chapter 18

3.7K 317 104
                                    

We were just kids when we fell in love, not know then what It was, I'll not give you hope this time.

~Ed~

______

Bayan kwana biyu.

Damuwa ta taro tayi wa sahresh yawa, gaba daya batajin dadin rayuwarta dukda Lailah na iya bakin kokarinta na kwantar mata da hankali tareda d'ebe mata kewa, asibiti ma tadaina zuwa, habaici kala kala babu wanda bataji daga gun mummy sakeenah da fareedah, mummy nafeesa tace ta dawo gunsu amma taki, tun ranar da abun ya faru  bata sake jin duriyar abbanta ba...gaba daya yama daina zama ya committing kanshi wa asibiti da company...gaba daya duniyar ta mata wani iri...duk lokacin da sukayi waya da aunty madeena nunawa takeyi kamar she's happy saboda batason wata matsala ta shiga tsakaninta da abbanta.

Tambayar ta guda da haryau ta kasa samun amsa shine meyasa captain ya za6i wannar hanyar ya tozarta ta, dan kawai ta amince zata aureshi? Tayi regretting kin amincewa da bukatarsa lokacin da yazo mata da farko...yanzu ya mata tabon da har ta mutu bazata manta dashi ba, yanzu duniya sun san sharrin da aka mata, kowa da yadda zaina kallonta,da wanda suka yarda da wanda basu yarda ba...tsoron fita takeyi saboda tana tunanin duk inda tayi za'ana nunata gashi abbanta sannannen mutum ne...dukda yayi iya k'ok'arinsa wajen ganin an deleting videon daga social media gaba daya...Faaris ya gama da rayuwarta kuma har abada bazata ta6a yafe masa ba...yanzu tasan babu mai kallonta da mutunci ballantana yayi sha'awar aurenta...sunanta ya gama 6aci a duniya, bata ta6a jin ta tsani mutum a duniya ba irin yadda ta tsani faaris...she has a wrong impression of him at first and think of him as a good man...he always seems to be happy and perky  saboda ya drawing attention na mutane su dauka he's a good man...but basusan asalin halinsa ba behind his facade... Maciji ne mai saran mutum ta kasa.

Kallon agogon beast tayi rike a hannunta tana hawaye, how he wish da beast na tareda ita yanzu tasan duk zai providing solution to all of her problems, he will stood by her and make sure no any harm can come to her way...he's so full of life and laughter, ina ma da zata ganshi a wannan lokacin saidai babu hali, tasan yanzu ya manta da ita.

Amina ce ta shigo ta sanar da ita abbanta na kira, gabanta ne ya fad'i lokaci guda, tunda abun nan yafaru ko sau daya bai ta6a nemanta ba kuma duk sanda taje gunsa baya nan...she just wish abbanta yayi trusting dinta, she just have to prove her innocence.

Da sallama ta shiga parlor'n ya amsa mata a tsanake...zama tayi a kasan kujeran da yake tareda gaisheshi ya amsa a tsanake...bayan nan shiru ya biyo baya.

"Abba kayi hakuri da abunda ya faru,nasa kazama abun magana agurin mutane duk inda kaje ana nunaka saboda ni...I know you're highly disappointed in me ka gafarceni... But believe me abba wallahi bani da masaniya akan abunda ya faru, ba hali na bane wannan."ta karisa tana hawaye.

"Sahresh,"ya kira sunanta ta dago tana kallonsa "ni mahaifinki ne, ni na haifeki, nayi rayuwa tare dake dukda kinzo bakya hannun na amma har a lokacin ina tare dake...nasan komai akanki da hallayarki, nasan tarbiyanki ko sau daya to akan me lokaci guda zanyarda da abunda na gani so daya wannan bani da tabbaci akai...har abada bazan ta6a yadda zaki ci amanar tarbiyan dana miki ba, na yarda dake fiye da yadda na yadda da kaina...I trust you hundred percent, ni ya kamata na baki hakuri saboda na juya miki baya a lokacin da kikafi bukatata saidai inaso kisani nayi hakane saboda da dalili...please forgive me sahr"

"Abba iyaye basu da daman baiwa 'ya'yansu hakuri...because all they did is for their childrens benefit, I've no right to question your actions towards me saboda if I was in your shoe I'll still act as you did..."ta daura kanta akan k'afafuwanshi yana shafa kanta.

"I just want you to turn a blind eyes akan duk abubuwan dake faruwa a gidannan harsai na gano wanda ke da hannu akan wannan lamarin...jawad kuwa kicigaba da sashi a addu'a har Allah ya ku6utar dashi daga halin dayake ciki..."

RABO...Inya Rantse!Where stories live. Discover now