yake?nida raayina yadinga nunan isa da gadara?a zahiri kuma cayai" uhm tonidai a gafarce ni nabarku lafiya.

wata kara yaji tasaki tareda futowa daga maboyar ta wacce tunda suka soma mgana tana jinsu tana zubar da hawaye don tasan ba lallai Ismail Yy naam da mganar dady ba intayi laakari da yanda ya bullo masa,tamkar dai Wanda ya haifeshi.

cikin kuka ta karasa gaban Ismail tasha gaban sa tana cigaba da kuka,shikam ido yazuba mata don baida abin fada burin sa kawai yabar musu gidan su, cikin kuka tadago da jajayen idanun ta hannun ta dafe da kirjin ta"Ismail kayi hkr don Allah banso haka ta kasance tsakanin ka da dad ba,"babu komai ai kema kiyi hkr banki yarda da bukatar ki waidon banason kiba Aa nakine sabida mahaifin ki inai miki fatan Alkairi da samun miji Wanda yafini"yana kaiwa nan yaketa reta yayi ficewar sa da sassarfa don jinsa yake kmr akan kaya.

kara rudhwa tayi da kuka tayi zaman dabaro agurin dad din tane yataso ya kamota yana rarrashin ta,"rabu da Dan abu takazan uba wahalalle mara rabo da yardar Allah saikin samu Wanda yafishi ni bansan mekike so a jikin wannan fakirin ba talaka dashi sai fadin ran tsiya tamkar wani Dan sarki toki kwantar da hankalin ki kuzabi daya a cikin yayan abokaina dasuke zuwa gurin ki Ku daidaita ayi auren a takaitaccen lokaci nisaina nunawa Ismail iyakar sa. duk wannan maganganun dayake bai lura da halin da Maryama tashiga ba sai bayan yagama babbamin sa dagotan dazaiyi yaga takima tayi lakwaf tamkar matacciya, Nanfa yakideme ya gigice ya ware murya ya kwalawa momyn ta kira,hakadai suka nufi asibiti da Maryama cikin tashin hankali don a zatan su kota mutune.
[8/4, 8:28 PM] Mamanhaneef: 33.                                     ***Sabanin daya gifta tsakanin Ismail da Mahaifinsa Sam bai masa dadi ba duk da yasan dama zaarin wai ansaci zanin mahaukaciya, har cikin makaran ta yabiyo Ismail yabashi hkr tareda baiyana masa halin da Maryama take ciki wacce take kwance a asibiti cikin mawuyacin hali,Ismail ya nuna tausayawar sa tareda bashi tabbacin xaije har asubitin yaduba ta,Kamal yaji ddn hakan donko babu komai zuwan Ismail asibitin zai ragewa Maryama radadin ciwo Wanda yanada tabbacin bata da wani magani daya wuce Ismail shikansa yana mmkin irin son da takewa Ismail kuma yakan tausaya mata har kwalla yake a duk sanda ya taddata tana razana tareda kiran sunan sa, momyn kuwa tashi daya ta zabge ta rame sabida ciwon yarta tatsaya mata arai tana matukar tausayin ta don tasan yarta batasan tawakkali ba balle tayishi batasan wata aba kaddara ba balle tasawa ranta salama tayi tsinkayen aure fa kaddara ne Wanda Allah yake kaddaro shi tsakanin bayin sa koda so ko babu so sai anyi shi, batada yanda zatayi a halin yanzu saidai tabi yarta da addua don tasani mijin ta yariga ya cutar da ita a yayin da yahana mata goyon baya wajen tarbiyyan ta yaran ta,tasan wannan babban gibin da yayi mata bazai taba kankaru wa cikin ranta ba.                            **                                        ***Anasa bangaren kuwa yakai zuciyar sa nesa yaje duba Maryama wacce yatar data cikin matsanan cin hali don a sanda yajema aman jini yaraeda ta tanayi likito ci suntaru akan ta tareda bata taimakon gaggawa, kukan daya tarar mahaifiyar ta nayine ya karyar da zuciyar sa har yaji tausayin ta tacika ransa baiji aune ba yaji kwalla ta diga kan kuncin sa, bai zaci son da Maryama kemasa yakai haka ba,tausayin ta ya tsaya masa arai har yakasa bacci a sanda yazo kwanciyar sa, da sassafe kuwa Yakoma asibitin don ganin halin datake ciki don yagama saddakar wa kanda safe zaije ne yatar da gawarta,             Asan da ya isa dakinna ta babu kowa cikin sa sai ita datake kwance saman gadon marasa lafiya tana bacci da alamu allurar bacci bata sake taba, Akan kujerar dake gaban gadon ta ya zauna duk jikin sa yayi sanyi idon sa kuwa yana kanta, motsi yaji a bayan sa yajuya Ashe momyn ta ce take futowa daga bandakin dake cikin dakin,                                   Cikin faraa tace"Aa mal Ismail ne da safe haka? Nan yashkga gaidata tareda tambayar jikin Maryama,ta amsa tareda karai masa bayani a game da tsiwonnata kme yanda likitan ta ya shaida musu.                                Yananan zaune ta farka daga baccin tasoma kiran sunan Momy ta a hankali cikin murya ta Mara lafiya, tashitai ta Isa gareta tana karai mata sannu, Ismail ma sannun yake mata cikin tausayawa,               duban sa tashiga yi wanj siririn hawaye ya surnano ta gefen idonta, tafurta sunan sa a hankali"Ismail"shjma sunan ta yakira"Maryama"magana take masa wacce shukadai yasan abinda take fada masa"ki kwantar da hankalin ki Msryama kisawa zuciyar ki salama kibawa likitan ki hadin kai don ganin sun comma nasarar ceton rayuwar ki,"kana tunanin zan rayu babu Kaine?"likita babu abinda zai iyayimin inhar baka ceci rayuwa ta ba,"ina zuwa"da kansa yahada mata tea yayi mata brush tareda taimakon momy yabata tasha dadan yawa ba laifi nos tashigo tabata magani tareda yimata Allura sannan yadawo ya zauna kusa da ita yana duban ta duba na tausayi dazai iya daya furta mata Kalmar datafi bukata taji daga bakin sa a halin yanzu, to matsalae shidai bai iya karya ba balle Yy mata don haka yadubi mahaifiyar ta yace"Hajiya nizan tafi amma zandawo zuwa dare, zanje ne nayi shawara da Mahaifiya ta a game da Maryama bazan yanke hukuncin auren ta kai tsaye ba sabida inada magaba ta, Cikin murmushi tace dashi tamshikenan Ismail Allah yasa hakan yafi alkairi, jin maganar sa tayi tamkar a mafarkii bashiri tamike zaune tareda cewa"Ismail zaka aure ni? Jijjiga kansa yayi tareda cewa"zan aure ki Maryama amma kafin nan da sharadi, cikin zakuwa tace"Wlh kowanne sharadi ne zan karbeshi inhar bazaka cutar dani ba, shuru yayi yana wani nazari cikin ransa, Nanfa bakin Maryama yabude harda mikewa tsaye da kanta abin yabaiwa momynta mmki lijitan ma daya shigo haka yacika da mamakin ta, nandai suka shiga mgana da Ismail cikin harshen turanci duk dai akan tsiwon nata, likitan ya jinjina wa Ismail tareda ganin karfin halin sa nayun kurin auren ta donya ceto rayuwar ta.  Yinin ranar haka Maryama tayishi cikin farin ciki da karsashi kai bakace itace Mara lafiyar ba illa ramar dazata shaida hakan. Kamal yaji ddn sadaukarwar da Ismail yayi yakuma tabbtarwa da kansa Ismail adaline yananan da halinsa na tausayi da sadaukarwa Wanda yasanshi dashi da jimawa,dad dinta kuwa?yafi kowa farin ciki yanuna murnar sa harya kissima kyautar daxai nunkawa Ismail akan wacce yayi masa a baya.
[8/4, 9:06 PM] Mamanhaneef: 34,                                    **                                         **Toda Ismail yakoma gida ya shaidawa Hajiyan sa maganar Maryama yabata labarin ta kaf tareda na mahaifin ta dakuma shaida mata halin da Maryaman take ciki, itadai jikinnata ne yayi sanyi tace dashi"Shikenan bazan hanaka auren taba don bazan so rayuwarta ta salwanta a dalilin kaba sabida nima ganawa yayan nan a gaba bankuma San ta inda kaddara zatazo masu ba, dadai na kowa ne don haka na amince ka aure ta amma Allah yagani hankali na yafi kwanciya da Nafesa, Murmudhi yasaki donjin ta ambaci sunan ta"Allah sarki Nafisa baiwar Allah nasan naiwa Nafesa laifi kwana kusan hudu bansa ta cikin ido naba, amma yau zanje gurin ta inason tabani shawara akan lamarina da Maryama,   itadai hajiya uhm tace tamike tabar masa dakin don hankalin ta bai kwanta da wannan xabi ba.                             *                                        *washe gari ya dauki mahaifiyar sa yakaita asibiti duba Maryama wacce zuwa yanzu takara jin sauki a yanzu ma tana zaune ne tana amsa wayar da dad dinta yayo mata, Cikin girmamawa da mutun ta juna suka gaisa da momyn Maryama, tanai mata yamai jiki, itama Maryaman cikin girmamawa ta shiga gaida hajiyan tareda yar kunya wacce batasan tanada ita ba, ganin tarbar girman data samu wajen momyn yasa hsjiya tasaki jikin ta har ranta yasoma kwanciya dasu donta fuskan ci Mahaifiyar Maryama macace mai kirki da mutuntawa,                      bawani jimawa sosai tayi ba Ismail ya maidota gida tareda yiwa Maryama Alkawarjn zai koma in baa sallame ta ba duda yanada tabbacin xaa sallame ta a yau inyai laakari da yanda jikinnata Yy kyau.            **                                        *A bangaren Nafesa kuwa?kwana biyu tana bukatar nutsuwa da Hutu don zuciyar ta tahautsine da yawan tunane tunane tarasa yanda zata ranta taji sanyi tafi bukatar kadai cewa akan zama cikin mutane don haka bata damu da rashin ganin Ismail da batayi kwana biyu,                                   Cikin kwana daya jal maganar auren Ismail da Maryama ta karade makaran tar su duk inda kazaga maganar ce dai ake kara cancana ta, dayawa sina mmkin yanda lokaci daya reshe yajuye da mujiya don wasu iya tunanin su Ismail da Nafesa soyaiya suke har wasu ma cikin su suka soma zargin kwadayi yakaishi yunkurin auren ta, bayan sun kwana da sanin sunjima suna soyaiya da Nafisa, Zance dai kala kala haka yake futowa daga bakin mutane, Ilham kanwar Maryama kuwa? Duk inda ta zauna takan bada labarin irin dukiyar da dad dinsu ya mallaka wa Ismail kanya Amince da auren yayar ta,                   Sam Ismail bashida masaniyar Abinda yake faruwa balle Nafesa, itada rabon ta da makaranta ma ta kusan dosae sati, shinedai yakan shiga shkma bawani jimawa yake ba.

FEENAT!!! Where stories live. Discover now