Da shekara ta zagayo salahuddeen yagama nursery 3, shima aka sashi a staff school primary 1, kta kuwa maymunatu tana primary 2 lokacin, kuma tunda tashiga term 3 duk 1st position takeyi,...to ko ya Salahuddeen da maymunatu zasu karke a makarantar ?............
Su kuwa Adamu da Ayuba suna makarantar Higher Islamic & Arabic Education, Adamu na JSS 3, Ayuba Na JSS 2...........
Kuma A Lokacin Ne Malam Muhammadu Yace Itama Umma Yakamata Yasata makaranta amma ta Addini, don zama haka ba dadi, koba komai cigaba da neman ilimin Addini yanada muhimmanci.....
( Da wannan nakeso najawo hankalin matan aure don Allah adaure a koma makarantar Islamiyya neman ilimi, kada mace tace don tayi Aure Shikenan ita tayi sauka tadena zuwa karatu, kisani lokacin dakikayi Aurene ma yafi miki muhimmanci da Albarka dama lada daki dage wajen kara neman ilimin Addini don inganta zamantakewar Aurenki da mijinki, dama Tarbiyyan 'ya'yanki, don haka Matan Aure Akoma Makaranta Please.......!)
Don haka akwai wata makarantar Addini ta matan Aure, Kuma Arabic da boko ne, sunanta (Abdurrahman Mora College), ana kiranta da Imamu, nan Abban yaran yayimata registration da Uniform da kayan karatu, Takuwa Fara Zuwa tana neman ilimin Addini da na boko, Duk da tayi Secondary School sannan tayi Aure, kuma ilimin Addini tanadashi daidai gwargwado don tasamu tarbiyya mai kyau..........!
Kasancewar Umma ma'abociyar cin masara dafaffiya, gyada ko gujjiya yasa suka saba da Asabe mai kabeji, tana kawomata talla har gida itada kannanta tana siya, kasancewar tasan tana cinikin yasa tanace da zuwa don tasan bata zuwan banza, don koba chanji zata bata ta tafi gobe idan tazo su daura lissafi, yau da gobe har suka fara gaisawa da malam Muhammadun, tunda wataran yana gidan suke zuwa, har ma Wataran idan tazo umman bata nan yakan siya ya ajiyemata kafin tadawo...........!
Malam muhammad dayaga harkan sana'ar sa ta bude, Allah yasa Albarka, sai ya fara neman hayan shago a jerin rukunin shagunan cikin campus din unimaid din, inda kuwa yayi sa'a aka bashi kasancewar shi sanannen ma'aikace a wajen, nan yabiya kudin hayar aka bashi receipt, nan yasa yara suka sharemai ko'ina harda sharan yana, yasa aka gyara abubuwan dasuke da bukatar gyara, akayi penti, aka rubutamai sunan shagonsa,( GIDAN ZUMA NATURAL HONEY AND MEDICINE STORE )..
Washegari daukan Izini yayi na tafiyar kwana 1 daga wajen Aiki zuwa garin kano, aka bashi izini, nan ya shirya yama umma da yara sallama yadau hanyar kano zuwa siyo kayan islamic Chemist dazai zuba a shagon tare da zuman......
Isarshi kanon keda wuya ya wuce cikin kasuwar ta kurmi tsohuwar kasuwa mai dumbin tarihi, kuma babu abunda bazaka samuba a cikinta, kasuwace mai fadi da cikar jama'a, nan ya zaga shagunan yayi siyayyar kayan man zaitun, man habbatussauda, zamzam, garin magarya, garin bagaruwa, tafarnuwa da sauran kayan magungunan Musulunci, aka hadamai kayansa aka daure, yakama hanya sai unguwar 'yankaba gidan mahaifiyarsa, nan ya isa yamma liqis yakuwa tarar tadawo, nan ya zauna suka gaisa bayan ya shigar da kayan daki, Mahaifiyarsa Gogal ta zubomai abinci da ruwan sha takawo, ya amsa yayi godiya, nan ya zauna yanaci suna hira har yagama, ana kiran Sallan Magriba yace zaiyi alwala yaje sallah daganan Zaije gidan yarsa sa'ade sugaisa, da gidan su saude da gidan Kawu mai wanki duk a gaisa, tunda da safe sammako zaiyi ya koma Maidugurin..............!
Sai karfe 10:00pm malam muhammadu yadawo daga ziyaran nashi, inda Yayi sallama Gogal ta amsa sannan yashiga, nan ya tadda ita zaune tsakar gida bisa tabarma ta kishingida tanajin shirin Taskar Labarai a gidan radion kano 2 Am uwa mabada mama, nan yamata sannu da gida ta amsa tana tambayarshi ko ta zubomai tuwan dare,? yace "a'a yaci kadan kidan yarsa sa'ade", yace bacci dai yakeji don haka zai kwanta tunda gobe sammako zaiyi ya dau hanya, tace "to Allah yakaimu"...yace "Ameen",nan yamata Saida safe yashiga daki yayi shirin kwantawa.......
Washegari kuwa da sassafe Mahaifiyar sa gogal ta hadamai abincin kari yaci, yamusu sallama sai tashar 'yankaba inda yahau motar maiduguri aka sa kayansa a boat din motar, mota na cika aka dau hanya sai Maidugurin...............!
Suna isa garin ya dau shatan mashin da kayan nasa sai cikin Campus din na unimaid, bai dira ko'inaba sai gidansa, inda bayan ya sauka yabiya mai mashin kudinsa, Sannan ya dau kayan yashiga gidan da sallamarsa.....
A falo ya tarar da iyalan nasa, inda umma ke rike da Abdurrahman yana ta bacci kwance a kafarta, hannunta rike da charbi tana Salatin Annabi da azkar, maymunatu da salahuddeen kuma sunatayin home work dinsu, sanan karatun Alqur'ani ke tashi cikin kira'ar Sheikh Abdulbasit Abdussamad, inda yake karanta suratul Yaseen da tangimi, karatun Kur'ani ya Karade gidan don tundaga tsakar gidan yafara jiyo karatun daya shigo, nan zuciyarsa tacika da farincikin ganin iyalan nasa cikin walwala da kwanciyar hankali ga kuma karatun Alkur'ani mai tsarki yana tashi, kai madalla da wannan iyalan masu riko da Addini..................
( Anan nake jan hankalin 'yanuwa musulmai baki daya, musamman iyaye mata da iyaye maza, saka karatun Alkur'ani cikin gida yana kore shaidanun mutum da aljan, sihiri kowane irine, kuma mala'ikun rahama zasu sauka a gidan suna nema iyalan gidan rahama da gafarar ubangiji, sannan maganine kuma warakane na dukkan rashin lafiya, yana yaye talauci yakara wadata a gidan, don haka a daure a dinga kunna karatun Alkur'ani acikin gida, kuma haka da daddare a yawaita saka suratul Bakara tanada matukar amfani domin tsarice da kariya daka dukkan wani abun ki kona cutarwa....
Haka matasanmu maza da mata mukasance muna loda karatun Alkur'ani cikin wayoyinmu kuma mu kunnasu muna Saurare akoda yaushe koda muna aikine..................)Nan suka taso suka tarbi malam muhammadun, suka gaisheshi sukamai sannu da zuwa, ya amsa da fara'a, nan umma tace "abban yara bari na hadama ruwan wanka kayi, sai ka zauna cin abinci", yace "to nagode Allah yayi albarka",..........
Kwantar da abdurrahman tayi bayan ta tofeshi da Addu'o'i, tanufi daki tawuce toilet ta hada ruwan wankan, saiga malam muhammadun yashiga dakin yayi shirin wankan ya nufi toilet, umma kuma tace a fito lafiya, nan ta fito mai da kayan dazaisa, ta feshesu da turare, ta ɗora bisa gado, sannan tafita ta nufi kitchen don hadomai kayan abincin,...
Washegari malam muhammadu da wuri yatafi shagonsa, don yau aikin jera kaya zasuyi, nan ya kwashi kayan daya siyo yatafi, dama ya gayyato yaran dazasu tayashi aiki, nan suka kara share ciki da wajen shagon, suka fara jera kayan cikin locker, kowanne aka saka shi inda yakamata, bayan wani lokaci suka gama shirya kayan, saiga shago yafito rass, malam muhammadun yasa akayimai sign board mai dauke da suna da address din shagon.........
Aikuwa aka fara zuwa shagon siyan zuma don malam muhammadun yafadama mutanensa yabude shago, idan anzo siyan zuma sai aga sauran kayan da suke shagon sai kaga an siya, ciniki ya mika ana samun Customers sosai...
Kasancewar malam muhammadun ya iya kiwon zuma wanda ya koya a misra lokacin dayaje karo karatu, don haka ya yanke shawaran maimakon siyo zuman dayakeyi cikin kauyuka mai ze Hana yafara kiwon zuman dakansa?
Karfe 9:00pm malam muhammadun ya koma gida bayan tashin shi daga shagon sana'arsa, bayan yayi wanka yaci abinci,suka zauna suna dan hira da umma, nan yake mata bayanin abunda yakeso yayi, nan tayi murna kuma tanuna goyon bayanta, Sannan tayi addu'a da fatan alkhairinta akan lamarin.............
Nan malam muhammadun ya rubuta takardar neman izinin fara..........................???
Taku Har Kullum
Maymunatu AbubakarDon't 4get 2 Vote, Share & Comments 🤝🤝🤝
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..