Bayan Wata Uku Da Komawarsu Sabon Gidan Hayan Nasu,Wata Yammar Ranar Asabar Saiga Sa'ade 'Yar Malam Muhammadu Tazo Daga Yankaban Garin Na Kano, Itada 'Yarta Rakiya, Malam Muhammadu Ne Yamusu Kwatance, Da'aka Kawosu Gate Din Unimaid Din, Sai Yaje Ya Tarosu Suka Tafi Gidan, Nan Suka Shiga Suna Rada Sallama A Tsakar Gidan, Nan Umma Ta Fito Tana Cewa "Wa'alaikumus Salam, Lalle Maraba, Sannunku, Kushigo",Nan Suka Shiga Tamusu Masauki A Falon, Nan Suka Zube Kasan Carpet Suna Maida Numfashin Dogon Tafiyan Dasuka Kwasa, Nan Ta Zauna Itama Suna Gaisawa, Tuni Maymunatu Da Salahuddeen Sun Tafi Kitchen Zubo Musu Ruwa Da kofuna, Sai Sallamansu Sukaji A Falon, Suna Shigowa Hannun Maymunatu Dauke Da Jug Din Ruwan Sanyi, Shikuma Salahuddeen Yana Rike Da Flate Wanda Ya Dauro Cups Guda 2, Suka Ajiye A Gabansu, Kuma Suka Gaishesu Sannan Suka Kuma ma Dakin Ummansu, Saboda Tahanasu Idan Anyi Baki Su zauna A Falon.....
Malam Muhammadun Shima Gaisawa Sukayi, Yamusu Sannu Da Hanya, Sannan Ya Shige Nashi Dakin, Itako Umma Kitchen Tatafi Don Ta Hado Musu Kayan Abinci.......
Bayan Takawo Musu Abinci Ne Tace "To Suci Abincin Idan Suka Gama Sai Sumata Magana Ta Nuna Musu Inda Zasuyi Wanka Suyi Alwala, Bari Taje Taba Abdurrahman Nono Ya Sha Taji Ya Tashi Kafin Yafara Kuka", Sukace "To, Ba Damuwa",.. Nan Tatafi Ɗakinta Wajen Yaran.......
Kiraye Kirayen Sallan Magriba Akeyi, Nan Umma Tafito Falo Inda Ta Tarar Dasu Har Sungama Cin Abincin, Suna Dan Hutawa, Nan Tamusu Jagora Zuwa Dakin Dazata Musu Masauki Su Kwana, Sukayi Sallama Suka Shiga Suka Ajiye Kayansu, Nan Ta Nuna Musu Toilet Din Dake Cikin Dakin, Ta Shinfida Musu Daddumar Sallah Saitin Gabas Don Suga Alkibla, Ta Musu Sallama Tafiya, Yayinda Gwaggwo Sa'a Tashiga Don Tafarayin Alwalan, Kafin 'Yarta Rakiya Tashiga Itama.......
Umma Ma Komawa Tayi Ta Tarar Har Su Maymunatu Sunyi Alwala Suna Shirin Tada Sallah, Itama Ajiye Abdurrahman Tayi Saman Gado Bayan Ta Tofeshi Da Addu'o'i Na Tsari, Ta Kwantar Dashi Ta Hannun Dama, Tashiga Dauro Alwala Itama......Yayinda Shima Malam Muhammadu Yayi Alwalan Ya Nufi Masallaci Tare Da Salahuddeen...............!
Baki Kuwa Sai Da Sukayi Sati Sannan Suka Koma Kano Da Tarin Tsaraba Daga Malam Muhammadu, Dama Sako Na Daban Daza'a Kaima Mahaifiyarsu Gogal...............!
Bayan Shekara Sai Abba Ya Yanke Shawaran Fara Business, Inda Yayi Tunanin Fara Sana'ar Saida Zuma Da Kayan Islamic Chemist, Kasancewar Lokacin Dayayi Karatu A Misra Yakoyo Kiwon Zuma, Amma Kasancewa Bayi Da Enough Plan Dakuma Wadataccen Waje, Sai Yafara Siyo Zuma Jarkan 20liters, Sannan Ya Siyo Robobin Durawa A Kasuwa, Ya Dura Ya Siyar, Karshen Wata Idan Ya Hada Kudin Yasake Siyowa, Haka Dai Yake Ciniki Da Kadan Kadan, Haka Dai Ciniki Ya Kankama..............
Bayan Wata 2 Da Tafiyar Su Sa'ade Da Rakiya, Sai Ga Yaran Sa'ade Maza Su 2, Adamu Da Ayuba, Dama Kafin Su Tafi, 'Yar Tasa Tafadamai Zata Turo Yaran Nata Ya Rikesu Yasasu A Makaranta Tanaso Suyi Karatu Kasancewar Mijinta Ya Rasu Kuma Ita Bazata Iya Daukan Dawainiyarsuba, Don Ba Sana'a Takeyiba, Itama Manyar 'Ya'yanta Ne Suke Yimata Bukatunta, Don Haka Ta Nemi Taimakon Dan Uwan Nata, Kuma Ya Amince Yace Suzo Badamuwa...
Shine Sukazo Yanzu Da Kayansu, Nan Ya Nuna Musu Dakin Dake Kofar Guda Wanda Yake Da Toilet Aciki, Yace Nan Ne Masaukinsu, Suka Shiga Suka Ajiye Kayansu, Sannan Suka Shiga Cikin Gidan Don Gaida Mutanen Gidan, Da Jagorancin Malam Muhammadun, Ya Shigar Dasu Falon Gidan, Umma Tashiga Suka Gaisa, Tamusu Sannu Da Zuwa, Ta Tanbayesu Ya Hanya?, Yasuka Baro Mutanen 'Yankaba?, Sukace Lafiya Qalau,. Nan Ta Tafi Kitchen Hado Musu Abinci, Suka Cigaba Da Gaisawa Da Kanin Mahaifiyar Tasu, Saiga Umman Tafito Da Kayan Abincin, Ta Ajiye Musu, Sannan Tafita Don Basu Damar Su Sake Suci, To Dayake Da Rashin Sabo Malam Muhammadu Yace To Su Dauki Kayan Abincin Sutafi Dakinsu Suci, Nan Suka Kwashe Suka Tafi Masaukin Nasu...
Haka Rayuwa Tacigaba, Zamansu Da Iyalan Gidan Lafiya Qalau, Sannan Bayan Kwana 2 Malam Muhammadu Yasasu A Makaranta Wato Higher Islam, Inda Yasa Adamu A JSS 3 Dayake Shine Babba, Sai Ayuba A JSS 2, Bayan Anmusu Interview Kenan, Nan Malam Muhammadun Yabiya Kudin Komai Suka Fara Zuwa Makarantar, Kuma Idan Sun Dawo Sai Su Taya Malam Muhammadu Wanke Kwalaben Zuba Zuma Kuma Su Dura Sannan Su Wanke, Su Taya Umma Sharan Tsakar Gida Dama Kofar Gida, Haka Rayuwa Tacigaba Da Wakana, Kwanaki Na Shudewa, Watanni Ma Kamar Da Gudu Suke Wucewa.......
Wasa_Wasa Malam Muhammadu Sai Cinikin Zuma Yakeyi, Daya Siyo Nan Da Nan Takare Yakuma Siyowa Tun Ma Kafin Watan Yakare, Kuma Wata Nayi Da'anyi Albashi Kowa Zai Biyasa Kudinsa Chass Babu Ciwon Kai....Suma Su Adamu Da Ayuba Yana Musu Hassafi Da Dan Ihsani, Suma Iyalansa Yana Kyautatamusu Daidai Gwargwado........!
Kwanci Tashi, Kwana Nesa, Rayuwa Na Gudana, Har Maymunatu Ta Shiga Nursery 2, Kai Tun Farkon Shigarta Duk Term First Position Takeyi, Don Haka Duk Ran Hutu Da Prize Dinta Dake Dawowa Gida Tayi Na 1.............
Kuma A Shekaran Ne Shima Akasa Salahuddeen A Nursery 1, Inda Shima Yafara Makaranta A Sa'a Don Shima Term din Farko Na 1 Yayi, Shima Yanata Murna, Don Gaskiya Yaran Nada Matukar Kokari Musamman Ma Maymunatu Yarinya Mai Hazaka, Da Basira, Kuma Batada Tsoro Ko Kadan, Shima Salahuddeen Akwai Kokari Da Basira Sosai Sai Dai Shi Bashi Da Hayaniya Don Ko Fada Maymunatu Ce Take Taremai Harma Ta Rama Mai Idan An Dakeshi A Makarantar, Ita Kuwa Bata Tabuwa Gun Kowa, Don Akwai Tsiwa, bakinta Kadai Ya ishe Mutum, Don Haka Ma Dalibai Ke Shakkanta, Bamai Tabota, Harma Sauran Ɗalibai Kawo Mata Kara Sukeyi Idan An Daki Wani, Kuma Saita MusuHukunci Daidai, Don Saita Ramawa Wanda Aka Zalunta, Shiyasa Daliban Makarantar LAURAT Din Basa Shiga Harkanta, Don Fada Da Ita Ba Riba.................!
Bayan Watanni, Maymunatu Tagama Nursery 3, Yayinda Salahuddeen Yake Nursery 2, Inda Lokacin New Session Na Daukan New Student Aka Kai Maymunatu Ta Zana Entrance Exam Na Shiga Primary 1, A Makarantar STAFF SCHOOL dake Cikin Campus Din Unimaid Din, Inda Sakamakon Exam Yafito, Iyaye Sunata zuwa School Din Don Duba Ko Sunan 'Ya'yansu Yafito A Wanda Sukaci Exams din, Aikuwa Malam Muhammadu Yaje Yadubo Kuma Cikin Sa'a Da Hukuncin Ubangiji Saiga Sunan Maymunatu Yafito, Harma An Ce Akawo Daliban Dasukaci Don Ayi Musu Registration Sunfara Karatun, Nan Yadawo Gida Yasanar Da Umma Dasu Maymunatu, Aikuwa Tsalle Da Murna Wajen Maymunatu Ba'a Magana, Inda Umma Tayi Addu'a Dafatan Alkhairi Ga Lamarin, Suka Amsa Da Ameen Gabadayansu............!
Da Ranar Interview Tazo, Malam Muhammadu Yakai Maymunatu Akayi Mata Interview, Kuma Ta Amsa Dukkan Tambayoyin, Aka Bata Entrance Form, Da List Din Abubuwan Da Ake Bukata, Dama Dukkan kudin Daza'a kashe Wajen Yin Registration....
Washegari Kuwa Malam Muhammadun, Yatafi Kai Maymunatu Bayan Umma Tacike Mata Form Din, Ansa Passport Ajiki, Nan Malam Muhammad Yabiya Komai, Akabata Uniform Da Learning Materials, Kuma Akace Ran Monday Za'a Fara Karatu A Sabon Term Din, Kasancewar Ranar Larabace, Don Haka Suka Amsa Komai Suka Tafi Gida Maymunatu Nata Murna Zata Shiga Primary 1....
Monday Nayi Umma Ta Shirya Maymunatu Cikin Sabon Kayan Makarantarta Da Lunch Box Dinta, Da Jakar Makarantarta, Komai Sabo, Malam Muhammadu Suka Fita Inda Suka Fara Shiga LAURAT NURSERY SCHOOL Aka Ajiye Salahuddeen, Sannan Aka Wuce STAFF SCHOOL Aka Ajiye Maymunatu, Sannan Malam Muhammadu Yatafi Wajen Aiki, Inda Kafin Su Fito Abban Yaran Yacema Umma "Idan Karfe 1:00pm Tayi Taje Ta Dauko Maymunatu A Staff School din", Amma Tafara Dauko Salahuddeen Idan 12:30pm Tayi Kafin Lokacin Tashin Su Maymunatu Yayi, Sai Sutafi Tare Da Salahuddeen Su Taho Da Maymunatun.........
Haka Umman Yaran Tayi Kamar Yanda Abban Yaran Yafadamata.......!
Da Shekara Ta Zagayo Salahuddeen................!
Taku Har Kullum
Maymunatu AbubakarDon't 4get 2 Vote, Share & Comments 🤝🤝🤝
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..