Chapter 2

196 14 0
                                    

Asabe ta harzuka iya wuya, a zuciye tanufi maymunatu da niyyar dukanta tanacewa " 'yar iskar yarinya mara kunya, saina zanemiki jikinki,yanda gobe ko ance kikara bazaki sakeba", don rashin kunya da rashin mutunci har Ni zakiyi tunanin duka?, uwarkima tayi kadan balle ke kuli_kulin kan Tsire" tana binta da nufin kamota zata daka........

Yayinda maymunatu tagudu bayan ummanta taboye, sai a lokacin umman tayi magana dacewa "karki kuskura ki tabamin 'ya bazan kyalekiba, duk da nasan abunda tayi baikamataba, amma kiyi hakuri don bazan lamunci dukaba"..........

Taja kwafa tace " Wallahi nakamaki saina zabeki kuma bari malam yadawo saina kai kararki wajensa", ta wuce fuuu tatafi dakinta ta banko kofa, jikake garammm! kamar zata Balla Kofar......

Umma kuwa jan hannun maymunatu tayi suka shige dakinta, ta zaunar da ita gefen gado, sannan tafara yimata fada dacewa " karki sake shiga fadanmu ni da asabe, ba abunda ya shafeki bane balle har kice zaki daga hannu ki daketa don ta zageni, ba irin tarbiyyan dana baki bane, don na koyamiki girmama nagaba dake, balle asabe datake matar babanku, dole ki girmamata, kome kikaga tayimin babu ruwanki", maymunatu tace " To umma kiyi hakuri bazan sake ba", umma tace " to Allah yamiki albarka", maymunatu ta amsa da "Ameen".........

Shiko salahuddeen daya shiga chanja kaya, kwantawa yayi gefen Katifar sa, don agajiye yake, ga yunwar data dameshi tun kan sudawo, har ciwon kaine yakamashi, dama  baya jure yunwa gaskiya, saiga idonshi yayi ja kuma jijiyoyin kansa sunfito radau, don haka baccin yunwa da gajiya sukayi awon gaba dashi..........!

Umma kuwa komawa kitchen din tayi ta dauko kofi tazo ta hadama maymunatu tea da bread tabata tace ta zauna ta sha, shiko salahuddeen kiran sallan Magriba ne ya tasheshi, sai gashi ya shiga dakin umman, nan tace yaje yayi brush kuma yayo alwala daga nan, sannan yazo ya sha tea din shima kafin yatafi sallan don tasan yana matukar jin yunwa..........
Sai da yasha, sannan yaje yayi sallah yadawo, kasancewar masallacin a kofar gidan yake, sannan tace kowa yaje ya dauko jakan Makaranta ayi bitan karatun da aka koya musu yau, idan da me homework yayi, kafin a kira Sallan Isha, aci abincin dare kuma a kwanta...............

Sai a lokacin abdurrahman kanin Salahuddeen yatashi daga baccin dayakeyi tun bayan la'asar daya kwanta, kasancewar bashi da lafiya yana zazzaɓi, nan umma ta daukeshi taje ta wankemai baki, sannan tazo ta hadamai tea, tana kokarin bashi yana kin sha kuma yana kuka, haka dai ta takuramai yasha kadan, ta shafamai man habbatussauda ta tofemai jiki da Addu'o'i, sannan yasake komawa baccin nasa.............!

Karfe 9:00pm sannan asabe tagama girkin nata, wata taliya tadafa dafaduka da manja, ko kayan miyan arzuki babu, ta tsula manja ko kyan gani a fuska babu, balle mutum yayi sha'awar dandanata a baki, haka dai umman tazuba musu suci ko kadan ne don karsu kwana da yunwa, itama haka dai ta tsakuri abincin kadan don cikin datake dashine kar ta zauna da yunwa itama, amma sunan abincin dai ci karka mutu kawai...........

Bayan sungama cin abincinne, suka karasa homework dinsu, umma tace "kowa yaje ya ajiye jakan Makarantar, ayi fitsari a wanke baki kuma a dauro alwalan kwantawa Bacci", sukace to suka tashi suka nufi makwancinsu....!

Aikuwa Malam Muhammadu nadawowa amarya asabe ta kwashe karya da gaskiya takai karar maymunatu, sai gashi yafito a fusace daga dakin Asaben yana kwalama Maymunatu kira, da sauri tafito daga daki ta sameshi tsaye a falo, tana cewa Abba sannu da zuwa gani, ai batama gama rufe bakiba, Taji...............!

Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now