Babana matansa 3,mamana(mama asabe)itace uwargida tana da 'ya'ya 5,nice ta hudu,sai ta tsakiyan (babah gambo turaki) tana da 'ya'ya 4,sai ta karshen(babah ruqayyah) tana da 3.duka 'ya'yan babanmu mun tashi 12 kenan,yayuna guda 3 suna da ilimi sosai,sai nima kamar su nake dan banda matsala da karatu en dai na addini ne dana boko kai duk 'yan dakinmu ban dauke kowa ba en dai ilimi ne kuma both na bokon da na addinin,tsabanin sauran yaran matan babu wanda ya damu da karatu bare kuma na islamiyya da sai sun ga dama,en banda 'yan dakin mu babu wanda yagama primary bare har aje ga secondary.momy tace kenan babanki ne ya hanaki sbd sauran 'ya'ya'yen matan gidanku?eh kusan haka ne babanmu ya kasance shiru2 kuma mai mataccen zuciya wanda baya iya hassala wa iyalansa komai sai abinda matansa sukayi,sauran mata biyun wanda suka hada kansu suka dawo da babanmu MIJIN TACE koh mai suka fada masa sai ya hau kai ya zauna,har daga baya suka ce masa ya hana 'yan dakin mu zuwa mkrnt tunda suma ga 'ya'yansu nan sun hanasu xuwa,suna zaune sbd rashin kudi sannan nauyin ya ragu wa babanmu yaji da ciyarwan dayake yi,bayan ko ciyarwan sai an ta aike zuwa shagon shi(na daukan hoto) dan a karbo kudin cefane,amma har suke cewa ya hanamu zuwa mkrnt bayan koh ciyarwan sai a slow,amma dayake mamanmu tsayayyar mace ce wanda bata daukan wargi tace wa babanmu ita taji ta gani zata cigaba da daukar nauyin mu duk da dama bai taka karah ya karya ba,a haka da 'yan sana'ointa ta samu take biya mana buqatun da baifi karfinta ba sbd kar ayi ba wan ba kanin.mamanmu ta dage taga mun ilimantu dan zamanin yanxu sai da ilimi dan duk wanda muka ga yana jindadi a kasar nan toh sai da yasha wuya ba daga kwance yakai ga samu ba kuma Allah yace tashi en taimake ka....da wannan nasihun maman mu yayuna maza suka tashi tsaye suka fara buga-bugan aikin karfi dan su tallafi karatun su....
A halin yanxu haka ma yayuna uku duk suna mkrnt kuma da taimakon sana'oin da maman mu keyi da dan buga-bugan da sukeyi suke sec skul dinsu cike da sa'a,kuma basu cika dawowa gida hutu ba;toh ina suke zama ?cewar momy,daya wanda muke kiranshi yaya kb yana kaduna wurin kawun mu anan yake karatun shi wanda ahalin yanxu yana ss3 a command day sec skul kuma shine babba,sai wanda take binshi Aisha wanda ake kira da yaya shatu itama tana gombe wurin kanwar mamanmu tana ss2 a gg doma,sai na ukun wanda nake binshi yusuf yana jos wurin dangi maman mu yana js3.momy tace amma shirin mamanku nan yayi Allah yasa ku jiqanta kamar yadda take jin naku,yadda ta tashi tsaye duk dan kar ku wulaqanta taga kun sami ilimi wanda dashi kowa ke tutiya a zamanin yanxu,toh; ke kuma meye shirin maman ku akan ki?shine yadda ta barni nazo nan kuma haka Allah yaso,kuma momy kin tuna randa aka kawo ni nan maman mu tace a fada miki kudin aikina kina tara mun,eh;na tuna toh shine kinga en nayi aiki na shekara 2 koh 3 kudin aikina zai isa a mun hidiman karatu na dashi ba tare da mamanmu ta wahala ba.shawaran nan yayi cewar momy ni kuma in sha Allahu zan na adana miki kudin ki harda riba ma zan kara miki,kawai dai ki zamo yarinya mai hankali da haquri baza ki taba dana sani ba.mairo tace in sha Allah zan cigaba......
Wannan kenan!!!
Tun daga wannan lkcn momy taji son mairo da tausayin ta ya kara shiganta sbd hankali da haqurin ta,kuma duk son da momy take mata itama haka take son momy kamar soyayyar 'ya da uwa,babu mai daukan uwargijiya ce da 'YAR AIKIN ta.