chapter 40

3.4K 292 91
                                    

~There is a beauty in being rejected,Misunderstood,Unseen, and unprotected by people. It teaches you to rely on Allah for everything~

_____

Dakinsa direct ya wuce yanajin zuciyarsa na tafarfasa, abu na karshe da zaiyi a rayuwarsa shine gujewa umarnin mahaifansa, amma wannan karon baijin zai iya hakurta da abunda zuciyarsa takeso... Dukda yana tsananin bukatar addu'arsu, bazai iya bari rayuwar sahresh ta tagayyara ba...Allah yaga niyyarsa kuma shi zai taimakeshi, zai dawo dasu sahresh kamar yadda yayiwa mahaifinta alkawari ko bada taimakon nigerian army ba, he can fight till his last breath saboda ceto Rapunzel dinsa...all daddy care is his reputation, a matsayin da yake zai iyasawa a hade karfi da karfi wajen fighting fayrouz...

Yana cikin hada kayansa cikin gaggawa mama ta shigo dakin da sallama,amsawa yayi ciki ciki, a halin yanzu baison sakejin wasu magaganun da zasu kara dagula masa zuciya... Saidai mahaifiya ta wuce wasa...da ko yaa haaris ne bazai iya basa daman yin magana ba balle kuma kannensa.

Riko hannunsa mama tayi ta zaunar dashi ta zauna a gefensa tana kare wa dan nata kallo... Zata iya rantsewa bata ta6a ganinsa a wannan hkalleta tunda ta haifoshi duniya... Sam shi ba mutum bane mai fushi ko rike abu a rai, da wuya kaga ransa a 6ace...saidai wannan karon an kaisa makura shiyasa akace ka guji 6acin ran mai saukin kai.

"Faaris."ta kirashi cikin kwantar da murya... Bai iya kallonta sai dafe kansa da yayi cikin hannunsa.

"Nasan abunda kakeji a yanzu kuma na fahimci abunda kake niyyan yi...kuma bazan hanaka ba...that girl is in need of your help and I know my son is a brave boy...Allah ya baka ikon kar6ota, my blessings are with you..."

Sai alokacin ya dago yana kallonta da jajayen idanunsa tare da bata side hug yanadan murmushin yak'e yace "nagode mama... Ki tayani baiwa daddy hakuri."

"Daddynka baiyi fushi dakai ba, all he wants is your safety, bayason ka shiga cikin matsala shiyasa yake maka tsanani, saidai wannan karon nima bazanbi bayanshi ba...I'll try to convince him kafun ka iso... Safe flight, Allah ya maka albarka."tafad'a tareda dan pecking goshinsa tare da shafa kansa.

"Ameen mamana..."tareda ita suka karisa  hada duk wasu abubuwa da yake bukata sannan ya dago bindigarsa yana kallo...

Ajiyewa yayi akan gadon tareda khaki dinsa da stars kana ya dubi mama data zuba masa ido yace "su suka bani wannan kuma na ajiye musu, ki fadiwa daddy ban dauki komai nasu ba...addu'arsa kawai nake bukata a yanzu..."yadda ya fadi maganar helplessly yasa jikin mama yayi sanyi

"Insha Allah addu'arsa zai kasance tare dakai, Allah ya tsare ya kuma kareka da kariyarsa."da ameen ya amsa tareda daura black jacket dinsa kan White shirt da black jeans dinsa.

______

Tana zaune kan darduman data idar da sallah,dakin da aka sata ta kurawa ido tana kallo...dakine daya amsa sunansa daki babu abunda babu a ciki saidai ita komai baki ya dawo mata...a kurki yafi mata inda take ciki yanzu...

Alkawari ta daukar wa kanta bazata sake kuka ba,bazata kara zubar da hawayenta kan abunda fayrouz yayi mata ba... He's taking advantage of her weakness, tayi imani Allah yana jin kukanta kuma shi zai kawo mata sauki ya kubutar da ita daga hannun wannan azzalumin da a yanzu she's legally his wife...agogon hannunta ta kalla tanajin zuciyarta na kuna, runtsa ido tayi tana tunanin faaris...Ko yasan halin da take ciki yanzu....ko abbanta yasani,tana cikin wannan tunanin taji karan bude kofa..  Da sauri ta daga kanta tana kallo... Wata matace da a kalla zatakai shekaru arba'in ta shigo tana sanye da bakar duguwar riga mai fadi da karamar hijabi akanta...

Kallo daya sahresh ta mata ta dauke kai tare da daura kanta kan kafafuwanta data nade ta dunkule gu daya akan darduman da take a kasa.

Cikin larabci ta fara mata magana tana gaisheta da fara'a saidai ko kallo bata ishe sahresh ba bare ta samu amsa ba... Zama tayi gaban sahresh din tareda ce mata "ni sunana khadija,duk da ban sanki ba nasan fin karfi aka miki aka kawoki nan..."

RABO...Inya Rantse!Where stories live. Discover now