32

611 45 0
                                    

Tambayoyi sosai alhj.tahir sule ya amsa da horo mai tsanani da aka masa akan yana da hannu a sace su mairo tunda ga number sa ne aka ga a binciken da akayi,"anan ya shiga ce musu shi bai da hannu ko kadan a sace yaran haj.batula hasalima yayi amfani da wannan damar ne ya sa driver shi ya qira haj.batula akan ya mata barazana en tana son yaran ta ta kawo 1million ta karbe su sbd mun taba bata kudi ta mana wani aiki batayi ba shine nai amfani da wannan damar don kudin mu ya dawo gare mu,kuma zancen kira driver na ne na bashi number haj.batula akan ya kirata ashe shi da wayana ya dauka ya kira, kunji yadda number na ya shigo zancen.

Dauda driver ga alhj.tahir da abokinsa mati sune suka je daukan kudin aka kama su kuma wannan bukkan na gonan su mati ne anan suke shiga su huta en sun zo aiki gona.
Yanzu haka duk suna rufe akan lallai sai an tabbatar da babu sa hannun su a sace yaran kafin a sake su,alhj.tahir shima ba'a barshi ba.

Matasa 4 nan ne ake ta gana musu azaba amma sunqi fadan wanda yasa su,dattijuwar ne da taji azaba ta bayyana tabbas sune suka sace yaran haj.batula kuma su suka nemo ni akan nazo ina musu girki akan kudi tsugugu ni kuma en dai akan kudi ne ba aikin da bazan yi ,amma basu bayyana min wanene ogansu wanda yake sa su ba.

Da suka ga dattijuwar ta fallasa su shine suka fito suka fadi sunan wanda yasa su wato dr.hameed katagum wanda shi da alhj.tahir sule duk 'yan ncc ne.
Ba'a bata lkc ba aka tura wassu polisawan suje su taho da dr.hameed,an je gidansa tun daga gate a kulle yake babu wani alama da zai nuna akwai mutane a gidan.

Wani daban samari suka tsaya suka tambaye su koh sun san yadda dr.hameed ya tafi,anan samarin ke fada musu yau kwanan su 4 da tafi philphines shida iyalan sa,sun musu godia suka tafi sun fadawa acp akan baya kasar duk shi da iyalansa suka tafi,acp yace shikenan ay dole ya dawo kasar tunda ba ba gidan iyayen sa bane anan, kuje dole ya shigo hannun mu dama ya san shi mai laifi ne sai yasa ya gudu tun kafin a binciko shi.

Sauran kudaden da ake jiran hallaruwansu na marigayi alhj.aliyu maidala miji ga haj.batula duk an aiko musu dashi ta details din account din haj.batula dayake yana da shares (hannun jari) a kasashen waje duk sun kammala har an raba musu gado kamar yadda addinin islama ya tanadar.

Malamin da yayi rabon gado a karshe ya fadawa ado baya cikin magada tunda mamacin yana da iyali kuma yana da iyaye toh su suke da gadon sa amma in d absent of iyayen mamacin wato sun rasu toh kana cikin magada.amma en baka ciki abinda za'a iya baka bai fi kayan mamacin ba sbd kai kafi cancanta da'a bawa.

Ado daya dauko malami takanas dan ayi rabon gado wanda shi duk a tsammanin shi yana ciki magada amma sai yaji akasin haka sosai malamin ya masa nasiha ya daina rawan kai a abun magada koh da yana da gado ya daina nunawa shi dukiya yake so abin duniya wanda gado a kaddara ake samun shi ta dalilin mutuwar wani ake samun shi ina abin farin ciki da nuna zalama anan,sbd gashi yadda ya tada kashin wuya a zancen sai haj.batula sun fita a gidan amma karshe cell aka kai shi aka gana masa azaba a abinda bai san hawa ba bare sauqa aka kamashi a bisa furucin da yayi kafin batan yaran da bayan batan yaran haj.batula sbd ana zargin sa da yana dasa hannu a batan 'ya'yan 'yan uwansa kuma duk bakinsa ne ya jawo masa.

Nasihan malamin ya ratsa ado sosai anan ya nemi gafarar iyayen sa da haj.batula daga rana mai kaman ta yau ya daina halaiyar ya dawo changed person zai tashi ya nemi na kantsa dan dogara ga kai shine wadatar zuci,kuma ya horu a hannun police ba kadan ba kuma hakan ma da taimakon haj.batula aka fito dashi.


***** ****** *****

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now