2

2.4K 154 4
                                    

2⃣.Karfe 7:05am mairo suka kwankwasa dakin momy ta bude musu suka shiga da sallama suka gaishe da momyn su mairo ma ta gaishe ta,momy tace har kun shirya? Mairo tace eh;momy tace kuban mintina na karasa shiryawa,ta gama ta fito tace wato dear hamda kin kara fasa wani cup din ko?(momy irin mutanen nan ne wanda kudinsu bai rufe mata ido koh kadan ba bare har ya makantar da ita na rashin kwabar 'ya'yanta en sunyi ba dai2 ba kamar wassu yaran masu akwai da ake barinsu suke abin da suka ga dama baza a san illar hakan ba sai sun girma lkcn za'a ga illar rashin kwabar da tsawatarwa) hamda da sauri ta daga kanta tana kallon mairo wanda a zaton ta har mairo ta fadawa momy ne..ki ban amsa na,dah kike kallon mairon ba itace ta fada mun ba duk naji abinda kikayi ne,ni ban fasa ba faaa da kanshi ya fadi ya fashe',momy tace kawai da kanshi ya fashe kika ce ko?bayan babu mai fasawan sai ke,shiru kake jin hamda data buya a bayan mairo,momy ta kara cewa wat next kuma zaki kara fasawa?bazata kara fasa komai ba,cewar mairo data ari bakin hamda taci albasa,momy ta katse mairo ki barta ta bada amsar da bakinta',hamda tace bazan kara fasa komai ba momy tace da kin kyauta kuwa amma en kika kara fa meh zan miki?tace duka momy tace gwanda da ke kika zaba da kanki amma sai ki gujewa faruwar hakan kinji dear hamda nahhh...momy ta kamo hamna da hamda ta rungumesu ta musu Allah ya bada sa'a su dawo lfy.

Da wannan mairo ta rike hannunsu suka kama hanyan mkrntrsu DOLPHIN MARIA wanda mkrntr ta kasance nursery,primary da secondary ne dake cikin G.R.A,na garin bauchin yakubu tafian 5mins ne yake kai su sbd zamowarsa kusa sai yasa mairo take rike hannayensu ta kai su sai taga sun kule sun shige cikin skul din kafin take tafia...tsabanin momy da tun lkcn data sallami masu aikin gidan kuma kafin a kawo mairo a gurguje take kai su a motarta ta ajiyesu duk sbd kar tayi latti a wurin aikinta,amma bashi ke hanata lattin ba,silar samo mairo kenan dan ta taimaka mata da wassu aikin gida wanda a halin yanxu mairo ta fara taka rawan FIYE DA 'YAR AIKI.

A gurguje mairo ta juyo dawowa gida sbd tana so ta dawo taga tafian momy kar ta dade tai ta jiranta,tana isowa kuwa momy har ta fito tana cikin motar ta C200 taje bakin window tayi wa momy sallama sannan ta tambaye ta mai za'a dafa a lunch momy tana murmushi tace muna maraba da kome zaki dafa mana,momy tace toh a kula da gida tace in sha Allahu momy ta fita a gate na biyun da baba mai gadi ya gama bude mata yaje bude mata na farkon,mairo ta maida na biyun ta rufe ta wuce cikin gida,momy ba ita zata dawo ba sai 5pm,'mairo da baba maigadi sune kadai ma'aikatan momy..baba maigadi yana zaune da matarshi a cikin BQ dake compound din farko sun manyanta sosai shida goggo biba har yanxu Allah bai basu haihuwa ba surukan momy dake garin jama'are su suka sama mata su wanda a halin yanxu momy ce ke tallafa musu da komai....

Wannan kenan!!!

Sai yanxu mairo zata samu nutsuwa itama ta karya kumallo sannan ta dan huta na wassu lokuta ba mai yawa ba sannan taje ta dora abincin rana,en ta gama girkin taga da sauran lkc kafin a tashi su hamda sai taje gun goggo biba ta taya ta hira. Zuwa karfe 1 na rana zata tafi taje ta dauko su,su dawo ta cire ma hamna kaya sannan ta dan watsa musu ruwan dumi dan su wartsake daga gajiya sai ta sasu suyi sallah sai a tafi dinning area aci abinci sai su huta na wassu lokuta kafin 3:30 yayi ta shirya su zuwa islamiyya dake cikin unguwar.

Mairo sa'idu,'yar aiki a gidan haj.batula 'ya mai hankali,ga sanin ya kamata indeed mairo was God sent,'yar shekara 15 tun daga ranar da aka kawo ta daga garinsu toro ta hannun kawar momy, mairo ta dawo kamar 'yar gida bata da baqunta gashi ta samu uwar daki tagari momy bata da matsala koh kadan bata da takuri ta dauki mairo kamar 'yarta yanayin aikinta ne ma yasa ta sakar wa mairo duk aikin gidan wanda mairo ita a gunta bai taka kara ya karya ba sbd a gidansu tana yin fiye da haka....amma duk ranar datake gida tare suke komai. Tasowar hamda da hamna kuwa sun dauka mairo yayarsu ce,mairo kuwa ba matsayin yaya ta zamo musu ba har matsayin uwa ta taka,dan lkcn hamna na kindergertin mairo goyon ta takeyi ta kai ta,a hankali suka fara girma suka fara sabawa da ita akan uwarsu musamman ma hamna,koh suna cikin matsala da kawayensu na makwabta ita take magance musu,ita take wankansu,ta sa musu kaya,ta taimaka musu da assignmnt,ta kaisu mkrnt sannan ta musu mai kankat din wato ta dafa musu abinci hakan ma wataran ta bawa hamna a baki....kunga kuwa dole mairo ta taka rawar FIYE DA 'YAR AIKI.....

Kufa makaranta meh kuka ga ya kamata ta taka rawan?

Ku biyoni

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now