BABI NA 19

449 21 0
                                    

MNHANEEF

2016
45

***Akan mudubin ta ta dora kwalin ta zauna ta zubawa kwalin ido hawaye na kwarara akan fuskar ta, tashiga tsantsar mamaki da al ajabi bata taba zatan ko tsammanin mijin ta nada irin wannan raayin ba, rashin haihuwa Ismail bayason haihuwa to wanne irin so yake mata? Son da yake mata irin wannan sonne na rayuwar duniya bawai don yasamu zuria ta tsatson ta ya aure taba? Tajima tana kissima abubuwa cikin ranta idon ta kuwa? Yayi jajir don kuka Ashe duk bakar wahalar da takesha wajen b'ari duk shine sila? Waime ma yahanata bincikar sanadin barin ta?

Cikin farin ciki yashigo gidan cike da muradin ganin matar sa wacce bashida buri sai nata, hannun sa rike yake da leda wacce ya shakota da nau ikan cimar da yasan tana matukar so don bayada buri wanda yawuce ya faran ta ran ta, yadan yi mmki ganin baiji koda motsin taba bayan taimasa sabo da taryar ta mai cike da kulawa da tsantsar soyaiya, kai tsaye dakin ta yanufa don yana tunanin ko batajin ddne don yabar ta tana fama da mura,

Saroro yayi yana duban ta don ganin a halin daya risketa hankalin sa duk yatashi baima kula da abinda ke kan mudubin taba,  ladar dake hannun sa yasski ya nufota yana kiran sunan ta duk ya shiga damuwa don ganin idon ta kumbure tasha kuka ta koshi.

Tunkan ya ida nufinsa na dora hannun sa kan kafadun ta ta dakatar dashi da hannu, tamike a hanzar ce ta sauke masa jajayen idanu wanta tareda cewa"karka kuskura kakuma dora hannun ka akaina wanda akai dama rashin Sanine ya jawo hakan ayau nayi dana sanin amince maka danasan haka kake wlh daban aure ka nayi zaman shekaru mai tsayi da kaiba, dana farga da wuri watakila da zuwa yanzu na manta dakai cikin shafin rayuwa ta, amma a yanzuma inada sauran lokaci don haka a yau nakeso kayanke duk wata igiya data baka damar cutar da rayuwa ta, kwalin ta d'auko tareda cewa" Allah ne kadai asarar kwaya kwayan haihuwar da kaimin a sanadin wannan, hannun sa takamo ta damka masa tareda cewa" ga Abinka nan bazan salwantar maka dashi ba maybe agaba Yy maka amfani! A hanzar ce tashiga kwaso akwa tunan ta tashiga juye kayan ta.

Tashin hankali baa samaka rana, hankalin Dr Yy matukar tashi mutuwar tsaye yayi don bashida Kalmar da zai kare kansa don yasan shidin me laifi ne duk da yadena amfani da maganin baisan ta wacce hanya zai soma lallashin ta kuma ta aminta dashi a karo na biyu.

Har tagama loda kayan ta yana tsaye yakasa koda daga  kafarsa bakin sa yayi masa nauyi jiyai duk ya tsani kansa, ganin ta dauki mukullin mota tasoma Jan akwati nan yasashi dawowa hankalin sa cikin zafin nama yasha gaban ta tareda cakumo ta jikin sa duk da tureshin datake tareda kursheken kuka tana ikrarin yasa keta ta tafi tagama zama dashi hakan bai hanashi rungume taba, ba karamin ruko Yy mata ba wanda takasa kwatar kanta har karfin ta yakare ta hkr d kokawar illah sabon kukan data dasa har muryar ta tadashe.

Tsawon lokaci suna haka saida yabari kukan ta ya tsagaita tadawo nutsuwar ta sannan yashiga rero kalaman ban hakuri tareda nadama da kuma bata hujjojin sa nayin hakan, shurutai tana saurarar sa don bata da abin cewa yariga ya kasheta da dadin bakin sa tareda rantsuwar bai sake ba, duk da ya tabbatar mata da tunda dadewa yadena amfani  da maganin mantawa yayi bai yarda kwalin ba, yakara mata da cewq"shima zuwa yanzu yanai musu shaawar samun haihuwar tunda ya kyalla ido yaga kyakyawar baby da abokin sa saifu ya haifo da wannan ya kashe bakin ta ta hakura a karshe dai ta share hawayen ta tareda cewa"kaji tsoron Allah Ismail Duk abinda ka aikata katuna Allah uana kallon ka kuma yasan abinda ke zuciyar ka don haka kafuto fili kafadan gaskiyar lamuran ka, in haihuwa ce bakaso kafadamin amma bakada hujjqr cewa donni kake amfani da maganin da zai tsinkar da sparm dinka sabida karya samamar ka Sanyin idaniyar ka?sabida kana sona kana tausayin karna wahala kayi wannan? To wannan wacce iriyar hujja ce ismail? Babu wacce ta farka daga bacci ta ganta da duk wacce kagsnta da danta ita tasan wahalar datasha kan ta sameshi,

Amma tunda kana tausayi na bakasan na wahala ai shikenan ita soyaiyar zata wahalar damu a gaba, wani dan gajeran tunanin yazo mata take wata dariyar mugun ta ta sauka akan fuskar ta a ranta kuwa fadi take"zanyi maganin ka badai akan soyaiya kayi hakan ba? Shikenan dani kake zancen nagode wa Allah tunda saidani zaa more soyaiyar!, a zahiri kuma catai" shikenan komai yawuce na fahimce ka kuma nagode da tausayin ka gareni, duk da yaji ddn sakkowar tata amma saiya tsinci kansa da zargin wani Abu, nan dai ya kawar da wannan tunanin ya kuma rungumeta yana kara kashe ta da kaifafan kalaman sa

FEENAT!!! Where stories live. Discover now