Maymunatu tafara karatunta a sa'a da nasara, karatu ya fara zafi, kasancewar da bambanci tsakanin karatun Primary dana secondary School, haka dai take daukan darasi ka'in da na'in, term din farko da suka zana exams maymunatu tayi kokari sosai, haka dai takeyin karatun cikin jajircewa,a haka har ta kammala j.s.s 3, inda suka zana g.s.c.e suna kokarin shiga s.s.1 yayinda shima salahuddeen yake j.s.s 2.1st Term Begins S.S 1A
Wata yarinyace chocolate beauty, shekarunta sun kai 14years, matsakaiciyace, tanada oval face, da kwayan idanuwa madaidaita wanda ake kira da sexy eyes ko bold eyes da zara zaran gashin ido da gashin gira bamai yawaba, saikuma dogon hanci mai tsini makar biro amma yanada dan fadi kadan, sannan da karamin baki mai dauke da fararen hakora reras, hannunta reras da siraran yatsu masu ban sha'awa, dirin ta kyaune wanda ake kira figure 8 ko coca cola shape, diri mai daukan hankalin mai kallonta, yarinyace santaleliyar budurwa sankowa kin wanda ya rasa, yarinya Mai Farinjini, ga ilimi, ga hankali da natsuwa, sannan akwai tarbiyya, tanada zurfin tunani da hangen nesa sosai, yarinya ce mai tsantsan ladabi da biyayya, ga girmama nagaba da ita, akwaita da tausayi dajin kai, ga son taimako ga wanda ya chanchanci a taimaka masa.
Yarinya yar black beauty tsaye take a bakin titin unguwarsu, tana jiran dan mashin ta tsayar ta hau yakaita makarantarsu dake cikin unimaid campus din, tana sanye da uniform white shirt mai dogon hannu, sai wando navy blue, da Sai hijabi navy blue shima mai dauke da tambarin makaranta ( Demonstration Secondary School Unimaid ), ta Sakaya kafanta da farar safa cikin bakin takalmi cover shoe sai sheqi yakeyi yasha folish, bayanta rataye da school bag black colour, fuskarta babu makeup amma dukda haka fuskartata fresh sai sheqi takeyi tamkar tafito daga engine, tayi kyau iya matuka sai baza kamshin turaren "White Oud" takeyi.
Kasancewar ranar monday ce, "monday ranar aiki ko nasara na tsoranki" shiyasa titin unguwar tasu cunkushe yake anata zirga zirga da ababen hawa, masu kai yara school nayi, masu tafiya wurin aiki nayi, masu sammakon zuwa wuraren sana'a suma ba'a barsu a bayaba, hakance tasa idon jama@ yayi yawa akan Maymunatu, duk wanda ya kalleta saiya sake kallonta, hakance tasa Maymunatu tafara gajiya da tsayuwar, ta hade rai don ta tsani kallo sai taji ranta yagama baci, gashi ababen hawan sunyi wuya, ko wanne yataho da passenger akai.
Karfe 7..............,..............
Short boring chapter, Hhhmmnn karkuji komai Yanzu labari yafara daukan salo mai kayatarwa da nishadantarwa, kudai kubiyoni kucigaba da jin yanda labarin Maymunatu zai kaya, kudai kubiyoni a next update dina kuji yanda zata kasance da Maymunatu...
Ina Neman Afuwanku Dakuyimin Uzuri Najina Shiru Dakukayi Banyi Update Ba Tun Shekaranjiya Danayi Alkawari, Hakan Tafarune Sakamakon Matsalan Wutar Nepa Da Nasamu, Wayata Babu Chaji Shiyasa, Amma Yanzu In Sha Allah Zaku Dinga Samun New Chapter In Sha Allah Koda Sau Daya Ne Kullum 🙏🙏🙏
Taku Har kullum
Admin Maymunatu
Garkuwar Mata
Marubuciyar Al'ummaDont 4get to Vote, Share & Comment
Ina Alfahari Daku Masoyana, Makaranta Novels Dina 🙏🙏🙏
I Love You All
Allah Yabar Zumunci
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
Genel KurguThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..