BABI NA UKU

465 38 0
                                    

aneef: FEENAT!! 

BY

       Mamanhaneef

©NWA

2016

6

***Tun daga wannan lokaci suka bud'e sabon shafi na soyaiya da k'ara aminta da junan su,nasihar hajiya hajara momyn Nafeesa tayi mutuk'ar tasiri cikin zuciyar Feenat tamik'a lamuran ta ga Allah ko kad'an bata k'ara nuna damuwar ta akan maganar auren da dr zaiyi ba,ganin hankalin ta kwance ya taimaka wajen samun nutsuwar dr,ita kanta hajiya binta mahaifiyar dr har gidan tazo da niyyar dannar k'irjin Nafeesa tun daga yanayin data amshe ta ta tabbatar bata da wata matsala tamkar tai mata sujjada dan matukar biyaiya,hakan yayi matuk'ar birge hajiya tak'arajin k'aunar Nafeesa har cikin ranta a k'arshe tai mata nasiha tareda bata hak'uri akan auren data umarci ismail ya k'ara,murmushi kawai tayi kan tace" wallahi babu komai hajiya ai komai muk'addari ne gurun Allah banida wata matsala da zata dameni hajiya indai auren Dr bazai zama silar tarwatsa farin cikin da muka gina rayiwar mu dashi ba.

cikin tausayin ta hajiya tace"da yardar Allah babu abinda zai faru sai alkairi kuma naimiki alk'awarin jajir cewa tareda saka ido akanku duk matsalar data tunkaro Ku zanyi kokari saka hannu don ganin na kawar da ita dake da sama ila duk daya kuke aguri na bansa sama ila k'ara aure don a cutar dake ba kuma ban hadashi da hawwa da wata manufa ba damacan Allah ya k'addaro akwai rabon aure a tsakanin su,

nan dai sukai ta tattauna wa da hajiyan haka nan suka rabu tatafi tana sa mata albarka dama tanada tabbaci akan Nafesa Sam batada futuna tasan babbar Saar da samaila ya taka samun mace irin nafesa alkairi ne kuma dacewa ce don mace tagari itace uwa gari uwa tagari.
[7/14, 2:59 PM] Mmnhaneef: FEENAT!!
BY. Mamanhaneef
©NWA
2016
7
***Bata zaci zata samu wannan sassaucin gurin
hajiya ba don ganin fushin data tafka kwanaki
duk dai akan rashin d'aukar matakin da Dr baiba
akan rashin haihuwar tasu, amma abin mamaki
ta hango tausayin ta da k'aunar ta cikin idon
hajiya duk da dai ance wata kusan tafi kusa da
sai tace ko hawwan tashigo gidan hajiya bazata
juya mata baya ba duda kasancewar hawwa 'yar
kanwar hajiya ce wacce suke uba d'aya.
A b'angaren Dr kuwa harkokin sa yake hankali
kwance koda mantuwa bai d'auki kafa yadoshi
hanyar gidan su hawwa ba hajiya da 'yan uwan
tane suke bidirin su shi har zuwa wannan lokaci
baisa ran sq a xai k'ara aure ba,kallon su
[Edit]
[7/14, 3:49 PM] Mmnhaneef: Kawai yake shida matar sa kansu a had'e yake zaman su suke mai dad'i tamkar wani Abu bai faru a kwanaki ba,maimakon Feenat tanuna kishi kotad'u mataki akan cin amanar da mijin ta yake shirin yimata shida mahaifiyar sa?Aa saita rike abinta hannu biyu kulawar data ke bashi a yanzu ma harta ninka ta da Dr har mance wa yake dawata hawwa da aka bashi wani sa inma itakan kawo masa maganar nan da nan kuma zai kawar da ita, Ab'angaren hawwa kuwa? Sam zab'in iyayen ta bai mata dad'i ba asalima tanada Wanda take so shima yana sonta sunyi alk'awarin aure dashi amma me?Kwatsam saijin maganar auren ta da Dr Ismail tayi da farko maida abin wasa tayi don a tunanin ta yanda suke da Anty nafeesa aibai kamata taimata haka ba. Tofa A zahirin gaskiya hawwa suna matukar shiri da Feenat tun tana k'arama 'yar shekara goma takan zuwa Hutu gidan Nafeesa sun shak'u mutuk'a tamkar k'anwar ta haka takejin ta tasan sirri ka dayawa na Feenat itama kuma tasan hawwa kwarai da gsky hakanne yasa hankalin ta yayi matuk'ar tashi a sanda Dr ke fada mata hawwa zai aura, a bangaren hawwan kuwa tsalle tayi ta dire tace sam bata yarda ba ita tanada wanda take so, tad'aga hankalin ta ta tada na iyayen ta,mahaifiyar ta kuwa tace sam bata isaba aure kamar anyi angama babu fashi, duk wannan budirin Dr baisan ma anayi ba hawwa bata kara tsinkewa da lamuran ba saida taga ankawo kud'in auren ta gashi koda wasa bata saka Dr a cikin idanun ta ba wannan ya tabbatar mata da shjma din takura shi akai to me mace kamar Anty Nafeesa mai zaiyi dani inbanda kwadayi irinna hajiya ta? Ta aiyana a cikin ranta, Abinda yafi damunta batasan da wanne ido zata kalli Anty Nafeesa ba,tana nan zaune wani tunani yazo mata tamike takama shirin zuwa unguwa. Innan ta dake kicin tana tankad'en gari ta ware murya ta kwala matakira da hawwa! Tafuto rannan nata a had'e don tunda aka fara mganar Dr ake takun sak'a da ita,turo baki tayi tareda cewa" gani inna ta karkata kai tace"ina zuwa haka kuma da azahar dinnan ga rana fatse-fatse?batare da ta bata amsaba ta rataya jakar ta a kafad'a tare da cewa"saina dawo"Cikin masifa da hayaniya ta taso tana fad'in yau kajimu da yarinya Mara mutunci kina jina inai miki magana sabida tsabar kin rainani shine zakiyi tafiyar ki?Tokije kinji Dan Allah inkin cika yar halak inkin tafi karki dawo aure dai babu fashi inzaki mutu yau sai ankai gawar ki gidan sama ila zaakai ta makabar ta,inban da rashin hankali irin na d'an yau ana kaiki inda zaki huta kina kai kanki inda zaki wahala?inban da toshewar basira me haladun yake dashi dazai rike ki?yana yawo iska tana yawo dashi a sararin samaniya me ake da irin su, daga wannan inuwa yabi wannan inuwa to wallahi bazan saida akuya tadawo tana cinyen dusa ba,duk wannan kumfar baki da inna take hawwa na tsaye rik'e da kugu saida inna takai aya tace"komadai menene da haladun ada baki gani ba sai yanzu, kuma duda bashida shidin haka yake iya bakin kokarin sa don ganin ya kyautata miki tunda kike turawa kantin sa aciyo miki bashi bai tab'a turowa kibashi kudin sa ba haka kuma baki fasa ba kullum yara na hanyar kantin haladu daduk bakiga gazawar saba saida kk hango mai maik'o ita kanta hajiyar da tasan abin da kk shirya akan auran nan dabata yi kuskuren amince miki ba,ni wallahi ranar nadama nake jiyewa kaina inna sabida babu Wanda zai shuka sharri yace zai girbi alkairi, tafiya kuma unguwa zanje gidan Anty Nafesa zanje naimata bayani banason ta kalle no a macuciya maciya amana butulu,tana kaiwa nan tayi waje abinta ba irin kiran da inna batai mata ba amma tayi tafiyar ta,hannu tad'ora aka tace" nashigq uku in kika tonan asiri shikenan nayi jifar gafiyar b'aido. Kubiyo ni

FEENAT!!! Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin