BABI NA 22

289 26 0
                                    

[8/18, 5:56 PM] Mamanhaneef: FEENAT!!

BY Mamanhaneef

53

***Tun daga wannan ranar soyaiya me k'arfi tashiga tsakanin Hawwa da Dr wanda yake bata kulawar da ko a mafarki bata tab'a tunanin zai bata ba, wannan yasa ta kuma bada k'aimi wajen shaye-shayen magunguna wanda ta dauke su da mutukar muhimmanci don tanada tabbacin su suka jawo mata soyaiya wajen Dr, zuwa yanzu kuwa?zuwa yanzu kuwa? Idon ta yak'ara budewa duk wani gida da ake saida magani na d'aa Hawwa tasan shi kusufa kusufa saidai in bata samu labari ba. Kudi ko nawane batajin kiwar futar dasu don Dr ya sakar mata k'udi tanayin yanda taso kamar yanda innan ta ke fata.

Yanda Dr ya sakar mata kud'i haka nan ta sakarwa innan ta tareda da 'yan uwan ta, don har kayan d'aki ta canjawa innan ta Baban kuma tak'arama sa jari kannan ta maxa kuwa? Babu wanda bata sayawa babur ba, har cimar gidan saida ta canja, dama hakan innan ta keso don haka Hawwa tazamto 'yar gaban goshi gurin inna.

Kallo d'aya zakai mata kasan tana cikin kwanciyar hankali, Abinka da fara sai tayi wani irin kyau ga k'ibar data narka tak'ara mata kyau duniyar ta takeci da tsinke, A b'angaren Dr kuwa? Dama shi d'an rayuwa ne soyaiya ba? Yana girmama ta yana bata muhimmanci shi baiki ya karar da rayiwar sa cikin bautawa soyaiya ba sai kuma yaci saa don Hawwa tadokoshi a wannan fanni don ita a yanzu take tashen kuruciyar ta.

A b'angaren Nafisa kuwa?Ko kad'an bata d'auki Hawwa tad'ora cikin ranta ba, illah dama data bata ta more Amarcin ta ta hanyar d'auke idon ta daga lamuran su, tun takwas takan tafi asibiti inta dawo ma takanyi zaman ta a sashen ta duk don gudun karta ganewa kanta Abinda zai hanata bacci.

Har zuwa wannan lokaci Hawwa na matukar girmama ta tareda ganin k'imar ta sakamakon Jan girman ta ko kadan batason Hawwa taga damar ta balle tasamu damar raina ta.

Mu Amalarta da Dr kuwa? Tasamu nakasu matuka wanda shikan sa baisan dalili ba balle ita, wacce ta zuba masa ido kawai tana son ganin iya gudun ruwan sa,
[8/18, 8:21 PM] Mamanhaneef: Da farko taimasa uzuri donta fuskanci yana cikin d'okin Amarci ne,amma daga baya saitaga tamkar ya canja akalar dokin sa ne, don ko a mu'amalar su ta auratayya baya iya bata kulawar data dace wani zubin ma saita gwammace baima zo inda take ba, daga baya ma saiya tsiri bacci da wuri duk ranar girkin ta, inma ta isa nasa d'akin saita tardashi yayi bacci, to a gsky Feenat nada mutuk'ar hak'uri da zurfin ciki don ko a fuska bata tab'a nunawa Dr abinda yake mata ya dameta ba, balle Hawwa wacce da Sam batasan halin suke ciki ba don ko kadan bataga Alama na balle canji.

Ana haka ne Hawwa tasoma laulayin ciki mai zafi, wanda tarasa dukkan kuzarin ta kullum cikin kasala da laulaye laulaye, Farin cikin da Dr ya nuna tareda kwallafa rai akan cikin Hawwa xai baka mamaki, haka ma y'an uwa da abokan arziki suntaya su murna, Ab'angaren Nafisa ma ta tayasu murna, yayin da yan uwan Dr sukazo duba jikin Hawwa kulawar da sukaga Nafisa na bawa Hawwa tayi matukar birgesu duk da sunada tabbaci akan Feenat basu zaci hakan zasu ganta ba, don haka Anty halima da Anty Salma suka kule cikin uwar d'akin ta harma da Aminiyar ta ruk'ayya don suyi k'orafi akan rawar kan da suka riski Dr nayi akan Hawwa duk haushi yacika ransu su Sam basa bayan Hawwa don har yanzu hankalin su yaki kwanciya da ita don gani suke da wata manufa Innan Hawwa tayi kutun kutun tahada auren Hawwa da Dr,

Basu rabuba saida ta tabbatar musu da itafa batada wata matsala rawar kan Dr bai dameta ba don karuwar sa karuwar tace Abin da dai tasani Samu da rashi duk na Allah ne tana tsaka da yiwa kanta Addua don tasan bai manta da ita ba,

Duk wani lokacin sa da kulawar sa ya had'a ya taekata ya ajyewa Hawwa baida lokacin komai saina Hawwa inhar yana gidan baida lokacin komai sai nata, girki kuwa? Sai abinda takeso zaa girka cikin gidan duk Feenat ta d'auki wannan nauyin, maganar rabon kwana kuwa? Duk ya tattara kwanan ta yagadawa Hawwa da sunan kulawa tun tana lissafa kwanakin harta bata a lissafi,  ya bata d'awainiyar girki ya bawa Hawwa kwanan ta ko bi takan ta yadena duk kulawar sa tana gurin Hawwa, takaima inba cin Abinci ba babu Abinda ke Had'asu da Dr saiko in sun had'u a d'akin Hawwan.

Duk wannan bai dameta ba tasan tana cikin jarrabawa ne don haka ta dage da Addua ta zubawa sarautar Allah ido, tun tana mamaki harta dena, a Haka cikin Hawwa ya cika wata bakwai,

Zuwa lokacin tadena laulayi tasamu lafiya saidai d'an ciwo wanda baa rasa ba irinna mata masu tsohon ciki,  tayi kyau tak'ara kiba cikin yai mata kyau tamkar a sureta a gudu, yayin da Nafisa ke tayata duk wata dawainiya ta cikin kuma har zuwa wannan lokacin Nafisa ke girki ta daukewa Hawwa duk wata wahala, zuwa wannan lokacin ma lissafin kwana ya hargitse a gidan don rabon da Dr yazo dakin ta harta manta, ada takan dau kafa taje nasa muhallin ganin bazata iya jurar wulakanci ba yasa ta daina don yana tareda itane amma hankalin sa yana gun Hawwa, shikuma ya nuna mata tafa nono fari,

Wata rana suna zaune a falo suna hira Dr ya sasu a tsakiya suna hira cikin nishadi inka gansu zaka rantse basa cikin wata matsala, Nafisa kenan ta iya shanye bacin rai ga iya muamala da Dan Adam dik a yanda yazo mata,

Sunanan zaune Abu kamar Almara Hawwa tasoma jin ciwo kadan kadan kan awa daya ta shude ciwo yayi tsanani hankalin su duk ya tashi Sun kasa yimata komai don haka sukai gaggawar kaita asibiti a takaice dai Nak'uda tayi sosai a k'arshe ta haifi d'anta bakwaini babu rai,

Dr yashiga damuwa don ya kwallafa ransa ga abinda ke cikin Hawwa, haka nan dai sukai tawakkali suka Hak'ura amma hankalin Dr ya tashi ya boye damuwar sa ne sabida dalilai biyu.

Hakanan Hawwa tai jegon ta na tsawon wata daya a gidan su wanda  innan ta tatsiro da hakan da manufar tatsar kudin Dr, duk da ran hajiyan sa bai soba hakann ta yarda inna tatafi da Hawwa gida wai acan saitafi samun kulawa, kudin dai datakewa ta samesu don Dr baida kwauro duk zuwan da xai saiya zube mata kudi amma duk da haka saita bijiro masa da wata bukatar wacce zata ja kudi mai kauri daga hannun sa.

Haka dai tagama zaman ta cikin gidan dg bisani tasaka rikici a dole inna tabarta takoma dakin ta, bayan tasake gyaran jikin ta wanda takeshe makudan kudi wajen sayenkayan gyaran,

A bangaren nafisa kuwa? Tazata Rashin Hawwa a kusa dashi zaisa hankalin sa ya dawo gareta, Abinda bata sani ba Akwai illar da Hawwa tayi mata a sanadin shaye shayen magungunan ta wanda  yayi sanadin hana Dr samun nutsuwa da ita, to Abune Hawwa keyin sa tankar mara hankali koma nace Mara mafadi,

Anya Hawwa tanada Hankali? A dalilin son ta faranta wa Dr bata shakkar shan kowanne irin Magani komai tsadar sa zata siyeshi tasha babu ruwan ta dabin ka ida ko akasin hakan,

Anya kuwa wannan salon zai haifa Hawwa da mai ido kuwa?

FEENAT!!! Where stories live. Discover now