BABI NA 27

476 16 0
                                    

[8/26, 7:20 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!!

BY Mmnhanif

63.

***Hankalin sa tashe yakira wayar hajiya yana labarta mata halin da ake ciki, ta tausayawa Hawwa kwarai da gsky don yarinya k'arama kamar Hawwa ace tagamu da irin wannan lalurar daban tausayi, Bayan sungama wayar da hajiya ne yakuma kiran Nafisa yake fad'a mata irin matsalolin da Hawwan take ciki itama din dai tausayi Hawwan tabata a karshe tai mata fatan samun lafiya suka rabu akan zaishigo gidan da daddare,

Jikin sa sanyaye ya zura wayar a Aljihun rigar sa tareda dafe goshin sa dayake Sara masa don azabar ciwo don tunda Hawwa ta kwanta a asibiti bai samu yahuta ba kullum cikin zarya yake ko ada dare baya samun isashen bacci don tsabar takurawar da Hawwa ke masa na kiran wayar sa cikin dare yanda bata bacci sabida zafin ciwo haka shima bata barin sa yayi, a wani b'angare na zuciyar sa kuma yana kunshe da mugun haushin Hawwa don ganin yanda tayi kokarin hallaka kanta akan wani banzan burin ta wanda bata tsinci ribar komai cikin saba data samu yanda take so din, duk da yasan don shi tayi abinda tayi din amma yana ganin wautarta donme xata faranta masa ta cutar da kanta? gefe d'aya kuma yaji babu dadin halin ko inkula da FEENAT  tayiwa Hawwa ko babu komai ai Hawwa tazama wani  bangare na rayuwar su duk da tq ajye aiki yasan tanada damar dazata taimaka mata don ko watannin baya tayiwa watta mace irin wannan aikin kai har wanda yafi wannan ma FEENAT tayishi kuma tasamu nasara to yanzu mezaihana takisa hannu cikin lamuran Hawwa? Bayan inma tayin ba Hawwa tayiwa shi tayiwa? Nan dai yak'ara ci zancen zucinsa yatashi da niyyar shiga gurin Hawwan to kuma saiya kasa don bayaso yaje ya tardata cikin wahalar ciwo don yana shiga dakin kukan ta ke kara taazzara ta rikeshi tana rokon shi yazo yacire mata ciwon dake jikin ta,  sai anmata Allurar bacci yake samu ya kwaci kansa,

Don haka yajuya yabarma asibitin gaba Daya, gidan Hajiya ya Isa tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin shida yace sai dare zaishigo, nan hajiya ta zaunar dashi tanai masa fad'a akan ya kwantar da Hankalin sa yadinga daurewa yanacin abinci karya kare a tsaye, daga bisani ma tabarshi da Nafisa tashiga dubiya makota,

Ita kam banza tayi dashi don wani mugun kishine ya turnik'e zuciyar ta don ganin yanda yabi ya d'aga hankalin sa akan Hawwa duk abinda yafaru ba ita tajawa kanta ba, nan yagama tak'ara had'erai tai kicin-kicin da ita k'arshe ma ta tashi  tai shigewar ta d'aki tabarshi a gurin, binta yayi da kallo harta shige dakin da d'an cikin ta wanda yafara bayyana kansa, saiyaji tausayin ta ya baibayeshi don itama abar a tausayawa ce,

A d'akin ta ya tardata kwance tadora hannun ta saman cikin ta, nan kamshin ta ya doki ruhin sa ya gusar masa da dukkan damuwar sa take yaji wani nishad'i yazo masa a kusa da ita yazauna tareda dora hannun sa kan NATA hannun wanda ta sanya saman cikin ta cikin zolaya yace" me ciki tana dusko ciskaka ciskaka, Sam bata nuna tasan yanayi ba tashitai zaune tana gyara Dan kwalin ta daya kwance yasa hannu yana tayata yana fad'in" waini laifin menayi miki ne FEENAT? yakamata ki tausayamin karfa abin yayimin yawa, cikin ko inkula tace" yayi maka yawa kamar ya? Bayan Hawwa kanada wata damuwar ne? Koba matsalar Hawwa ce a gaban ka yanzu ba? Murmushi yayi kan yace" da kuma FEENAT ba, tab'e baki tai, yaci gaba, kinyi gaskiya Hawwa ce agaba na a yanzu ke kanki kikaga Hawwa saikin zubar mata da hawaye, dakata Dr wai matsalar Hawwa itace tasa kayi wannan ramar duk kafuta hayyacin ka? Waishin wannan damuwar ita zata bawa Hawwa lafiya ne? Niban tab'a ganin mutum irinki ba Dr mai maida damuwar wani taka! Ganin ta hak'ikan ce tanata fad'a yasashi zuba mata ido har saida takai aya tana sauke numfashi,

Kamo hannun ta yayi kan yace" waime yake damunki ne FEENAT? Hawwa fa matata ce, da karfi tazame hannun ta" naji mai mata Allah yakara dankon auratayya" saroro yabita da kallo sai a wannan lokacin ya fahimci ba komai ke damun Feenat ba sai zallan kishi don haka yayi yar dariya kan yace" yi hak'uri uwar gida sarautar mata uwar biyu mata a gurin sama'ila burin sama'ila farin cikin sa nishadin sa kwanciyar hankali kai rayuwarsa ma gaba d'aya dungurum gum sadaukar wa ce a gurin ki, duk da taji zafinsa datake ji yaragu amma saida ta galla masa harara kan tace" to ai Kaine Dr dubi fa yanda kakoma saikace mara galihu? To ina naga galihun Fenat? Banidame kula dani ke kanki kinsani kinsan koni wanene kina sane kikazo gidan hajiya kika bata had'in kai kuketa ganan azaba, ada dake da Hawwa unajin saukin azabar da sonki tareda kewarki suke Dan danamin to a yanzu fisabilillahi waxan duba naji dad'i? Hmm ta sauke ajiyar zuciya kan tace" shikenan nizan dawo gareka in matar ka tasamu lafiya saina komo, nida baby muna buk'atar kulawar ka, "nafiku bukatar kulawar ku zan tabbatar miki da hakan duk sanda kukazo gareni, murmushi tayi tareda sinne kanta jikinsa,Jin furucin ta yayi masa dadi harsai da murnar sa ta bayyana ya rungumeta sosai cikin jikin sa, tashitai ta had'o masa abinci da kanta tadinga bashi yaci dayawa don rabonsa dacin abinci kamar haka tun yana tare da Feenat,ya dauki kusan away hud'u a gidan suna tarairayar junan su tareda sanya juna cikin nishad'i mara misaltu wa, Kansu rabu saida ta tabbatar masa da gobe zata shiga asibiti taduba jikin Hawwa, yaji dadin hakan haryaita samata Albarka.

FEENAT!!! Onde histórias criam vida. Descubra agora