Afuwan afuwan 'yan uwa wannan page dinne kafin page din saman sa. D previous page is 21 nd dis is 20. Bear wit melkcn kawar haj.batula haj.surayya itama tana gidan ta kai mata ziyara.
Sun tarar da haj.batula a falo tana zaune,first lady ta zauna a gefen haj.batula tare da sakala hannunta ta wuyan ta,shima gwamna ya zauna a seater dake opp dasu,sun gaisa anan suka fara bata haquri gami da kwantar mata da hankali ta,sannan gwamna yakare da fadin "kiyi haquri haj.batula ki dau dangana in sha Allahu nan bada jimawa ba za'a ji lbrn su,har muna fatan Allah yasa a kama wanda suka sace sun.Makalallen hawayen dake idon haj.batula ya karasa saukowa kan kuncin ta first lady ta fito da handkerchief dinta ta share mata hawayen ta sannan ta cigaba da tausarta.
Haj.surayya dake kitchen tana bare-bare tana gaggawa ta fito tazo taga gwamna itama dan ta samu bada lbrn itama ta ganshi face2face#teasing lolz,ta fito ta leqa ta labulen falo kadan sannan ta koma kitchen din dan ta kawo musu snacks da drinks.Dauke da katon tray ta fito wanda yake dauke da snacks da drinks sai tumblers ta isa ta ajiye musu a center table ta zuba musu sannan tace 'bismillah' kana ta zauna kafin nan ta gaishe su.
Zuwa karfe 10 gwamna sunyi wa haj.batula sallama,haj.surayya itama baifi da mintina ba mijinta yazo ya dauke ta suka wuce suka bar haj.batula da matan da gwamna ya turo su dan su taya ta zama.
_innalillahi wa'inna ilaihirraji'un_ haj.batula ke ta nanatawa ta tashi cike da razana sakamokon mafarkin 'ya'yanta da tayi wanda ya zame mata jiki dan kullu yaumin en har dai bacci to zai dauke ta toh sai tayi mafarkin su gasu nan suna kuka suna miko mata hannun su ta riqe su kar a dauke kuma.
Ta miqa hannunta zuwa bed side drawer ta jawo wayarta taga karfe nawa ne,biyar saura ya nuna mata,tace kenan har nayi baccin awa 1 dan dama sai da ta idar da nafilar dare kafin ta kwanta tayi addu'a ta shafa sannan ta koma hannun damar ta ta kwanta kafin a fara kiran assalatu.
***** ****** ****
Kofar da zai sada ka da falo haj.batula taji ana ta bugawa ta amsa tace a shigo amma ba'a ji ba aka cigaba da bugun.
A ranta ta raya da'a ce su mairo na nan da mairo koh su hamda wani yaje da gudu domin ya bude kofar,amma yanxu ba yadda ta iya ita ce dole zata je ta bude kofar .Ta isa bakin kofar tace wane ne?da karfi taji anceb nine,taji muryan mai maganan amma bata dauki muryan ba ta kara cewa wane ne kai?sai taji ance ki bude tukkun sai kigane wa idonki waye ne.
Anan ne ta gano ba kowa bane illa ado kanin mijnta.Ta bude tana mai masa sannu da zuwa ta masa iso ya shigo ya zauna, ta zauna suka gaisa bayan dogon gaisuwa da tambayan mutanan gida duk da dai acikin damuwa take haka ta zage suka gama gaisawa.
Kafin nan ta wuce kitchen domin ta kawo masa abincin dasu abun sha,ta fito dasu food warmers ta jera a dining sannan tace mai yaje toh yaci abinci..dama babu irin wasan kanin miji tsakanin haj.batula da ado sbd kwata2 haj.batula bata shiga shirgin shi bare ta san jirgin da ya kwaso shi.