Malam muhammadu ya nemi izinin hukumar makarantar unimaid kan abashi aron wani fili wanda yake cikin campus din, yanaso ya fara yin kiwon zuma ne dakansa, filin yana daga chan ciki karshe karshen katangar makaranta, wajen kaman dajine, don ba gidaje sai daidaiku, ga dogayen bishiyoyi da fulawowi kala kala, akwai yar karamar korama ruwa yana gudana aciki, tabbas wajen Zaiyi kyau da kiwon zuma, shine malam muhammadun yanemi izini abashi aron wajen, to kasancewar ansanshi, hakan tasa hukumar makarantar ta amincemai tabashi aron zuwa wani lokaci idan har ta bukaci wajanta zai bata, kuma ya amince akayi yarjejeniya aka rubuta harda shedu a takarda...........
Haka yasa capenter yahadamai akwatuna na katako masu murfi yanda za'a iya rufewa a bude, dogaye masu fadi, daga kasa jikin akwatin anyi yar kofa, daga sama kuma ajikin akwatin anyi hannun dauka dama da hagu, Sannan anyi musu Wajan sagalewa a jikin bishiya, an sagalesu Chan saman bishiyan akan reshe mai Gwari anyi dabara an daure yanda bazai fadoba koda anyi iska, wasu kuma anyi dogayen tebura masu Tsaho sosai an daura wasu akwatunan a kai,........
Sannan yasa tailor ya dinkamai Uniform din akin Zuman, overoll ce babba fara an dinkata da yadin pure cotton Mai Kauri Yanda ko zuma bazata cijekaba idan tahau jikin kayan, sanan an samu hular malafa an dinka net ajiki an Zagaye gaba daya,Sai wajen zugewa idan mutum yasa, saboda koda zuman ta hau jiki bazata tabo fuskanta ba balle ta harbeka......
Sai takalmi rainbooth irin na masu shiga gona da damuna, da Safan Hannu Mai Kwari wanda mutum Zaisa idan zaiyi Aiki.....
Sai kuma ya tanadi bokitai masu murfi wanda zai dinga zuba sakar zuman idan ya kwashe, da Robobin Aiki Manya.....
Sai yasa masu kira suka keramai dan karamin abun hura iska wanda zaka zuba garwashi kasa karmami yanda zaka samu hayaki, wanda zai dinga koran zuman idan yaje aikin diban sakar zuman, saboda zuma Sai Da Hayaki idan kanaso Sutafi kayi aiki a natse.....
Sannan Yasa Aka hadamai engine dazai dinga tace zuma, acire tukar zuman daban, ruwan zuman daban,.engine kamar na markade akayishi, sama a bude akayishi wajen zubawa, daga chan kasa kuma dan kofa akayi kamar girman bakin kofi, inda ruwan zuman zai dinga fita, sai a tara bokiti daga kasan ko jarka yazuba a ciki,...
Amma akwai abun tata shima dayasa aka siyomai a kasuwa irin abun tatan koko na mata, sai a sa abun tatan cikin engine a bude bakin, sai a zuba sakar zuman a daure bakin, sai a rufe da murfin engine Wanda zai shiga ciki ya danne zuman da aka zuba a abun tatan, hakan zai bada damar a tace ruwan zuman tass daga jikin tukar, idan tagama tsanewa sai a juye tukar sa sake zuba wata, haka za'ayi tayi har agama tacewar.......
Haka kuwa akayi, bayan malam muhammadun yagama hada dukkan kayan aikin kiwon zuman sa, sai yafara,komai aka ajiyeshi inda Yakamata, Sannan yatafi, kiwon zuma na daukan lokaci kafin ta taru dayawa don haka yatafi yacigaba da sana'arsa yabata tsahon lokaci kafin yakuma waiwaiyanta lokacin dayakesa ran zai samu amfani mai yawa...........
Filin da malam muhammadun yake kiwon,kusa da gidan wata **Aljanace** mai dadadden tarihi, wacce ake cemata **Aljanan Campus**, tarihi ya nuna cewa tayi shekara aru aru masu yawa, kuma da tana cinye mutane, kuma ba'a ganinta sai shekara shekara take fitowa daga cikin gidan nata, kuma babu gida kusa da ita, daga baya dai tadena cin mutane, kuma har aka samu mutane na iya zuwa wajen, har dai masu ƙarfin hali suka fara zama a wajen bayan hukumar makarantar ta gina wasu gidaje a kusa da gidan aljanar Campus din, Wannan kenan........
Haka dai sana'ar malam muhammadun ta bunkasa, kuma yafara bada magungunan Musulunci kasancewar yanada karatun Dibbun Nabawiy, kuma yanada sani anan bangaren don In baku mantaba abaya nafada muku yaje Misra shekara 4 karatu, to achan ya koyo harkan kiwon zuma da bada magungunan Musulunci, to shine yanzu ya bunkasa sana'ar hakan, kuma kasancewarshi malami masanin Addini sosai har Rukiyya yakeyi yana cire Aljanu, kunga Don yaje kusa da gidan Aljanar Campus bazata iya cutar dashi ba, tunda yasan maganinta............
Bayan watanni malam muhammadun yakoma don duba kiwon zuman sa, aikuwa abun sai san barka don kuwa yasamu amfani mai yawa da albarka, nan yakoma shago yacigaba da cinikinsa, sai yamma bayan sallan la'asar ya dau kayan aikin kiwon zuman sa ya nufi wajen shida Yaransa su 2 masu tayashi aiki a shago, sukayi aikin kwaso sakin zuman cikin Sa'a da nasara, suka kammala suka kwasa sauka kai gida, kasancewar a gida yake aikin tace zuman, kuma Ummace manager aiki idan bayanan,ko su Adamu da Ayuba su tayaya ko suyi su kadai idan tana aiki a lokacin.....
Kasancewar ubangiji yasama siyarda zuman albarka, ana siya kuma tana saurin karewa, hakan yasa bai dena zuwa siyo zuman dayakeyi ba cikin kauyuka, saboda kafin nasa zuman dayake kiwo ta taru ya kwaso ta shagon ta kare kuma ana siya dayawa, don tafi komai tafiya cikin kayan shagon..............
Malam muhammad kuwa ganin sana'arsa ta bunkasa Allah yasamai Albarka, ai sai ya rubuta takardar ajiye aikinsa, dama shi tun farko yafi sha'awan rike sana'a baya son Aikin Gwamnati, dama da farko yafara aikin gwamnati ne kafin yasamu sana'ar yi, daya samu sana'ar kuwa sai ya ajiye aiki ya riƙe sana'arsa kawai ta ishe shi ya riƙe iyalansa.......
Asabe mai kabeji kuwa dama tana kaima masu shaguna suna siyan dafaffiyar masara, don haka ganin an bude sabon shago an tare sai sukace bari su kai talla ko za'a siya?, Aikuwa sai da suka shiga sai sukaga ashe mijin Maman salahuddeen ne mai shagon, nan asabe da Kannanta Sukace "lah! ashe malam ne mai shagon" nan suka gaisa Sukace sun kawo tallan masarane da gyada, yace to shi bayaci amma bari ya siyanma yaran shagonshi, nan yace ana kowa ɗaya afadamai nawa yakama ya basu kudin, nan suka basu su 6 kuma #20 ce ko wace masara, don haka Yabasu #120, suka amsa sukayi godiya suka tafi....
Akwai wata mata bafulatanace mai suna Ayye mai fura, dama yawancin ma'aikatan cikin unimaid campus Din sun Santa suna siyan fura da nono ,don har Office take kai musu suna siya, nan ma dataga an tare a sabon shagon, sai tafara kaiwa,aikuwa taga ashe malam muhammadune dama sun saba, nan take tambayarsa malam kadawo nan ne? yacemata "eh", tace aikuwa zan dinga kawowa tunda Nasan zaka siya", yace "eh kirinka kawowa", nan ya siya na ranar yabiya tatafi tanamai tayashi murnan bude shagon dayayi....!
Yau da gobe tafi ƙarfin wasa, sai gamutunci ya kullu tsakanin malam muhammadun da asabe mai kabeji, har takai Kannanta ma dasuke zuwa tare sun saba da malam muhammadun suna gaisheshi fiyeda da, kuma kullum sai yayi musu ciniki, wasa wasa har labarin malam muhammadun da cinikin da yake musu yakai gidan su asaben kowa yasan labarin malam muhammadu mai shagon zuma.........
Abu kamar wasa sai asabe ta fara nuna tana ra'ayin malam muhammadun, tun yana ganin abun kamar wasa ko Kuruciya, har takai yafara yarda da gaske takeyi, ko tallan suka kawo yasiya sai tamai ragi ko tace yabar kudin, wataran yabarshi, wataran kuma Yace dole saita amsa ko yaba Kannanta, sai yace " idan bai karamata kudiba, ai baya karya Jarin ba",...
Dataga tafara samun shiga, nan fa tafara kawomai damammiyar fura mai sanyi a kwarya da ludayinta, kasancewar taga shi ma'abocin shan furane, tunda tana ganin Ayye mai fura tana kawowa yana siya, haka zai amsa yayi godiya amma baya sha, idan ta tafi sai yaba yaran shagonsa su sha don baigama yarda ya saki jiki da itaba,........
Sai kuma takoma kawomai kunu a kwanan sha da zafinsa, don taga wataran yana zuwa da flask din kununsa Idan yataho da kayan abincinsa daga gida, nan ta fahimci yana Son kunun kenan, shine tafara kawomai daga gidansu da zafinsa,....
Turkashi, yau da gobe bata bar komai ba, don yanzu tafiya tai tafiya, malam muhammadun yafara sabawa da Asabe da hidimarta, har yafara shan abubuwan datake kawo masa yana amsa da godiya, har ranar da ba'a kawona sai yaji badadi, sabo da shakuwa mai karfi tashiga tsakanin malam muhammadun da Asabe, hakama tsakanin malam muhammadun da iyayen asabe da 'yan gidansu sun saba ansan juna ana gaisawa, don 'yan gidansu sunfara zuwa siyan zuma ko magani a shagon, dama akwai wata yar uwar asaben datake fama da matsalan Aljanu, don haka Asabe tafadama iyayenta aka kaita shagon malam muhammadun yamata rukiyya, kuma tasamu lafiya, don haka zumunci yakuma kulluwa tsakaninsa da yan uwanta...........
Turkashi......Ana wata ga wata....Ina umma baiwar Allah???....Shin tasan kalan wainar da ake Toyawa kuwa ?????.......To ku biyoni a update dina Na gaba, don jin yanda zata kaya......................!
Taku Har Kullum
Maymunatu Abubakar
Ana Tare My Fans....!
🤝🤝🤝🤝🤝🤝Don't 4get 2 Vote, Share & Comments 👏👏👏
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
Narrativa generaleThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..