Kararrawan agogo ne take ta kadawa,ta katse wannan shirun na karfe 5 din asubahi;sanyin hunturu na ta kadawa a hankali,a wannan asubar da kowane mahaluki en yayi sallahn sa zai so ya koma bacci,MAIRO ma zata so hakan amma tasan ba mai yuwuwa bane sbd alarm ya riga da ya tashe ta,sannan son tayi aikin ta ba tare da bata lkc ba ma bazai barta ta koma ba,irin horon da aka mata a baya shima bazai barta ba,a hankali ta yaye bargon da ke lullube a jikinta tashi tayi tana mika gami da salati,ta kunna wutan dakin sannan ta kashe table clock din da yake yi,ta nufi bandaki domin dauro alwala ta fito ta dauki hijabin ta sannan ta tada kabbara,raka'atainil fajr ta fara yi kafin ta tashi ta gabatar da asuba,ta idar tai addu'oin ta ta shafa ta mike ta nade sallayan da hijab dinta,a hankali taje ta nade bargon ta sannan ta gyara gadon, ta kimtsa komai sannan ta canja kayan jikinta zuwa wata doguwar riga (khaki gown)wanda shine zaiyi nuni asan 'yar aiki ce wanda ke aiki a gidan masu akwai......
20mins after 5,tana cikin kitchen ta cika kettle da ruwa ta kunna socket din,sannan ta fita a kitchen ta nufi palour domin ta fara shara da goge2,ta gama ta koma kitchen ta tarar ruwan ta ya tafasa ta dauko flask ta juye sannan ta dauki ashana ta kunna gas,ta dauki tumatir da albasa ta yanka sannan ta dauko kwai ta fasa ta kada shi ta daura frying pan ta fara soyawa bata dauki lkc ba ta gama omelette,ta gama lkcn har karfe 6 tayi dai2 lkcn tashin 'ya'yan momy guda 2 domin ta shirya su zuwa mkrnt.
Kamar kullum tashi su shine aiki mai wuya da bata kauna,HAMDA ita ce mai kin tashi koh dah a lkcn zafi ne bare kuma a yanxu da ake lkcn sanyi sai ta kara shigewa bargo,HAMNA ita ce karama amma tashi ta bai ya mata wuya ko kadan,amma duk da haka mairo tasan yadda take tafiyar da hamna 'yar shekara 5 akan hamda 'yar shekara 9,bayan ta gama tashin su ne tai musu wanka da ruwa mai dumi sannan ta sa su suka dauro alwalar su,lkcn har half past 6.
Surutun hamda da hamna shi ya tashi momyn su daga baccin da ta koma bayan ta idar da sallar asuba,amma maimakon ta tashi sai ta kara jan bargo ta cigaba .....tayi2 ta cigaban amna bazai yuwu ba,anan zuciyarta ta tuna mata da schedules din da zatayi yau,tana cikin zancen zuci ne taji fashewan mug a dining area.....
Muryan mairo taji tana cewa;ke ce ko hamda?wa ya ce kije gurin?hamda tace bani bace hamna ce,kece mana hamda ina ganin ki ay cewar mairo,hamda ta kara cewa kofin ne ya fado ya fashe bani na fasa ba,mairo tace nasan ya fashe ay lkcn da kike kokarin zuba tea wa kanki ko?hamna tace nima zan sha tea din cike da kulawa mairo tace kar ki damu muje na zuba miki 'yar kirki,ki cigaba da halinki na kwarai kinji koh?hamna tace ehh gami da nodding kanta,ke kuma cup breaker sai momy taji abinda kikayi '.
Hamda tace en kika fada mata zan ce ke kika fasa ay,mairo tace momy tasan abinda zaki aikata ay,duk a wannan lkcn momy na jinsu tasan hamda zata iya kitsa hakan ta fada mata,sbd tasha yin haka a lokuta da dama kawai bata daukan mataki ne amma yau ta cancanci duka duk tana daga kwance take wannan nazarin ta daga kanta ta kai dubanta ga agogon bangon dakin taga har 6:50 yayi tace uhmm is tym to get up.
Lokaci kalilan ya ragewa HAJ.BATULA ta shirya zata so ta koma baccin ta amma yanayin aikinta da schedule din da zata je ta tarar a office dinta na secretary to the state gov't(SSG) bazai barta ba ta kara koh da minti daya ne .A kagauce ta tashi ta kunna wutan dakin dana bandaki ta shige domin tayi wanka.
Tana daga bandaki ta ji kukan hamna,kamar zata fita a bandakin taje taji mai ya faru domin tasan bazai wuce ita da hamda ba amma sai taji muryan mairo tana yiwa hamda fada akan dukan hamna na ba gaira ba sabar, ni ban dake taba taji hamda ta fada,mairo tace kin dake ta mana mutum ya taba kuka ba dalili ne,hamda tace tohhh kice mata ta daina kallo na tana fada tana turo baki,mairo tace toh laifi ne dan ta kalleki?bayan wassu dakikai momy taji kukan hamna ya lafa tasan mairo ta kashe zancen ne sbd taji ta tana rarrashin hamna;tace fyn gal karki damu cornflakes zan hada miki ita kuwa tea zan hada mata,da wannan momy ta maida hankalinta zuwa wankan data keyi minti kalilan ta gama wanka ta fito, tana gaban mirror tana kwalliya,zuwa lkcn su hamda sun gama karyawa sai tafia mkrnt.