BABI NA BIYU

669 46 0
                                    

aneef: FEENAT!!

BY. Mamanhaneef

©NWA

2016

2,

Tun daga tsakar gidan yasoma jiyo mitar da hajiyansa take, wacce ko shakka babu yasan tasace daman yasan za ari wai ansaci zanin mahaukaci ya, nandai ya cusa kansa cikin kayataccen falon hajiyar tasa bayan ya tsaya a tsakar gidan sun gaisa da uwani wacce kewa hajiyar hidima.

nan dai yazube a gaban ta cikin k'ask'antar da kai yashiga gaishe ta tareda tambayar lafiyar ta, k'annan sa dake gefe Amina da Fateema suka shiga gaidashi a yayin da ya amsa a tak'aice don yak'agu yaji kiran da hajiyar kemasa don hankalin sa gaba d'aya yana kan matar sa ya matsu yakoma gareta don ya wanke mata dinbin damuwar daya hango kwance cikin idon ta.

jiyai ta katseshi da cewa" sama'ila anya kwa k'alau kake ? inata magana kayi shuru koma hankalin ka ba agurina yake ba? Cikin in ina yace" Aa inajin ki nace daiko lafiya? Murmushi takaici tayi tareda tab'e baki kan tace" waime kake nufine sama'ila munyi magana dakai tun kwanaki daga cewa zakai tunani shuru kaki cewa kamai, cikin rashin fahimta yace" wacce magana kenan hajiya? nanfa tad'au salati ta dure kan tacigaba" yanzu duk mgnar da mukai kananufin ka mantata kenan? Wato kaidai magana inhar bata matar ka bace baka tab'a d'aukarta d muhimman ci ko?Cikin tattausar murya yace" ba haka bane hajiya kinsanni inada mantuwa shaf namanta mganar da mukai kituna min shine mafita tunda nakasa tunawa,aishikenan ni abin yashafa dole na tuna maka don naga alamun soyaiya kasaka agaba rashin haihuwa baya da munka ko kana cikin jerin mutane marasa son haihuwa ne oho! tonidai nafad'a maka tyn wuri kasan mekake ciki, inkai ne bakason k'aruwa kasanar dani inkuma akwai wata kullalliyar da kuka shirya kafad'amin nadena wahalar da kaina tunda bakai kadai na haifa ba illah iyaka dai na bincika naga matsalar a gareka ne duk hukuncin Dana yanke kaika jiyo inma daga gurin ita rayuwar taka ce kake boyewa zansani,

cikin lallami yace" kidena damun kanki hajiya babu wata matsala da Allah zai doro mana Mu boye miki ai abokin kuka ake fadawa mutuwa,lokacin haihuwar ne Allah bai kawo ba amma bamuda wata matsala.

to Alhamdll tunda abin haka ne tofa dole ka aminta da zance na Wanda kasashi a makwashin shara ka watsar, mgnar Hauwa u nabaka ita halak malak zan aura maka ita inason naga jikokina kan kasa ta rufe idona inyaso kuko shekaru Dari zakuyi kyna jiran lokaci saiku jira bandamu saina samu jika daga bangaren nafeesa ba, tunda ba ita kadai Allah y hallatta maka ba?Sai nace Alhamdll

gumin dake karyowa Dr Ismail kadai yaisa ya tabbatar mana da rudanin da yashiga sakamakon mgnar hauwa da hajiya tai masa duda cewa wannanne karo na uku kenan, Innalillahi yashiga karantowa cikin ransa take Wasu mganganu suka shiga dawo masa cikin kunnansa,tattausar muryar ta tadawo masa" DR KARKASANI NAYI ABINDA ZAIZAMEMIN MATSALA DONKU MAZA BAKUDA TABBAS!

KUBIYO NI

MMNHANEEF
[8/29, 8:21 AM] Mamanhaneef: FEENAT. BY. Mamanhaneef. Page 4. ©NWA. A kwance take saman luntsumemen gadon ta
Wanda yasha shinfud'u na alfarma sanyin split y
gauraye da dadan tuy. raren wuta na daki,sanye take
da kayan bacci ta k'udundune cikin bargon ta
lokaci zuwa lokaci tana duban agogon bangon
dake d'akin,misalin karfe 11 na dare taji motsin
shigowar sa ta sauke numfashi hmm tare da
gyara kwanciyar ta, shuru-shuru tana tsumayin
shigowar sa babu shi babu alamun sa harta soma
zargin kanta don haka ta ture bargon ta mik'e cike
da kasala jikin ta duk yayi sanyi tanufi b'angaren
sa,
gaban ta ne yafad'i dmm don bata tab'a ganin Dr
a cikin wannan halin data ganshi yanzu ba, a
zqune yake gaban madubin dake d'akin
yazubawa guri d'aya ido duk ilahirin jijiyoyin jikin
sa suntashi idonsa yayi jawur ga wani gumi
dayake keto masa tamkar ya had'iyi kunama jin
motsi yayi a bayan sa,yayi saurin waigo wa don
a zaton sa tayi bacci.
FEENAT yakira sunan ta cike da damuwa,itama
fal take da damuwar kwallah harta cika gurbin
idanu wanta tadaiyi ta maza ta cije ta k'araso
inda yake,kafad'ar sa ta dafa ya juyo ya ruk'o
hannun ta sai a lokacin ta lura da hawayen dake
kwance kan fuskar sa, cikin mamaki
tace"subhanalla Dr kuka yau da kanka? Meyayi
zafi haka Dr?Cikin shauki na tausayi da jimami ya
ruk'o tareda cewa" ki yafeni FEENAT na zalince
ki na cutar dake nazama mai san zuciya a gaeeki
a yau nayi nadama mara amfani da nasan da irin
wannan ranar da banbiyewa San raina na cutar
dake ba, meyasa na yanke hukunci banyi dogon
tunani ba? Meyasa kika biyewa gagararriyar
zuciya ta Mara adalci FEENAT? Yanzu ne lokacin
daya kamata naimiki hallacci amma banida
kwanjin hakan ina k'arkashin ikon mahaifiya ta
FEENAT ki yafeni banida niyyar wulakanta ki ko
cin zarafin ki Allah ne ya kaddaromin kara aure
bisa umarnin hajiya ta.
rungume yake cikin jikin ta itama hawayenne
yake FIFA daga idanun ta takasa furta kalma
guda d'aya, jin yayi shuru yasata k'ak'alo
murmushin yak'e kan tace"dama nasan zaarina
komai Daren dadewa wannan ranar tananan
zuwa,shiyasa tuntuni nacire tsammanin tabbas
cikin rayuwa ta,don haka kasani indai nice
kasawa ranka bakada matsala ta b'angare na
nimai son duk abinda kake so ne Dr inhae na
hanaka aure tona zalince ka don haka kadena
jifan kanka da muggan kalaman da basu dace ba,
nice dai nayi kuskure nakasa hangen nesa saida
lokaci ya kure mini inai maka nasiha da kabi
umarnin mahaifiyar ka.
Cikin wata iriyar matsanan ciyar damuwa duk ya
cika da tausayin matar sa mai sonsa mai
tsananin hakuri a garesa, duk da ta amince masa
shikan sa yasan ya cutar da ita, zanyiwa hajiya
biyaiya amma saida yardar ki a game da wacce
takeson aura min don Sam zabin hajiya bai
kwanta mini ba,cikin sanyin murya tace"wacece
zabin hajiya? batarw da tunanin komai ba yace"
wai hawwa!
zaro idanu wants tayi tare da cwwa"hawwa
kuma? wani irin jiri taji yana Neman kwasar ta
lawww ta tafi zata fadi a razane yayi kanta
tareda riko ta.
[Edit]
[8/29, 8:21 AM] Mamanhaneef: FEENAT!!!

BY

Mamanhaneef

©NWA

2016

5

A kan makeken gadon sa ya shimfid'e ta hankalin sa tashe yasoma kiran sunan ta,FEENAT FEENAT!! idon ta a lumshe yake har zuwa wannan lokacin bata denajin jiri na kwasar taba cikin ranta kuwa sunan Allah take ambata kota samu sassaucin nannauyan ciwon daya tokare ta,jin dr duk ya rude ne yasata ambatar sunan sa tareda cewa"kabani guri Dr bana bukatar komai da kowa a yanzu, cikin mamaki yakuma duban ta yace" FEENAT anya kina cikin hankalun ki kuwa?Yau nine bakya buk'ata?a hankali ta bude idon ta wanda ke lumshe kan tace"eh kabani guri kawai ina bukatar nutsuwa ya bud'e baki zaiyi magana ta rushe da wani irin kuka wanda yakara daga hankalin sa, don yasan matar sa sarai ba karamin abune kesa feenat kuka ba shi sam baiyi zaton hakan daga gareta ba don yasan matar sa mai hkr ce tareda dunbin tawakalli ga uwa uba ilimin addini dana zamani wanda rayuwar ta taginu a turbar su.

mik'ewa yayi guiwar sa a sanyaye yaja jikin sa yabar mata d'akin cikin matsaman ciyar damuwa wacce yadora laifin ta akan hajiyan sa,yana zaman-zaman sa lafiya da matar sa ta jawo masa sun sami matsala tunma baayi auren ba.

A b'angaren feenat kuwa yana futa takuma rushewa da kukan ko kadan zuciyar ta taki saurara mata da matsanancin zafi da radadi kasa hak'ura tayi a cikin wannan daren ta tashi ta d'auko wayar dr wacce ke jone a caji tashiga neman lambar mahaifiyar ta cikin saa tasamu kuma duka daya zuwa biyu ta d'aga.

a b'angaren hajiya hajara kuwa a zaune take kan sallaya tana lazimi idar da sallah ta kenan tana shirin fara karatun al kur ani wannan sabon tane a kowanne dare saita rayashi cikin bautar ubangijin ta da wannan dabi u feenat ta tashi don ganin mahaifiyar ta nayi shiyasa komai na ratuwa. ke zuwar musu da sauki don sun rike ubangiji ko kadan basa wasa da mika lamuransu gareshi.taji ring din wayar ta a gefen ta wacce ke jone a caji da farko taji tsoro sai kuma tayi tunanin kodai dady ne ke bukatar wani abin oho, ta dauko wayar ganin number ismail gaban ta yafad'i a fili ta furta" ya salam feenat kira a wannan daren? jin kukan feenat ya daga hankalin ta fadi take" Nafeesa lafiya meyafaru ina ismail meuafaru?Cikin kuka tace" Ki taimake ni momy nashiga jarabta momy zuciya ta taimin zafi narasa yanda zansa kaina momy ismail zai kara aure sabida ni ban haihu ba,kukan ta yakara tsanan ta,cikin sanyin nurya momy tace"kiyi shuru naji damuwar ki amma babu abinda zan iyai miki kanki fad'amin wayafi cancanta kifada wa?Wazai yaye miki damuwar ki wazai share hawayen ki?kinyi babbar mantuwa Nafesa shin zaki dore bisa turbar dana doraki?

Cak kukan ta ya tsaya kalaman momyn ta sunyi matukar tasiri cikin ranta,cikin sanyin jiki tace"Allah! wlh momy bantaba ba kuma bazan taba mantawa da ubangiji ba yanzu ma damuwa ce taimin yawa,amma yanzu zan gurfana gareshi naso na tafka kuskure, cikin jin dadin furucin yarta tace" yauwa Nafeesat ninasan ked'in abida ce mai yawan ibada mai yawan hkr mai tawakkali da juriya da yarda da kaddara yanzu ki kashe wayar zankira ki da safe muyi magana,

Cikin karsashi tatashi tanufi band'aki saida tawatsa ruwa kantai alwala. take taji sanyi a jikinta cikin ranta kuwa tana zumudin zuwa gaban ubangijin ta don ya agaje ta.



jiyai tadafa kafad'ar sa a d'arare yajiyo yadube ta don yariga ya futar da ran samun salama a gurin ta,murmushin daya gani a kyakyawar fuskar ta ne yasashi jin wani kwarin guiwa cikin madaukakn mamaki yake duban ta idon nan yy jajir amma ga murmushi nan taeeda annuei akwance akan fuakar ta cikin salon tausayin ta yataso ya rungume ta yana furta"Ina sonki FEENAT Allah ya Albarka ci yaruwar ki inhar aljannarki a karkashina take to nabaki halak malak, jiyai ta katseshi da cewa"naji kaima kaje kanemi taka aljannar don bana fatan nasamu aljannar da babu kai a ckin ta.

TOWWW ALLAH YASA MUDACE...

FEENAT!!! Donde viven las historias. Descúbrelo ahora