9

2.4K 70 0
                                    

Kusan sati kenan da mairo takara lura da limousine din nan da wannan alhj da 'yan koransa suna magana akansu kuma harda nunosu,harda suka dawo gida take fadawa momy amma haj.batula bata wani dauki zancen da muhimmanci ba.

Kwanaki sun ja,wani dare haj.batula ta dawo a gajiye a wurin aiki bata buqatan komai sai dai ta ganta a kwance tana hutawa bare yau da sukayi meetn da ya dau dogon lkc,meetn din da sukayi a ofishin gwamna da duka ciyamomin 20 din *lga* councils dake cikin jahar.
Sai after 6 suka gama meetn din, a wannan lkcn da take shirin tafia gwamna ya kara ce mata ta jira na wassu mintuna,wanda tattaunawansu ya kaisu har awanni.

Sai kusan karfe 8 ta iso gida tun daga jin dirin motan momyn su suka san ta dawo kafin tayi horn har sun fito dukkansu domin bude mata gate.mairo ta bude mata gate ta shigo tai parkn din motar a ma'adanar ta.fitowan haj.batula daga mota ta hadasu dukkansu ta runguma a maimakon dah da take rungumar kowa da daddaya.
Yanayin momynsu ya nuna musu agajiye take sosai sai yasa kowa ya hadiye korafinsa a cikinsa sbd yau bata ta raba fadan abinda ya faru in her absence,mairo ta bude back seat dan fito da abubuwan ciki handbag ne,files da wassu kayayyakin a leda wanda bana dauke hasashen snacks ne data saba taho musu dashi ne.

Sanin mairo tasan za'ayi rigima tsakanin hamda da hamna akan wanda itace zata dauki handbag din momy,babbar kwabo hamda ita ta kafe ita zata dauki handbag da mairo taga tana shirin tada rigima nan ta lallami hamna uwar haquri akan ta dauki ledan snacks kuma en ta dauka yau ita zatayi iko akanshi sai ta ga dama ta bama kowa,#kuji mairo mairo da daurewa hamna gindi fa bayan nima nan 'yar samosan dana hango raina ya raka lolz.

Shine karshen gardaman su suka shige ciki.momy kam dama tana gama hugging dinsu tayi shigewarta ciki dan taje ta watsa ruwa mai dumi koh ta huta gajiya dama tun a can tayi sallolin ta.

Su mairo sunyi dinner su already momy ce kadai taci nata,tagama cin abincin ta shigo palour ta zauna lkcn karfe 9 dai2 da za'a fara national news duk da tasan jikinta na buqatan hutu amma son taji mai yake faruwa a kasar bazai barta ba.haka ta karyata jikinta ta zura idonta akan tampakacecen plasma dake jikin bango.
Mairo suna zaune a wani kebantaccen wuri da aka ware acikin palour dan studyin tana koyawa hamda da hamna assignmnt dinsu da aka basu;hamda a qunantitative reasoning while hamna kuma verbal apptitude.

Farkon news headline din da aka fara fada shine kidnappn din yara da akayi aka je boyesu a boyayyen wuri da ba'a sani ba wanda halin yanxu ana kan bincike hakan.

Sai second headline shine bude sabon kasuwa da gwamna ya halarta a garin udubo na karamar hukumar gamawa. Yadda haj.batula ta kishingida ta bada fuskan ta wa *tv* sai kazata hankalinta na kan news din ne nan koh ta dade da yin bacci.baccin dayake cike da mafarkin abin sonta wato mijinta uba gasu hamda,a lkcn ne ta farka taga ashe mafarki takeyi hakan ma akan kujera a kwance kuma a falo ita kadai ta daga kanta tabi ko ina da kallo taga babu kowa a palour sai ita kadai hakan na nuna mata cewa mairo sun tafi makwancinsu.

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now