31

610 49 0
                                    

Lkc daya duk suka zagaye ciki da wajen gidan kuma duk 'yan cikin gidan basu farga da zuwan su ba sbd motocin su a kan hanya suka barsu,kawai gani sukayi mutane sun shigo musu un-expected sun kakkama su dan matasa 4 basu farga da mairo bata gidan ba sai da suka ganta da polisawan.

Ana cikin chaje dakunan ne aka hango su hamda da hamna dake rakube a wani saqon dakin hamna ta kwanta a cinyar hamda ita kuma ta dora kanta bisa kan hamna bacci suke amma sai ajiyan zuciya suke sakewa fuskar su duk shatin hawaye ya bushe,da gudu mairo taje ta rungumo su tana kuka tana cewa rashin sani yafi dare duhu a she duk gida daya muke dasu hamda ban taba sani ba har na gudo na barsu,bude idon da sukayi suka ga mairo tuni suka kara rungumeta sosai kamar tace zata gudu ta sake barin su,tausayin su sosai polisawan sukaji,sukayi Allah wadai da wa'yanda suka sato kananan yaran nan wanda basu da alhakin koman su.

Mutane 5 aka tuso a cikin gidan hannun su duk da handcuff matasa 4 da dattijuwa daya duk aka tusa keyarsu har zuwa bakin titi gun motocin sun,hamda da hamna kuwa gagam suka rike mairo fur suka ki polisawa nan su dauke su a rage musu tafia sbd nisan jejin zuwa titi amma haka suka taka sayyadar su gani suke kamar za'a kara sace su a raba su da mairo.

Sun shiga motoci suka kamo hanya...sun iso sun tadda mutane da suka zo taryan su a headquater police din,haj.batula da kawayen ta haj.surayya da haj.zahra da tazo itama ,kakanin su hamda,har maman mairo da yayar ta ba'a barsu a baya ba,kukan farin ciki haj.batula take sosai ta rungumi yaranta da mairo kowa sai da ya rungume su ana nuna farin ciki da godia wa Allah da ya bayyana su,sannan duk suka dunguma zuwa gida haj.batula.

Zuwa yamma lbr ya zaga gari ay yaran haj.batula santa da akayi kidnappn dinsu an gansu kuma duk ta dalilin 'yar aikin ta ne.
Mutanen da aka kamo kuwa duk an rufe su kafin a zo a fara bincikan su aji su waye suka sa su.

***** ***** *****

Bayan wata 2,haj.batula ce ke zaune a office dinta tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun ta,karfe 1 ya nuna mata tun bayyanar su mairo duk wani aiki dake gaban ta btw 1-2 ajiye shi gefe take taje ta dauki 'ya'yan ta daga mkrnt ta kaisu gida.


Ta isa dolphin ta dauki su hamda sannan ta dauki hanyar prince&princess dan taje ta dauko mairo wanda tun bayyanar su ta nema mata admission,a bakin gate din mkrntr suka tsaya sbd 2 bata gama cika ba bare a tashi su mairo,kafin lkc ya cika take tambayan su hamda karatun su ina dai basa wasa tasan hamna gud gal ce bata wasa da studies dinta wasa sai hamda.

Hamda ta turo baki tace Allah momy ina kokari yanxu a aji kadai arithematic ne yake ban wuya kuma yanxu anty mairo (tun dawowar su suka fara kiran mairo anty lolz) ta daina koya min,ina kuwa zata koya miki itama yanxu da take fama da nata karatun kawai dai ki dage en ba haka ba nasa hamna tana miki waqan olodo rapata momy ta fada tana dariya.

Mairo ta shigo ta zauna a gaban motar suka dau hanya,ta gaishe da momy sannan ta juya wurin su hamda tana tambayan su mai aka musu yau.
A wajen gate momy ta ajiye su tana mai cewa banda fada a su hamda tayi reverse to koma gun aikinta,baba maigadi ya bude musu kofa ya dan zolaye su sannan suka shige,kula da aikin sa yake sosai yanxu sbd yadda yake garkame gate din gudun kar a kuma na baya duk da dai a hanya aka dauke su .

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now