Tana shirin kwanciya ne taji wayarta ta fara ruri,ta kai dubanta kan wayar taga bakuwar number ne,baya cikin ra'ayin ta daukar bakuwar number amma yanxu ya bi mata jiki ganin ana yawan kiranta ana mata jajen batan yaranta yasa ta miqa hannu ta dauki wayar ta kara a kunnen ta gami da cewa "hello",hello hajia shine muryar da taji mai maganar yayi,"wake magana",kar ki damu kanki da sai kin san mai maganar a gadarance ake maganar,saqo zan isar gareki kawai,"saqo kuma",eh saqo sauri nake ki tsaya ki saurareni,nasan yadda yaranki suke kuma suna raye.
"A cikin zuciyarta tace alhmdlhy,sanar dani yadda suke tana mai kara kusanta wayar da kunnen ta",bana son rashin nutsuwa kiyi shiru ki saurare ni,toh na nutsu ina jin ka zamu baki su amma da sharadin sai kin bi dokokin mu,"ba matsala fado min su",gobe ki taho da million biu in cash muke so,ki sa kudin a motar ki ke kadai muke buqata karki buqaci rakiyar kowa en ko kika zo da wani sai da wassu yaran bana naki ba.
"Ina ji",zuwa 6:30pm sai ki dauko hanyar awala hotel wato hanyar da zai kaiki kafin madaki,ki ta tafia har zuwa gubi,anan zaki bi wata 'yar hanya ta hannun damar ki sai ki gangara kiyi tafiar kamar kilometre biyar toh anan zaki ga 'yar bukka..."dan Allah ku mun rai duk ni kadai zani gun nan kusan magariba ga hanyar bata da kyau dan Allah ku ban yarana dokokin ku sunyi min tsauri dayawa".
'En har kina son yaranki dgsk follow my orders and do as i say kuma kiyi shiru na karasa miki sharudan,"cikin inda-inda tace cigaba toh ina ji",ki daina wani shashekar kukan ki joor ni taimakon ki zanyi,"na daina go ahead",yauwa kamar yadda nake fada zaki ga bukka sai ki shiga ki ajiye a tabarmar dake dakin,sai ki kama gaban ki,kuma ina kara jan kunnen ki karki kuskura wani yaji zancen nan bare har ki fadawa masoyin ki gwamna d worse din shine kice zaki sanar da police en har ki hada zancen nan da police just consider ur children death.
En har kika kiyaye wannan washegari zaki ga yaranki har gida da fatan kin gane?zanyi yadda kuka ce en har ban yarana 3 a raye,uku kuma mu yaranki biu ne a gurin mu dan babbar cikin su mun dade da shafe babin ta,gigitaccen kara tasa ki tare da fadin '''qalu innalillahi wa inna ilaihiraji'un''' ta tashi tsaye tana kuka sosai ni batula ya zanyi da raina 'yar da ba tawa ba suka kashe en har haka dgsk ne ya zan fara fuskantan iyayen ta da zancen nan.
A haka ta daure ta dauki hijab dinta ta zura tayi hanyar waje, koh wayar ta data tarwatse bata tsaya daukawa ba a haka ko baba maigadi bata shaidawa en da ta nufa ba ta dai fito kan hanya ta tsaya.
Tsirarrun napep ne ke wulgawa ta gabanta duk wanda tasa hannu dan ta tsayar duk basa kulata na karshen ne da ta tsayar ya tsaya sbd yaga yanayin ta kuma hankalin ta a tashe yake,hajia lafia,ina zaki?yarana ne wlhy daya kalleta sosai sai ya ganeta,ita ce ssg wanda ake ta sanarwan batan yaranta a tashoshin yada lbrai kuma gashi sai ambatan yarana take,hajia nagane ki ay an same sune?eh toh amma....maganar ta tsaya a dai-dai lkcn da take so ta fada mai dalilin rudewarta,amma sai ta tuno da kashedin su.
Ki fada min ko akwai wani taimako da zan iya yi miki,bawan Allah babu kawai ina so yanxu ka miqa ni gidan kawata dake nan bendel road gida mai no 28,shiga to muje sun iso yace hajia nan ne ko ta sauqo tace eh,jira na shiga na fito maka da kudin yace lah ki barshi na kawo ki _fisabilillah_ ne Allah ya bamu ladan niya ya bayyana yaranki kuma.
Ta kwankwasa kofa barr.shamsu ne ya leqo ya ga itace sannan ya bude mata ta shiga,tana mai yin hawaye sosai,haj.surayya da taji shirun yayiwa itama ta fito daga bedroom dinta da shirin su na bacci duk suke ita da mijinta.
Akan kujera duk suka koma suka zauna baza ta iya boye musu wannan zancen ba tuni ta fede musu daga biri har wutsiyar abinda aka kirata aka fada mata a waya,bayan sun gama sauraren lbrn da tazo musu dashi sunyi shiru sunyi jugum suna nazarin yadda zasu yanke abinyi dan wannan maganar tana buqatar nutsuwa haka suka je suka kwanta sai gobe su san nayi.
"Taya mutum zai yarda da maganar su zancen nan dole abi a hankali gashi sunce zuwa gobe suka bada..en aka tsaya muka ce zamu bata lkc zasu iya kashe yaran kuma en har mukayi ba yadda suke so ba nan ma yaran na cikin hatsari,gashi sun kara da cewa kar a shigo da hukuma zancen toh wane mataki zamu dauka?duk barr.shamsu ne yake kwance yake tufka da warwaran nan.
Yana daga kwance yake tsaka wannan batun har a karshe yace dole abi yadda suke so wato za'a kai musu kudin amma dole za'ayi alertn police.....a haka ya tashi ya danna wayarsa yaga asuba har tayi,ya tashi yaje ya dauro alwala fitowar sa ya tashi matar sa.
Sun fito dukkan su da shirin su wato kowa yayi wanka,ruwan tea kadai haj.surayya ta dora sbd barr.shamsu yace mata da wuri zai fita zai je gun acp akan case dinnan,haj.batula ce ta fito itama daga dakin da aka sauketa, itama tayi wankan ta tasa kayan da haj.surayya ta ajiye mata tasa en tayi wanka.