chapter 3

56 8 0
                                    

Kafinma ta rufe baki taji Saukan Mari da duka tako'ina, sai kuka Maymunatu takeyi tana kiran ummanta, tanacewa "umma kizo ki ceceni", "abba dan Allah kayi hakuri", saida ya Jibgi abarsa Son ransa, yagaji ya kyaleta, sai a sannan umma ta taimakawa maymunatu ta tashi, don ko da tazo cetonta tana ba abban hakuri cewa yayi " idan baki matsaba Saina hada dake", don haka ta tsaya gefe, nan tana Maymunatu dakinta ta zaunar da ita tana mai sake yimata fada da Nasihar Karta sake shiga fadansu da asabe don ba huruminta bane, kada abbanta Yasake dukanta irin haka, Maymunatu dai gada Kai kawai tayi tana ajiyar zuciya, don ta samu iya dakuwa kasancewar abbansu bai iya fushi Ba idan yakama mutum sai ya kusa ballashi.

Karfe 4:00am na asuba umma ta farka yanda ta saba donyin Qiyamul Laili a karshen dare, ta dauro alwala ta tada Sallah, tayi Addu'o'i sannan ta roki Ubangiji biyan bukatunta da yayewar matsalolinta, tana nan kan daddumar aka kira Sallan Asuba, taje ta tada yara don yin sallan asuba, tadawo ta tada Raka'atanul Fajri,tayi Sallan Asuba tasakeyin Addu'o'i da Azkar din Safiya na cikin littafin hisnul muslim da 40 Rabbana.

Maymunatu ma ta dauro alwala, tayi Raka'atanul Fajri, tayi Sallan Asuba, sannan tayi Azkar Da Addu'o'i kamar yanda tasaba, shi kuwa Salahuddeen yayo alwala yajira Abba yafito, Abban yafito suka tafi masjid.

Bayan sun dawo ne Abba yanemi waje ya zauna da charbinsa a hannu yana lazimi, Salahuddeen ya dauko Al'kur'aninsa yafito falo, itama maymunatu dauko nata tayi suka zauna yin karatun Alkur'ani na Asuba kamar yanda Abban nasu ya sabar musu kullum, zuwa karfe 6:00am sukayi addu'a suka tashi don yin shirin makarantar boko.

Bayan sun gama Karatunne suka gaida Abbansu cikin girmamawa ya amsa, sai a sannan yakema Maymunatu fada dacewa " karki sakeyin abunda kikayi Jiya, dole ki girmama Asabe itama mahaifiyarki ce, babu raini a tsakaninku" tace "to", sannan yace a dauko zuma da cokali kowa yasha kafin ya tashi, suka sha suka tashi don shiryawa.

Mahaifin su maymunatu yamaida shan zumar al'ada ne kullum bayan Idar da karatun, saboda zuma maganin dukkan cututtukane inji "Annabi S.A.W" zuma na bude kwakwalwa musamman ta yara, tana ƙara lafiya, tana ƙara hazaka da basira, fahimta da kaifin tunani ga yara, sannan tanasa yaro yazama mai kokari akan ilimin da nemansa, musamman karatun Alkur'ani.

Ita kuwa umma dataji sun Idar da karatun, saita fito falon tana gaida Abban yaran, sannan ta wuce don taimakawa su maymunatu da salahuddeen shirin school, sannan tayi aikace aikacenta, yanda tasaba tunda ba ita bace da girki ranar.

Abangaren amarya asabe kuwa........

Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

Written & Published By
Maymunatu Abubakar

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now