24

578 68 2
                                    

Washegarin ranar barr.shamsu ya isa ofishin acp,office din acp ba bakon barr.shamsu bane sbd abubuwa na hadasu a guri da dama kai tsaye ya shiga office din yana mai miqa ma acp hannu suka gaisa acp ya nuna masa gun zama,bayan ya zauna ne yake cewa acp i 've a task for u,acp yace ina jinka,akan zancen batan yaran haj.batula ce wanda kwanakin baya aka sace su tare da *'yar aikin* ta,ohh any news cewar acp a kagauce a'a nazo ne akan zance mai muhimmanci wanda ya kamata a maida hankali akai.

'Acp yace go ahead',kaga haj.batula na da kanin miji ana kiran shi da ado tun kwanaki yake bin haj.batula da ta mallaka masa takardun gidan da take ciki da sauran dukiyoyin da wansa ya bari,sannan ya fake da lallai gidan da suke ciki shi kani ga marigayi shi ya kamata ya gaji gidan ba ita ba.

Toh,da ya zowa haj.batula da zancen nan shine taje ta sanar da iyayen mijinta akan su san meh ake ciki,toh alhmdlhy surukanta sun kashe zancen kuma duk kafin batan yaran akayi rigimar nan cewar barr.shamsu yanxu haka kuma bayan batan yaran ya kara koma mata akan kudurin sa na farkon nan.

Abinda yasa na dora zargi na akansa kenan cewar bare.shamsu da ya tsagaita da maganar,acp yace ehh toh ba shakka da wannan bayanin naka kowa zai iya zargin sa da sace sun.

Gsky dole da alaman tambaya anan sbd sai da yaran suka bata ya koma mata da zancen gidan,kuma shima zai shigo cikin binciken mu cewar acp,bari na maka wassu 'yan tambayoyi barr.shamsu wane irin sana'a ado yakeyi?gsky bai da wani kwakwaran sana'a duk kame-kame ne dan yadda haj.batula ta mun bayani bashida tsayayyen sana'a yau kaga yana aikin gini gobe kuma zaka ganshi a wani daban.

Toh ya yanayin karatun shi yake?eh toh ta kara da cemin bai yi wani nisa a karatu ba dan tun da ya gama sec yake zaune ba aikin fari bare baqi kuma marigayi wansa babu yadda baiyi dashi akan yaje yai fowardn karatunshi ya bar zaman kashe wando amma shima yaqiya,toh shikenan barr.shamsu zan duba zancen ka kuma zamu je mu fara bincikan sa daga nan barr.shamsu ya tashi yai masa sallama ya tafi.

**** ***** *****

Sati shida kenan wanda yayi dai-dai da wata daya da sati biu da batan su mairo kenan, daga ranan haj.batula ta tilas ta wa kanta fita aiki ko zai rage mara damuwa da zaman kuncin da take fama dashi tun batan su.

Bayan sun tashi a aiki ne ta wuce gidan haj.surayya domin ta huta anan sai zuwa isha ta dawo gida,bayan ta dan huta ne haj.surayya tace dama akwai maganar da nakeso na miki,na me fa?cewar haj.batula,ba komai bane illah zaman ki ke kadai haka ya isa ya kamata ki nemi abokin rayuwa wanda zai maye gurbin tsohon mijin ki kuma ya zame wa su hamda uba,uhum!..surayya kenan banqi ta taki ba amma a zamanin yanxu samun na kwarai mai sonka tsakani da Allah sai an tona,kenan zaki ce mun masu zaryan zuwa gunki duk basu miki ba kuma babu na kwarai a ciki cewar haj.surayya.

Kawai mu bar maganar nan surayya zan iya zama haka har karshen rayuwata ba aure zan zauna na kare mutuncina da darajata,sannan na kare na 'ya'yana na kuma tarbiyartan dasu hanya madaidaiciya.

Duk wannan ba hujja bace da zai sa ki zauna ba aure ,toh yah yanayin alaqar ki take da gwamna?haj surayya ta jefo mata wannan tambayar,haj.batula ta dan murmusa tace har kema kin fara mana kallon masu wani alaqa daban kamar yadda masu tsegumi suke kai?toh ni kam babu wata alaqa irin wanda kika dauka a tsakanani da gwamna face alaqar ta wurin aiki sannan aboki ga mijina kuma sannan ya riqe zumunci.

Here is anoda chapy.... cmmnt nd vote dearies

FIYE DA 'YAR AIKIWhere stories live. Discover now