Ta karaso ta zauna ta gaishe su sannan take cewa barr.shamsu ya taji yana cewa zai je ya fadawa acp maganan bayan sunce kar a yadda hukuma ta shigo,babu wata hanya da zamu bi daya wuce wannan tayaya kenan?haj.surayya ta tambaye shi.
Yanxu ace haj.batula ta tafi da kudin da suke buqata jar wurin da suka kwatanta mata kuma ita kadai ta shiga ta ajiye musu kudin kuma da ta shiga bukkan ba kowa kinsan tun ana za'a san baza su cika alkawari ba,hasalima babu mai wayon da zai zauna a bukkan,kima baza su so a kama su so early ba,amma dole a duk yadda suke suna kusa da gun dan su hango zuwanta da kudin.
Kuma ace ta ajiye kudin ta tafi kuma wanda suka sa ta kai kudin sun fito daga maboyar su sun dauki jakan kudin,toh kunga anan bamuda guaranteen zasu fito da yaran sun riga da sun tafi kenan kuma sun ci bulus.
Amma kinga en muka sanar da police zan fada musu su san yadda zasuyi suje wurin da aka ce taje kuma dukkan su shigan muftis zasuyi appearn kamar manoma masu aikin gona kuma tun da wuri zasu je suyit surroundn din gun bawai tare zasuje da ita ba.
Yamma nayi ita kuma sai ta kama hanya ta isa ta ajiye kudin kamar yadda suka umarceta kunga dole bayan tafian ta su fito a maboyarsu su je su dauki kudin,daga nan police din da suke zagaye a gun zasu fito suyi arrestn dinsu daga nan a tisa keyarsu zuwa en da suka boye yaran.
Kunga anan dole a sanar da acp....haj.batula da haj.surayya suka hada baki suka ce kwarai kuwa wannan shine mafitar.
A gurguje ya kurbe tea dinsa ya tashi yana haramar tafia sannan ya dora da lallai haj.batula tana gama karyawa itama ta shirya ta tafi gida domin ta samu taje tayi withdrawing kudin daga nan en da hali ki wuce office sbd karki nuna sarewar ki ta yuwu ko ina kika js suna bibiyar ki,kuma duk abinda ake ciki zan kira ki dan haka wayar ki tazamana a hannun ki,ya fita itama ta kurbi ruwan tea din badan rai naso ba kawai da ya riqe mata ciki daga nan tayi sallama wa haj.surayya ta kamo hanyar gida...
Zuwan sa ya sanar da acp komai acp yace maza ya tashi ya tafi sbd wanda suka kafa sharadin kila sun san alaqar ka da haj.batula kuma ta yuwu suna bibiyar ka kuma baza muso haka ba zai bata mana shiri,dan haka kome ake ciki zamu na waya ya fita yana godia.
Kusan azahar barr.shamsu yana office dinsa mutane biu suka shigo suka nuna masa id card dinsu daga nan ya gane sune sergeant din da acp yace zai turo masa duk suka masa bayanin yadda plan din su zai kasance,sai yaji ma plan dinsu ya sha bam-bam da nashi suna gama fada masa suka tafi.
Kamar yadda suka ce masa ya kira haj.batula ya sanar mata a lkcn ya kirata "yah kinje bankin kuwa?eh,kina ina yanxu haka,ina office ,yauwa ki nutsu kiji mi zan fada miki akwai sergeant biu da zasu bi ki ku tafi tare kuma ba gidan ki zasu zo ba,sunce tun kafin 6 zaki fito dai-dai gidan man *oando* zasu tsayar dake kamar masu neman ragin hanya kuma muftis zasu sa,ina kin gane gidan man?eh ina wanda ke hanyar maiduguri road,yauwa nan toh zasu tsayar dake sai su shige motar daga nan zasu miki bayanin komai".
Kin fahimta koh?eh,ki dau haquri zasu kare ki in sha Allahu duk da mai duka mai komai ne ke karewa,zasu san yadda za'ayi suyi dabarar da za'a ce lallai ke kadai ce a motar dan haka ki kwantar da hankalinki ki ci abincin ki sannan ki shirya ki tafi,wish u best of luck na gode sosai Allah ya saka nan suka kashe wayoyin su.
La'asar nayi ta fito ta kamo hanyan gida tana zuwa ta gabatar da sallahn ta kafin nan ta jawo abincin da ta tsaya ta saya a hazibal domin taci ,duk da har yanxu tana tararradin tafian ta.