Chapter 30

17 1 0
                                    

Haka dai maymunatu da salahuddeen suka cigaba da yin hutunsu, inda umma ta raba musu ayyukan gidan don su dinga tayata, maymunatu zata share dakin umma da dakinsu da falo, Shikuma Salahuddeen zai share tsakar gida da kofar gida, sannan saisu hada wanke wanke, maymunatu tayi sabin ruwan kunfa, salahuddeen kuma yayi dauraya, haka idan umma zatayi girki, suna Kitchen tare suna tayata da kananan ayyuka kamar yanka albasa, jajjaga attarugu da bare mafi ko juya miya, da sauran Abunda baza'a rasaba.


Yanzu ayyuka sun ragumma umma tunda yara na hutu suna tayata, amma idan aka koma hutun makaranta aiki nama umman Yawa, shine malam muhammadun yake shawartar umman ko zata nemo 'yar aiki ta dinga tayata, tace to "aiki namata yawa, amma batada ra'ayin daukar 'yar aiki yanzu, zatayi ayyukanta don shine samun ladan mace a gidan aurenta, kuma ita umma uwar tsabta da kula da abubuwa, bazasu dinga daidaitawa da mai aiki ba, don duk yanda mai aikin zatayi mata bazata mata daidai yanda takeso ba, abubuwa dayawa tafiso tayi da kanta, idan wani yamata sai ta sake don bata natsuwa saboda tsabar tsabtar ta, don haka bataki badai ta dinga kai rainon Sadeeq kusa da gidan mai Anguwa ba, gidan maman A'isha mai reno, sai ta goya fadimatu tayi aikinta, zata samu enough time tayi dukkan ayyukan nata, idan ta kammala har da girki sai taje ta dauko Sadeeq din daga gidan raino, malam muhammadun ya amince da shawaranta, aikuwa aka fara kai Sadeeq gidan raino, idan malam muhammadun ya shirya zai tafi shago da safe, sai umma ta shirya Sadeeq din da kayansa kala 1 da abincin da zai ci, sai ta kaishi ta dawo gida, malam muhammadun kuma ya wuce, idan tagama ayyukanta wajen Azahar karfe 2:00pm sai taje ta dauko shi, dama karfe 10:00pm take kaishi, awa hudu kawai yakeyi gidan rainon


Bayan kwana 2 umma tace Suzo su kaishi gidan rainon, kasancewar gidan acikin unguwar yake kuma babu nisa, domin baifi gida 5 bane a tsakani, dama gidan kusa da bakin titi yake, dama su Anas da haka yaran maman anas dake flat na 2 sun shigo wajen su maymunatu, nan sukace zasu rakasu cikin anguwar don kai Sadeeq din, haka kuwa akayi, suka tafi kaishi su 4, wato salahuddeen da maymunatu da anas da hanifah, suna tafe suna firan makaranta, dama makarantar bokonsu daya, suka kaishi suka dawo, su ansa suka koma flat dinsu, maymunatu Kuma suka shiga kitchen don taya umma girki, haka rayuwar yaran ta kasance a gida cikin hutun gwanin ban sha'awa, Shiko Sadeeq watarana ma ba'a kai shi gidan Rainon saboda su maymunatu na nan kuma zasu taya umman aiki.


Yaran unguwa kuwa sukan hadu da yamma a waje suyi wasansu, kasancewa anyi hutun boko da islamiyya duka, maymunatu mai farinjini har cikin yara sa'o'inta, kowa nason yin wasa tare da ita, shigo salahuddeen bayi da hayaniya sosai, domin idan baimaga dama ba, bayama wasa cikin Mazan, yakan koma gefe ya zauna yana kallonsu kawai.


Hutu ya kare har an koma boko da islamiyya, nan yara suka koma daukan karatu ka'in dana'in, an dukufa neman ilimi, domin ilimi shine gishirin zaman duniya, don haka yaran kowa yabada himma karatu suke bil haqqi da gaskiyansu


Bangaren hamshaqiya amarya asabe kuwa, har yanzu bata gama girki da wuri sai jefi jefi, domin bata dawowa da wuri daga makarantar Imamu, don haka to koma yin girki kala daya, magana idan tayi na rana to shine har dare, saboda ba'a gama cinye na ranaba balle har ayi na dare, karfi da yaji haka takoma yin girki tazarce, daga na rana sai na safe, yayinda umma ke girki sau 3, Safe, rana, da dare.


Innalillahi wa'inna Ilaihi raju'un................!


Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

Taku Har Kullum
Admin Maymunatu
Garkuwar Mata
Marubuciyar Al'umma

Ana Mugun Together
🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝🤝

Love You All My Fans
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now