18

610 43 0
                                    

Haj.batula mata mai cikar diri wanda yake tafia da dumbin kyawunta amma dare daya ta zabge ta lalace sbd alhinin rashin 'ya'yanta da 'yar mutane data mata laqabi da 'yar amana amma har wa yau shiru ba lbrn su.police kullum a cikin bincike suke sai dumbin tambayoyin da suke ta yiwa haj.batula "bakya zargin kowa wanda yake so yaga bayan 'ya'yan ki ?,har kin yarda sosai da 'yar aikin ki wanda kuke kiranta da mairo sa'idu?,bakya zargin mairo zata iya hada baki da kidnappers din?,irin wa'yan nan tambayoyin da suke yi mata kullum shike kara hargitsa mata lissafi yakai zuciyar ta da fara zargin 'yar yarinya data tabbata baza ta iyar cutar mata da yaranta ba bare kuma har tasa wassu mararsa imani su sace su no nooo mairo baza tayi hakan ba dan mairo na kula mun da 'ya'yana sosai wanda ba ko wace 'yar aiki bace zata kulasu haka ba kai ko ni nan iyakacin kulan da za su samu kenan kai ko cikin masu aikin zamanin nan mairo *fiye da 'yar aiki take*.

         A wurin haj.batula police din suka nemi jin lbrn mairo wanda tace musu 'yar toro ce,da bayanin da ta musu suka isa garin toro gidan su mairo,basu sha wuya ba aka nuna musu gidan mal.sa'idu mai hoto,sun ko yi sa'a yana gida.a bakin police din mal.sa'idu ke jin bacewar 'yar shi wanda jin hakan ya razana shi sosai dan basu ji lbrn batan ta ba sai yanxu da police din suka zo domin bincika ko mairo ce keda sa hannu a batan su,mal.sa'idu ya laqaba alhakin batan mairo akan uwar ta mama asabe wanda duk ita ce tayi babaucin tura 'yar sa aikatau gidan masu akwai kawai dan ta samo kudin da zatayi karatu kuma bazai lamunci batan 'yarsa ba koh sama da kasa zasu hade sai ta nemo masa'yarsa kila ma a gidan masu kudin aka sayar da ita duk mal.sa'idu ke zancen zuci nan.

          Anan mal.sa'idu ya shiga gida yana wani cika yana batsewa shi a dole 'yarsa ta bata da zafi ya shiga kwala kiran mama asabe duk suka fito anan ya shaida musu dalilin hargagin sa mama asabe mutuwar tsaye tayi sannan ta razana kuka take tana roqan Allah yasa a gansu kuma yasa suna hannun na kwarai.kishiyoyin ta kuwa a fuskan su sun nuna jimamin su amma a xuci murna fal suke dama suna bakin ciki da cigaban 'yan dakinsu mairo.

  Anan gidan su mairo kadai  uwar tace ta damu da batan 'yar ta,toh ga mal.sa'idun shima ya dan damu amma yafi jin haushin mama asabe sbd ita ya dorawa laifin batan mairo bayan bai san komai na Allah ne.

      Ganin da police din sukayi koh kadan 'yan gidan su mairo basu da masaniyar batar ta sai suka haqura da abinda ya kawo su suka bige da lallashin suka zo yi kar su damu in sha Allah zasu gano yadda suke har da wanda suka dauke sun.

       Bincike dai bai bar kowa ba hatta kawayen su hamda suma sai da aka je gidajensu domin musu tambayoyi.acikin kawayen sun wassu sunce sun ga mairo tazo ta dauke su ta riqe su amma basu lura da wassu mutane na dabban ba.

       A bangaren gwamna shima yana nasa hobbasar yaga an gano kidnappers din,sbd a wannan yammacin ne ya gayyato ass comssn of police zuwa wurin shaqatarwa shi dake guest house dinsa,suna zaune a kasan wani open hut mai dauke da hadaddun kujeru shakatawa,bishiyoyi masu kyau ne suka kewaye wurin sannan grass carpet ne a malale a gurin,akan center table din gaban su cike yake da kayan dadi kala-kala abubuwan sha iri-iri kai wurin nan is extremely beauty wanda ni maryam.nace wurin nan da wurin masoya ya dace ba na gwamna ba hakan ma da wani wai dan sanda *lolz* kai ku gudu masu karatu kar su sa a kamo mu woo no my water inside.

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now