I've loved you since we were eighteen
Long before we both thought the same thing, to be loved and to be in love._One direction_
^*^*^*
Dakin mummy tashiga ta tarar da ita kishingide akan gado tareda system ko meye takeyi oho da alama ko niyyar tashi sallah batayi ba, tsugunawa tayi tareda gaisheta.
Bata kulata ba saida tagama abunda takeyi a kan system kafun tadago ta kalleta suka hada idanu da sauri sahresh ta saukar danata dan gabanta fadi yake duk sanda ta kalleta.
Tsaki taja tareda cewa "munafuka... Kinyi abu sallah sallah kamar mutuniyar arziki..."ta gyara zamanta tana hararanta itadai batace komaiba bata kuma kalli inda takeba mummy tacigaba "daga yau ki ringa sa alerm dinki karfe hudu idan har ubanki bayanan idan bahaka ba kinsan sauran dan akwai abubuwan dazaki namun, kuma kirinkayi da jiki dan nagani da kiran da makarantarku keyi akan lattinki dan munafurci yamiki katutu kullum sai kin jawo wa mutum magana...yanzu kitashi ki hada kayan wankeni ki kai can gunsu sa'adu, sannan ki tattari inner wears dina ki wanke, ki tambayi raudah abunda takeson ci dan bazataci girkin su talatu ba...sannan ki hada mata books din datake bukata...tashi kiban guri."
"Toh!"kawai ta iya cewa tareda mikewa zata fita taji ance "ke anjima ubanki zai kira saura ki yi munafurcin dakika saba uwarki zanci a gidannan...get out of my side."
Idan dasabo sahresh tasaba idan har abba bayanan abunda yafi haka tana ganin amma daga zarar yadawo soyayya ake nuna mata kamar za'a cinyeta, direct closet tanufa tahau hada kayan wanki wasu an cakudasu da masu tsafta tattarawa tayi ta hada a laundry basket, tareda hada inner wears din ta ajiye gefe dan dawowa ta dauka.
Kwankwasa kofar dakinsu sa'adu tafara dan da alama ma basu tashi ba, lekowa yayi ta spy hole dan tabbatar da waye kafun ya bude kofar yadubeta tareda amsar kayan hannunta yanai mata sannu, gaishesa tayi tareda murmushi harta juya yace "sahresh"juyowa tayi tana dubansa danjin abunda zaice "meya sameki a goshi?" ya tambaya yana kallonta.Taba goshinta tayi tace "ohh! bugewa nayi da kofa!" Kallon tuhuma yake mata alamar bai yadda ba tayi murmushi tace "dagaske nakeyi."
"Kema kinsan ba yadda zanyi ba da bayau farau ba,ki bani dama in gayawa alhaji abunda ke faruwa a gidannan."girgiza kai tayi da sauri tace "aah nipa babu abunda akamun kuma ko kafada abba ba yadda zaiyi ba kuma matsala zaka samu a gidannan."
Tabbas kuwa hakane shi kansa yasan Alhaji ba lallai bane ya yadda saboda kulawan da hajia sakeenah take mata idan yananan,mutum da gidan ubansa amaidashi bawa har agola tafita.
"Kiyi hakuri komai mai wucewa ne kinji."murmushi kurum tamasa kafun ta wuce ya girgiza kai dan kwata kwata sahresh marainiyar Allah bata cancanci hakaba, sunyi zaman mutunci da mahaifiyarta har Allah ya dauki ranta...Allah ya kyauta.
Dakinta tashiga tareda gabatar da sallah asuba tayi addu'o'inta kafun tayi wanka, inner wear din tanufa kana tayi washing room tasa a washing machine, wucewa dakin raudah tayi dakyar ta iya tashinta daga bacci tanata mita... Bata bar dakin ba har saida ta tabbatar tashi wanka tareda alwala ita kuwa tashiga hada mata books dinta sai alokacin take mata wasu assignment din, fried egg kawai tace zataci hakan bai bawa sahresh wahala ba.
Dakin fadeelah ta nufa already ta shiga wanka tattara kayan data kwabe tayi a kasa tadan gyara dakin tafitar mata da unifoam ta ajiye mata komai da jakan.Kitchen tanufa ta soya wa raudah egg tareda dafawa fadeelah indomie dan ita cin indomie constant ne da safe...taje ta ajiye akan dining. Komawa tayi dan juye ruwan zafi a flask daidai ta daga Kettle din taji ance "ubanwa yace ki tabamun book din da kika gani kasan pillow na." Dan tsorita ta saki kettle din zuwan ta zube mata kan hannu sosae taji azaba. Tanufi basin tasa hannun akan running water dan azaba batasan sanda hawaye yazuba ba.
YOU ARE READING
RABO...Inya Rantse!
RomanceTwo girls... One made of innocence and right conduct and the other made of ice and fire For Sahresh Lameedo...Things were a bit complicated ever since her mother's death... She doesn't live the easiest life ever since...she was living in the darknes...