BABI NA SHA DAYA

312 23 0
                                    

[8/1, 6:56 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!

BY. Mamanhaneef

2016

28

***A bangaren Maryama kuwa?Tananan zaune takasa koda kwakwaran mitsi zazzwbi takeji cikin jikin ta kanta kuwa wani irin sarawa yake don tsantsar damuwa,kamal ne yafuto daga dakin nasa da shirkn futa masallaci don yasoma jiyo kiran sqllahr magriba, bai tsammaci akwai mutum a gurin ba donshj harma ya manta da batun Maryama don a tunanin sa tunda ya banke kofar sa komawa zatai,amma me? juyowar da zaiyi ya ganta xaune kanta akan gwuiwar ta,Maryama!?Yakira sunan ta tareda d'ago da kanta da hannun sa, gaban sane yafadi don ganin yanayin datake ciki baiyi wata wata ba ya kwalawa Ihsan kira aikuwa tafuto a firgice tana fadin"lafiya bros?

tunkan ya bata amsa ta hangi Maryama cikin wannan yanayi ta kwaso da gudu tazo ta rungumo ta jikin ta tana cewa"meyasa meta bros?Kinga kamota mukai ta daki, nan dai suka kamata suka kaita dakin ta suka kwantar da it's, hannun ta dafe da kirjin ta Wanda ke mata azabar ciwo sai nishi take don azabar ciwo,

batareda bata lokacj ba Kamal yashiga bata taimakon haggawa tareda yimata wasu gwaje gwajen daya dace, sai a lokacin Ihsan ta sauka kasa inda dakin mahaifiya su yake ta shaida mata halin da Maryama take ciki,Nan dai suka rankaya suka koma tare, tsawon kwana uku aka dauka ana jinyar Maryama wacce daga karshe dole suka dangana ta da asibiti, kasancewar sunsan damuwar yar tasu yasa basu wani damu da bayanin da likitanta yai musu ba, don tun a rnr kamal yafada musu komai, sunfi karkata agurin rarrashin yar tasu tareda bata tabbacin Ismail yazama nata yagama don mahaifin ta yabata tabbacin koduk dukiyar sa xata kare saiyayi yanda zai nemawa yarsa muradin ranta,wannan furuci nasane yasata jin dadi harta kwantar dda hankalin ta tasoma karbar abinci a rnr don ko shayi zatasha da kuka zata shashi don daci yake mata Sam batajin dadin komai,

mahaifiyar tace kan nuna mata muhimmancin hkr tareda nuna mata bafa duk abinda kakeso kk samuba,wannan dalilinne yasa suka so samun sabani da mijin ta Wanda yakuma shaida mata shifa adole saiya samowa yarsa abinda takeso inkuma Dada tayar mata da hankali zatai to tatafi gida kuma karta kuma dawowa, kokadan ranta bai sosuba don hakan yazame mata sabo, don haka tahada inata inata ta bar asibitin bayan tace dashi"Inaso kadinga tuna cewa"ba kullum ake kwana a gado ba kuma ba komai dukiya take samarwa ba wani abin saikaga ga dukiyar amma bazata iya siyama ba sabida bb ikon ka balle aje gabatun Alfarma, maganr ta kona ransa harya bita da bakaken magangu Wanda ko saurarar sa batai ba tayi fucewar ta,kwanan Maryama biyar a asibiti aka sallamo ta don jikin nata Yy kyau damuwar ta taragu don tasan dady nta zaiyi komai don yacika mata burin ta nasamun muradin ta wato Ismail, Sauki dai tasamu sauki najiki amma kasan ranta cike yake da fargaba aduk sanda ta tuno Ismail da Nafesa saitaji gaban ta yayi muguwar faduwa,tayi wata iriyar rama inka ganta kaika ce jinyar shekara tayi a kwance sabida tsabar rama,
[8/1, 8:29 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!

29

***Da sallama tashiga falon mahaifin ta,wanda ta tarar da yayun ta guda biyu yaya mohd da yaya Hisham suna mgnar kasuwancin su da Abban nasu, shigowar ta yasa Alh Abdallah ya katse hirar tasu da cewa"Mohd kuje kudan bani guri zamuyi mgna da kanwar ku inyaso gobe dq safe in Allah ya kaimu makara sa dama maganar taku duk ta gundire ni,

jin hakan yasa Nafeesa yin murmushi tareda cewa"yauwa Abba na dama nazo maka da hira mai dadi ba irinta su yaya ba maisa gundira, jin saukar rankwashi tayi bayan ta zauna aikwa ta dafe kan tareda sakin yar kara"ash ash Abba kaga xai burmamin madiga! aa kwakwalwa zai burma miki yar sharri haka kawai muna magana mai muhimmanci kinzo kin katsemu bayan hirar ki ta kirki bata wuce ta yaya Ismail,cewar hisham, yaya mohd kuwa dayayi rankwashin cayai"hmm aini dai banga Alamun zaa cika alkawarin da aka daukar wa Abba ba,tunda ta nunamin Ismail nace anzo gurin,

yar dariya tayi kan tace"eh naji sokuke ku hadani da Abba na kuma babu kofa,tafada tana mai karasawa gaban Abban ta wanda yake duban su fuskar sa cike da murmushi yace"nifa banason wayon duka mohd ayi wasa amma banda zungurin uwar miji da tabarya, dukkan su sukai dariya sukaiwa Abban nasu sallma sukabar shi da Nafesan shi don tunda suka ganta sunsan dole sutashi, don Nafesa batada abokin shawara wanda yawuce mahaifin ta ko kadan bata boye masa damuwar ta sunyi matukar shakuwa da mahaifin ta donko fuskaeta ya kalla yakan gane yanayin ta sabida tsabar shakuwar su.

tiren dake shake da kayan marmari ta janyo tasoma yanka masa tufa tana mika masa yana sawa a baki yana taunewa cike da nishad'i, itma murmushin take tana tambayar sa mutanen bauchi wanda ayau yabaro gurin su, Cikin faraa tace"Abba dama nakagu kadawo ayau sabida gobe Ismail zaizo ya gaishe ka,"wanene Ismail Nafeesa?"Nanfa hirar Ismail ta baeke  bata boye masa komai ba tyn farkon haduwar su kawo yau dasuke tare,kallon yar tasa kawai yake yanda take  bashi labarin cike da nishadi wanda zaj iya cewa bai taba ganinta cikin irin saba,

ta karashe da cewa"gobe zaizo ya gaida kai Abba,murmushi yayi kan yace"Nafeesa yaushe kika soma kula maza bansani ba? kin manta cikin alwashin ki harda na rashin kula maza har sai bayan kun kammala keratin ki?ya gyara zaman sa kan yacigaba"waima ina ina duk hakan takasance batare da nasani ba? Alamu sunnuna kunjima tare kuma kundhaku dashi innai laakari da yanda kike zancen sa kina nishadi kodai yar tawa tasoma soyaiya taiwa burin ta tawaye?Murmushi tayi tadanji kunyar Abban ta daga baya kuma ta dake tace"Ko daya babu ita a tsakanin mu,Abba Ismail yanada kirki halin sa shizaisa a kaunace shi, kuma Abba duk yan gidan su sunada kirki kuma suna sona,

kuma bawani jimawa tare mukai ba Abba kawai Allah ya hada jinin mune,tam naji batunki Nafesa amma a ina yake kuma wanene mahaifin sa?Abba Ismail maraya ne Baban sa Yakima da rasuwa shiyake rikeda gidan su yanada kanne ga kuma mahaifiyar sa yana aiki a asibin koyarwa na (AKTH)yazo BUK ne karo karatu yana  shekara ta karshe a matakin degree na biyo(Master),gyada kai yake yana sauraron ta,"Abba kasan karatu nasa a zuciya ta banajin akwai wani Abu dazai canja raayi na, uhm uhm Nafeesa karfa abubuwa su rincabe azo anai mana dariya kinsan yayunki yan adawar mune,

"nidai ina zargin akwai abinda malam ya hanani fada a tsakanin Ku dondai kin kafene,dariya tayi sosai kan tace"Allah Abba babu komai nibansan ma yanda akeji in ana son mutum, au to bari nagaya miki inkuma yazamana hakan tafaru dake to saiki bani gari"eh na yarda Abba,

"yawan tunanin abinda kake so"damuwa dashi"kishi akansa"son kasancewa taredashi"farin ciki a yynda kk tare koma kima kina tunanin sa,nishadi a sanda kk hirarsa"son duk wani abinda yake so"kin abinda yakeki"son faranta masa dadai sauran su,haka naitaji a lokacin danake kaunar mahaifiyarku, rufe fuska tati cike da kunya tace"Abba na nidai banajin" katseta Yy kan yace"saida yatsare gida alamun batun wasa yakau"bakya karya nafesa kuma banason kimin ita ayau inason kije kiyi Istihara a yau nima zanyi tawa duk abinda kkji ki sanar dani.

hakann tabaro dakin Abban ta zuciyarta a cunkushe da tunanin kala kala.

FEENAT!!! Where stories live. Discover now