22

608 44 1
                                    

Da wannan haj.batula ta rufe babin tunanin da takeyi ta miqa hannun ta dauko wayarta dan ta kira kawayenta kuma aminan ta domin neman shawarar su.

Ringing daya,biu haj.zahra ta dauka tana cewa aminiyata kaddai an gansu ne?ganin basu jima da suka gaisa da haj.batula ba sai yasa ta tambayeta a kagauce koh an gansu ne.

A'a wlhy kawai dai wata 'yar matsala ce ta kara kunno kai na batun ado dana baku lbr kwanaki,toh yau ya kara zuwa min da zancen ne akan lallai na tattara yanawa2 na bar musu gidan dan suma zasu taro su dawo nan da zama,toh shine nake so ki bani shawara akai kafin na dauki mataki,kar nazo na yanke hukunci cikin fushi.

Toh yanxu ke meh kika yanke zakiyi?cewar haj.zahra,eh toh dah nace zan kai zancen kotu ne amma wata zuciyar kuma take cemin en nayi hakan kamar nakai su babagana ne,shine nace bari naji ta bakin ki tukun dan neman shawara na da kyau.

Haj.zahra tace iyyy!kaiwa kotun ma yafi amma sai dai kaiwan kamar yadda kika fada kamar su babagana kikai,sai ki haqura ku kashe zancen a gida kuma ni a ganina zancen nan mai sauqi ce tunda gida yake ta ambata ki bada takardun su bana sauran dukiyar ba,gashi kuma tunda dadewa kika bamu lbrn akan da aka gama gina gidan tunda ran baban su hamda sunan ki yasa a takardun gidan,kuma a karshe ya mallaka miki halaq malaq.

Toh kinga free falo zaki fito ki nuna masa ya gani baro2 da idanunsa yaga dai sunanki ne a jiki,hasalima baya cikin gado don naki ne halaq malaq en bake bace kika sa a cikin kayan rabon gadon ba,bare hakan ma bata taso ba,dan haka nake tausar ki sannan ki tafi jama'are kije ki sami su babaganan ki basu lbr komai da yazo ya miki hatta cin mutunci daya miki ki fada har ta kalmar 'zaki gani' daya fada miki karki qi fada dan wannan kalmar akwai girma gareta.

A karshe kuma nake tausarki da ki kara haquri da halin kanin mijin kin nan,dama kannen miji ya aka kare dasu bare kuma dan uwansu ya mutu ya bar dumbin dukiya haka,kai wassu kannen mijin ma har Allah2 suke ya mutu suci gado abin yazama ruwan dare wlhy sai addu'a kawai.

Anan haj.batula tayi mata godiya da irin shawarwarin data bata kuma in sha Allah zata nunawa ado takardun haj.zahra tace ba komai wlhy aminantakan kenan,kuma ina so na fada miki dazaran kudin da ake jira ya kammalu toh maza kar ku bata lkc ki garzaya ki kira lauya koh malami a raba gadon nan ku huta da rigiman ado sannan ku saukewa mamacin nauyin dake kansa dan watarana kina ji kina gani ado zai halaka ku keda 'ya'yanki a banza akan abin duniya dan nasan da 'ya'ya maza ne gareki sai dai nace haka ado zai ganku ya kyale ku da zancen dukiyar nan dan koh kusa yasan bai da gadon.

Haj.batula tayi na'am sosai da shawaran haj.zahra a karshe tai mata godiya sannan ta kashe wayar bata tashi a gun ba sai da ta kira haj.surayya ta fada mata komai da suka tattauna da haj.zahra da irin shawaran da ta bata itama haj.surayyan tayi na'am da shawaran ni maryam ina daga gefe nace ohh wannan aminantakan na burge ni.

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now