11

1K 65 0
                                    

Akan su bata shawara akan tana so ta sayi gida meh suka ga a yin hakan?haj.surayya tace lallai ne sayan gidan?naga already kina da gidanki mai kyau ga ki a cikin sa ba haya kike ba bare kice zakiyi naki na kanki,sai dai ki godewa Allah,sai dai en dan qadara kike so,haj.batula tace alhmdlhy wannan gidan mijina ne na gode Allah,amma kunsan 'yan uwan mijina har sunyi furucin cewa ba nawa bane;dgsk?cewar haj.zahra,iyyi dgsk a takaice ma wannan kanin mijin nawa ado ya aiko min da text akan duk wassu takardun qadarori daya kunshi na gida,motoci dana filaye na kammala su ya dawo ready zai zo ya karba dan ba nawa bane ni kadai.

Cabbdijam!!! Cewar haj.surayya,toh ni dana ga zancan haka bana gani nai shiru bane shine na tashi na tafi jama'are takanas dan naje na fadawa babagana (surukinta) na kwashe duk abinda ado ya min text na fada musu,amma shine babaganan yake cemin bada yawun kowansu ba ya aikata haka,har yake cemin meye zasu tada hankali a abin magada,kuma gashi akwai magada kawai dai fitinan ado ne da yake so ya girbi abin da bai shuka ba.
Iyayen mijina sun ce min karna damu da zancen ado bare har na dauke shi da muhimmanci as far as dey are concerned,kuma hamda da hamna sune da gidan babu wanda ya isa ya koreni as long as jikokinsu dasu suna nan a raye.

Ki godewa Allah da ya baki surukai masu son ki cewar haj.zahra,haj.surayya tace sannan kuma ki kara gode masa daya baki 'ya'yan da zasu gaji dukiyar.haj.batula tace haka ne kam kullum ina kara gode masa dan ba danshi ba bazan kai matsayin nan danake ba.
Toh yanxu da na gama fada muku meh kuka ga ya dace nayi?haj.zahra tace ay wannan ba zancen daga hankali bane abinda akwai magada meye na tada haka?haj.batula tace halin adon ne sai shi dan iyayensa ma bai wani dauke su da muhimmanci ba dan ba abin da bazai iyayi ba dan ya mallaki gidannan ba.haj.surayya tace mu shawaran mu dah zamu baki shine en har dai zaki sayi gida toh a matsayin qadara zaki ajiye bawai dan ki saya ku koma ba abinda ko ina kuka je an san gidan nan na magada ne meye zaki daga hankalin ki Allah ya so ma kin tari zancen da wuri har kika kai gaban surukan kin mu a karshe abinda zamu ce miki Allah ya kade hau da fitina sannan ya rabamu da fitinan dangin miji irinsu ado masu tada zaune tsaye cewar haj.zahra.

Mairo tace lallai yau momy naji da bakin *'yan gayun ta* da ta laqaba ma suna don momy zuwa tayi ta umarci mairo da ta dafa special dish wa baqinta kafin magariba tayi suce zasu tafi.
Haj.zahra sunci sun sha kafin suka hau shirin tafia gida sun fito a falo sukayi wa su hamda da mairo ihsani sannan momy ta musu rakiya ta dawo.

**** **** ****

'Yan tenders board sun gama decidn wanda zasu ba ma kwangilar.yanxu sun miko shi gaban gwamna ya tantance shi sun kamata a basu?mai girma gwamna ya dauki report din yana going through,amma a mamakinsa duk kwangila 3 duk sunan kamfani daya yake gani wato *ncc* su zasuyi.ban taba sanin wannan kamfanin har tayi karfin d zata iya tituna ukun nan ba,amma naga sabo ne sbd bansan sunan su ba sai kwana nan duk gwamna ne yake magana shi kadai.

Yai ta studyn reports din da yan boards suka aiko dashi amma yaga sun hana kamfanoni da yawa wanda suka fi ncc tashe...a lkcn ya kira zuwa office din *ssg* ta wayar intercom din office din,haj.batula ta daga wit much respect,yace mata tazo office dinsa nan da wassu mintina tace bah damuwa gani nan tahowa.

A lkcn ta tashi ta kimtsa table din ta sannan ta fito tayi hanyar office dinsa sai da ta fara ratsa office din *PA* sa suka gaisa ta shige faffadan office din gwamna bazan iya wassafa muku girmanshi ba amma kuyi imagine how big it is lols.

Ta zauna ya miqa mata reports din gabanshi yace gashi taje ta karanta tai studyn din shi ta fahimci mai report din ya dosa,amma kafin nan tai photocopy ya nuna mata xero machine din a wani angle dake cikin office din sai ta dauka ta bar mishi na shi,sannan ya kara da gobe in sha Allahu za'ayi meetn akan shi da entire cabinet
Ta gama photocopyn ta miko masa original din,ya mata godiya sannan ita kuma ta masa sallama ta fito.

Bayan fitowanta ta koma office dinta ta nutsu ta zauna sbd tai studyn report din tunda gwamna yace mata gobe akanshi za'ayi meetn,lkcn tashin ta yayi ta bude drawer ta mayar akan sai gobe en ta zo zata karasa dubawa,unknown to her bata san kowani irin lkc zata dauka tana dubawa ya wuce zaton ta ba.

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now