Chapter 22

11 1 0
                                    

Bayan shekara 1 da haihuwar **Fadimatu Zara'u**, malam muhammadun ya taso da maganar karin aure, nan yake fadama umma cewar ""aure zai kara kuma Asabe sai aura"", umman tace "wace asaben kake nufi?", Yace "asabe mai tallan gyada", sai da 'yan hanjin umma suka hautsuna, gabanta yayi mummunar faduwa, take taji wani irin ciwon kai ya kamata nan take harda wani jiri taji yana dibanta, nan ta dafe kirji don ji tayi kamar an chakamata mashi, ta fara karanta addu'ar da duk tazo bakinta, bayan wasu mintuna tafara dawowa natsuwarta, sannan ta daure ta dake tace to Allah ya sanya Alkhairi, yabaka ikon yimana Adalci, yace "Ameen, kuma har ansa ranar auren, nan da wata 2", tace " Allah ya nunamana".

Nan malam muhammadun yacigaba da shirye shiryen aurensa, don rigima irin ta maza maza, kana gidan haya, sai karo aure koda Bakada Wadataccen waje, don kawai Allah ya kara budamaka samu da rufin asiri, saboda runto shida ba gidansaba haya yakeyi, amma haka yasa masu aikin gini, suka cire kofar garage jin gidan, dayake babbane aka maidashi room & parlo, aka fidda kofa tacikin parlon gidan, aka fidda winduna 2, akayi painting, aka yi weiring na nepa, aka sa duk abunda ake bukata, saiga waje fes yafito sai kamshin fenti dakunan keyi.

Amma fa duk gyaran nan da malam muhammadun yayi batare da sani ko neman izinin masu gidan bane, aikuwa akasamu wani dan tsugudidin yaje yafadama mamallakan gidan, aikuwa Saiga Kalifa babban dan masu gidan yazo, a fusace yana zage zage na rashin mutunci yanacewa sai an biyasu, dama shi ɗan Shaye Shaye ne na karshe, don yanzuma a mayensa yataho, babu wanda baisan halinsaba, don yan drugs sunsha Zuwa gidan mamaye zamu kamashi, sai ya gudu, ko ya shiga cikin ceiling yakwana Aciki, sai sungama patrol suntafi zai fito da safe, kai harma daga karshe yadena kwana a anguwar gaba daya, yakoma gidan yan club dinsu a tudun wada, to Haka dai ya karaci zage zagensa yatafi, don umma ta sanar dashi maigidan baya nan sai dare yake dawowa, washegari yasake dawowa da safe, mai akai ta kai ruwa rana, haka dai da kyar aka samu aka sasanta da taimakon mutanen Anguwar, daga karshe dai yabada hakuri aka sasanta.

Kowa cikin abokanan malam muhammadun saida suka Kushe auren nasa, suka nuna rashin goyon bayan su, tunda sukaji maganar karin auren kuma wai asabe mai gyada zai aura, kasancewar sun Santa, Don Tana kai musu tallah wajen aikinsu, ko gidajensu tunda tana zuwa gidajen Quaters din na cikin Campus din unimaid.

Amma malam muhammadun ya rufe ido yana cewa shi ba ruwansa, shidai yana Sonta, kuma zai aureta duk da ba tada ilimin arabi balle bokon, amma shi dai yana Sonta kuma zai aureta.

Duk da Haka abokansa basuyi fushi ba, suka cigaba da Fadamai rashin dacewar auren asaben yana malami masanin Addini, kodon tarbiyyan 'ya'yansa, amma so makahone, so hana ganin laifi, hakance yasa idon malam muhammadun ya rufe, bayaji baya gani.

Wata 2 kuwa na cika aka daura auren malam muhammadun da Hafsatu Abdullahi wato asabe, aka kawo amarya ran asabar da yamma, anguwar kaya tayi baki, nan aka cika a gidan, yan kawo amarya suka dinga hayaniya, da ihu kamar gidan dambe, yayinda makota sukai ta shigowa umma dannar kirji, a gaskiya makotanta sun mata kara sosai, saboda zaman amana da mutunci da sukayi, dama idan zama yayi zama makota sune 'yan uwa na kusa...

Yan kawo amarya kuwa harda kunna cassette din wakar Mandiri, suna chashewa da rawarsu harda kure volume, har lokacin Sallan Magriba basuda niyyar kashewa, har sai da aka aiko daga masallaci akashe kida za'ayi Sallah, sannan suka kashe amma fa basu dena ihu da hayaniyarsuba, sai bayan sallan isha suka gama tafiya gaba-daya akabar Amarya Asabe daga ita sai Halinta, kafin Ango Yadawo.

Da farko kadaran Kadahan, zaman uwargida umma da amarya asabe, umman bata taba nunamata damuwar wai ta aure mata Mijiba, kuma taja girmanta, bayan watanni sai abubuwa dayawa na zaman gidan yafara lalacewa, abunda malam muhammadun bayayi da sai yafara tsiro dasu yanayi, wanda kuma yakeyi da yanzu ya janye ya dena, wasu abubuwan kuma ya sauya yanda yakeyinsu daga yanda yasaba, wannan duk sabon tsarin amarya asabene, kunsan ance "amarya bata laifi kota kashe dan masu gida", nidai nace " Wallahi sai dai idan bata kasheba, kuma ta gwada tagani idan hukunci bai hau kantaba",

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now