Bayan ta gama shirin ta barr.shamsu ya sake kiranta yace ta turo masa number da aka kirata dashi jia sbd ana so a binciko mai layin.
5 minute to 6 ta fito ta kulle ko ina na gidan tayi wa baba maigadi sallama ya mata Allah ya bada sa'a ta shige motar ta da bismillah ta chale bisa titi.Round about ta zaga kafin nan ta mika zuwa ga hanyar da zai sadata da gidan man oando ta shiga ta mashigar duk tana ta zuba ido koh zata hango mutane biu da aka fada mata har layi yazo kanta ta bude tank dinta aka sa mata 10 litres amma har yanxu idon ta bai gano su ba sai da ta dau hanyar out din station din ta gansu tuni suka mata alama da hannu akan ta tsaya ta musu lift sun bude sun shiga suka mike zuwa yadda suka dosa.
Daya a gaba daya a baya haka suka zauna tana ta tukin ta a nutse da zuciyar ta fal da tararradin zuwa sun kusan daukan hanyar gubi ta ga dukkan su sunyi squattn wato duk sun tsuguna babu mai cewa akwai wassu mahaluki a motan bayan ita.
A hankali duhu ya fara shiga ga hanyar duk birji ne ga gargada suka ce mata ta tuka a hankali karta damu suna tare da ita,suna dab da isa taga kowa ya fito da pistol a aljihunsu wato bindiga,a hankali ta iso har kofar bukkan da motar tayi parkn kamar me rada tace musu mun iso na gaban ne yace mata ki cire tsoro ki fita da kudin maza akwai mutanen mu anan fiye da 20 dan haka ki saki ranki nd feel free.
Da addu'a fal bakinta ta yaye labulen assabarin kofar ta shiga dakin taga wayam kamar wani kango sai tabarma ne kadai a yashe a dakin ta ajiye jakar kudin ta fita da sauri ta bude mota ta shiga,a hankali suka ce mata kin dawo toh maza tuka mu tafi gida mun gama da namu aiki sauran aikin yana ga men din mu dake zagaye da nan.
Suna cikin tafia tace musu en suka shammanci men dinku fa,suka ce ba abinda zai faru ma in sha Allahu suna nan har wayewar gari sbd dole mai fakon zuwan ki na jira ki tafi ya fito ya dauka ne...an kusan shigowa gari suka koma normal position wato sun zauna akan seat.
Suna zuwa dai-dai station din suka ce ta ajiye su anan ta musu godia sosai da irin taimakon da suka mata suka ce don't mention hajia we re doing our job,Allah yasa zuwa anjima ko gobe muji feedback mai dadi tace i pray so....suka daga mata hannu itama ta musu asuba ta gari.
Tun a gate baba mai gadi yai mata barka da zuwa ta fada me abinda ake ciki,ta isa falo cike da kadaici da tsoro duk sun addabe ta duk da dama tun sace su mairo ta fara rayuwar kadaicin.
Tana zaune tai dialn number barr.shamsu shiru no ans har ta gaji da kira,zaman shirun ya isheta ta tashi taje daki tai alwala tai sallah ta watsa ruwa ta fito cikin dogon rigar ta wanda zata sha iska dashi,wayarta ta kara dauka ta kira haj.surayya da murna ta dauki wayar tace kaddai kin dawo gida "wlhy kuwa ban jima da dawowa ba na kira mijin ki zan sanar dashi na dawo sannan na bashi lbrn abinda ake ciki amma no ans.
Lah kila yanxu haka wayar shi a silent take sai yasa ay ta kiran shi no ans,meh zai hana ki karaso kawai yau ma mu kwana tare tun da chan din ke kadai ce,toh bari na kimtsa sai na taho.