Chapter 29

13 1 0
                                    

Bangaren islamiyya ma satin daya zagayo akayi hutun karshen zango, inda maymunatu tayi 1st position, salahuddeen yayi second position, da suka dawo gida ran hutu wacce ta kama ran laraba, sai gasu da report sheet dinsu da paper din jarabawa, hade da kyaututtuka, saboda kyaututtukan 1st & 2nd position aka basu maymunatu da salahuddeen, da kyautan zuwa da wuri, da kyautan tsafta, sannan da kyautan dalibai mafi natsuwa da tarbiyya, haka suka shigo gida da murnansu, baki har kunne sun kasa boye Farincikinsu, nan suka shiga da sallamarsu, umma tana falo zaune itada Sadeeq da fadimatu, nan ta amsa musu suka shiga falon suna rige rigen gaida umman don suyi saurin bata report sheet dinsu da kyaututtukansu dasuka shigo dasu, nan ta amsa gaisuwar tasu suna ta rige rigen bata labari, ta amsa tana duba  report din nasu, nan ta dinga murna tana fadin "Masha Allah, madallah da wadannan yara nawa 'yan Albarka masu kokari, Allah yakara basira da fahimta, ubangiji ya Albarkaci Rayuwarku, yabaku Ingantacciyar Rayuwa, yasa kugama da iyayenku da duniya lafiya", sukace "Ameen Thumma Ameen".


Sai data dafa kansu, tamusu ruwan Addu'o'i na tsari karin Albarka, sannan tace "to kyaututtukan ku sai Abbanku yadawo za'a bude sai muga menene a ciki kuka samo yaran umma da abba" sukace "to umma", nan suka wuce sukayi abubuwan da umman ta koya musu suyi idan sun dawo daga makaranta, sannan suka zauna cin abinci, sun kammala cin abincin anata kiraye kirayen sallan magriba, don haka umma da yaran sukayi haramar sauke faralin gaida Ubangiji.


Yaran sunyi bacci kafin Abban nasu yadawo, don haka sai da asuba bayan sun Idar da karatun Alqur'ani da Asuban, sannan aka dauko kyautukan da report sheet dinsu, Abban yadinga dubawa daya bayan daya, yayinda nishadi da farinciki suka lullube mahaifin yaran, yayita jin dadi har cikin ransa, don baiyi asarar kudin makarantarsu ba,  aka fara bude kyautar farko, inda aka rubuta **Best Punctual Students**, aka bude Raping paper, Agogon bangone kato mai kyau maroon colour, sai kyauta ta biyu, an rubuta **Best In Neatness**, flask din ruwan zafi ne aciki na silver mai kyau, sai gift din Maymunatu na 1st position, packet din exercise book ne, da biro 6, da pencils 6, da cleaner da shapner harda colour pencil, yayinda shi kuma Salahuddeen mai 2nd position aka bashi exercise book guda 6, pencils 3, da cleaner da shapner, harda colour pencil, kyauta dalibai mafi natsuwa da tarbiyya kuwa Alqur'ani mai girma da tsarki guda 2 aka basu kowa day_day, **juzi'u Yaseen**,nan mahaifinsu yayita sa musu Albarka trailer trailer, saida aka gama murnan ganin kyaututtukan sannan suka tashi daga falon, Abba yatafi dakinsa, umma da yaran suka dunguma dakinta don dasa sabon hira ita da yaranta

Haka dai................


Short Chapter, Ayimin Hakuri Readers, Wallahi am Always Busy and occupied now adays, Shiyasa Nake updating short chapter.


Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

Taku har Kullum
Admin Maymunatu
Garkuwar Mata
Marubuciyar Al'umma

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now