Chapter 5

29 5 0
                                    

Jaririn yafar Tsala Kuka....'inyaaa 'inyaaa 'inyaaa, Abban Yaran Yaje Bakin Gadon Ya Zauna Yana Kallon Jaririn, Sai A Lokacin Umma Tafito Daga Toilet Don Cire Kaya Tashiga Wanka, Nan Taga Abban Zaune Gefen Gadon, Tamai Sannu Kuma Ta Gaisheshi, Ya Amsa, Sannan Yace " Ashe Kin Haihu ?" Tace " Eh Tun Dare Nafara Nakuda, Nan Dai Ta Fadamai Yanda  Nakudar Ta Kasance" Yace "MAsha Allah, Allah Ya Raya Ya Dayyiba" Tace " Ameen "....

Nan Malam Muhammadu Ya Dau Jaririn ! Yamai kiran Sallah A Kunne Yamai Huduba Kamar Yanda Addini Ya Tanada, Ya Radamai Abubukar Wato Yaro Yaci Sunan Mahaifinsa...Nan Abba Yace Umma Tamiko Dabino Da Zuma Da Zamzam Aba yaron, Inda Abba Ya Lakutamai Zuma A Baki, Sannan Ya Tauna Dabino ya Sake Lakutamai ya Tande Baki kuwa, Sannan Akabashi Ruwan Zamzam yasha...Sai Lokacin Abban Yaran Ya koma Falo Ya Masu Maymunatu Addu'an Tashi Karatu, Saida Kowa Yasha Zuma Kamar Yanda Suka Saba, Yace Suje Suyi Shirin School, Sukace "To ", Suka Maida Alqur'ani Sannan Suka Nufi Dakin Ummantasu...Basu ganta A Bayiba Amma Sunjiyo Motsin ta Cikin Toilet Alamun Tana Wanka ...Nan Sukaga Baby Akan Gado Yamafara Bacci Bayan Abban Ya Ajiyeshi, Sai Suka Fara Tsallen Murna Suna cewa " Lah ! Umma Ta Haihu", " Umma Ta Haihu", Nan Suka Hau Kan Gadon Suna Kallon Baby Suna Jin Dadin Sunyi Sabon Kani Bayan Abdurrahman kuma.....

Ahaka Umma Tafito Tasamu Su Maymunatu, Suka Gaisheta Ta Amsa Da Fara'a A Fuskarta, Tace " Kunga Kaninku ko?", Sukace " Eh Umma", Tace " Kuna Bacci Na Haihu", Maymunatu Tace " Umma Meyasa Baki Tasheniba", Umma Tace, " Aikin Na Manyane Bazaki Iyaba"  Sai Salahuddeen Yace " Umma Babyn Yanada Kyau", Umma Tace " Ai Kai Ya Biyo A Kyau", Yace A'a Umma Shiga Farine Nikuma Bakine Ai" Umma Tayi Dariya Tace " To Baku Tambayeni Sunanshi Ba, ko Bakuso kuji Sunan Kanin Naku ?" Sukace " Umma Munaso ",Tace " Sunan Shi Abubakar Sunan Abbankune, Sai Mu dinga Kiranshi Da Sadeeq", Sukace " To Umma Allah Ya Rayashi" Tace "Ameen".......

Nan Umma Ta Koma Kitchen Tasake Juyo Ragowar Ruwan Zafin Data Rage, Tazo ta Haɗa Tayima Su Maymunatu Da Salahuddeen wanka, Nan Abdurrahman Ma Yatashi Shima Akamai Wanka, Ta Shiryasu Maymunatu Cikin Uniform Dinsu, Abdurrahman Ma Akasamai Kayansa, Sannan Taje Kitchen Don Dubo ko Asabe Taga Hada Breakfast din......

Data Shiga Kitchen din Ta Tarar Asaben Ta Dama Koko Ta Soya Dankalin Hausa Tasamusu A Kulan Zuba Abincinsu, Nan Umma Takira Maymunatu Da Salahuddeen Sukaje Kitchen din Suka Sameta, Nan Tace Maymunatu Ta Dau Jug din kokon da Suga, Shikuma Salahuddeen Yadau Flate, Spoon Da Chokula, Yayinda Umman Tadau Flask din Dankalin Da Robar Yaji Suka Nufi Dakin Umman Don yin Breakfast Din..........

Malam Shehu kuwa Saida yadan Jira Su Maymunatu Don Yau Basu Gama Shiryawa Da Wuriba Kasancewar Sun Bata lokaci wajen Shiryawa don Sun Tsaya Kallon Baby, Nan Dai Suka Dau Jakan Makarantarsu, Yadafasu Ta Tofesu Da Addu'a, Suka Fita Tanacewa " kuyi Addu'ar Fita gida", Sukace " To Umma ",Tace  " To Ayi Karatu Da Kyau Banda Wasa A Aji", Sukace To umma "............

Abba Kuwa.................

Taku Har kullum
Maymunatu Abubakar
I Love You All My Fans

Don't 4Get 2 Vote, Share & Comments 👏👏👏

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now