Chapter 13

21 4 0
                                    

Zaman Malam Muhammadu da Iyalansa A Gidan Dan Mulki, Kadaran Kadahan, Umma Da Matar Gidan Maman Maryam, Suna Zaman Lafiya, Kasan Halin Mata Na Zamunci da Saurin Sabo, Musamman Idan An Fahimci Juna....Maman Maryam Nada Babban Danta Ibrahim, Sai Kanwarshi Maryam.....A Bangaren Dan Mulki Kuwa Mutum ne, Mai Fada, Mara Hakuri, Don Sai Yazo Yanama Malam Muhammadu Fada Da Korafin Suncika Amfani Da Kayan Electronic, kudin wuta Yakaru, Don Basu Suke biyan kudin Nepa ba, Dama umma Nada electric Cooker Har 2 Datake Girki Dasu, Ga Heater Nasa Ruwan Zafi, Ga Iron Na Guga, Shiyasa Gashi kudin Hayar ma ba wasu masu Yawa bane, Har Takai Daga Karshe Yace Sai An Raba Kudin Nepan Suma Su Biya Rabi, Haka Dai Malam Muhammadu Yabashi Hakuri Yace Kuma Zai Biya In Sha Allah Idan Ankawo Bill Karshen Wata, Sai A Sannan Suka Samu Sa'idan Masifan Dan Mulki, Haka Dai Suka Cigaba Da Zaman Hakuri A Gidan Har Zuwa Wani lokaci............

Ana Cikin Haka Kuwa Wata Safiyar Juma'a Umma Ta Tashi Da Ciwon Nakuda, Tun Asuba, Haka Dai Taketa Dauriya Da Karfin Hali, Har Dai Malam Muhammadu Ya Shirya Yafita, Nan Dai Nakuda Tacigaba Da Karuwa Tana Nukurkusarta Har Zuwa Karfe 2:00pm Rana Inda Ta Haihu Lafiya Santalelen Jaririnta Namiji Mai Kama Da Ubansa, Nan Umma Ta Yanke Cibi, Kasancewar Tayi Karatun Unguwar Zoma A Tsarin Islamic, Shiyasa Tasan Abunda Yakamata Tayi, Amma Tsarin Malam Muhammadu Ne Bayason Zuwa Asibiti Don Shi Yana Bada Magungunan Musulunci Wato Dibbun Nabawiy, Takira Salahuddeen Dake Falo Dayake Tun Sanda Taji Haihuwar Ta Taho Tace Salahuddeen  Yakoma Falo Ya Zauna, Tace " Jeka Kiramin Maman Maryam" Yace " To Umma"  Yafita Kiran Maman Maryam Din.......

Salamun Alaikum Maman Maryam Takeyi A Kofar Dakin Umman, Daga Ciki Umman Ta Amsa Tace Tashiga, Maman Maryam Na Shiga Taga Jariri Tace " Maman Salahuddeen Ashe kin Haihu " Umma Tace Wlh kuwa Maman Maryam Ai Tun Asuba Nafara Nakuda Kadan Kadan, Sai Yanzu Dai Na Haihu, Tace " Masha Allah, Shiyasa Banji Motsin kiba Tun Safe, Allah Ya Raya Ya Dayyiba  " Umma Tace " Ameen "..

Nan Maman Maryam Tasa Ruwa A Heater Don Lokacin Akwai Nepa, Nan  Ta Gyarama Umma Wajen, Ta Gogema Jariri Jiki Da Man Zaitun, Tasamai Kaya Don Ba'ason Ayi Ma jariri Wanka Daga Haihuwarsa, Sannan Ta Haɗa Kayan Zannuwan Da Umman Tayi Amfani Dasu Suka Ɓaci, Tafita Dasu Tajika zata Wanke, Sai Ga Sallaman Malam Muhammadu Yadawo Daga Masallacin Juma'a, Nan Ya Tarar Umman Ta Haihu, Yace "Ashe kin Haihu" Tace "Eh", Yace "Allah Ya Raya, Me Muka Samu" ?? Umma Tace "Ameen, Namiji Aka Samu", Malam Muhammadu Yace Miko Minshi Namai Huduba, Tace " To Sannan Tamikomai Jaririn", Nan Yayi Bismilla, Yamai Kiran Sallah A Kunnen Dama, Yamai Huduba Da Suna Abdurrahman.........
Yasake Cewa Umma Tamiko Zuma Da Dabino Da Zamzam Aba Jaririn, Nan Tamiko Ya Tauna Dabino Ya Bashi, Sannan Yasake Lasamai Zuma Kuma Yabashi Ruwan Zamzam Yasha, Yaro Yanata Tande Baki Yaji Zaki.................

Haka Kwanaki Suka Cigaba Da Wucewa Har Akazo Gobe Suna, Inda Kannan  Umma Su 2 Sukazo Daga Kano, Da Yayan Bichi Da Yaya Mami,...................

Ran Suna Ko Yaro Yaci Suna Abdurrahman, Inda Maman Bichi, Da Yaya Mami Dama Maman Maryam Sukayi Aikin Soya Naman Suna, Suka Gyara Gidan Sannan Suka Dafa Abincin Dazasu Ci, Haka Dai Suka Wuni Aiki A Gidan, Sai Yamma Suka Karasa Sukayi Wanka, Sannan Suka Zauna Hutawa......

Sai Da Sukayi Sati Sannan suka Shirya Suka Koma Garin Na Kano, Cike Da Farinciki Da Nishadi, inda Gaba Ɗaya Suka Sauka A Unguwar Kofar Nassarawa Gidan Su Umman Wajen Inna Sabuwa, Aka sauke Yaya Mami, Sannan Maman Bichi Ta Wuce Bichin Bayan Ta Huta.......

Haka Rayuwa Tacigaba Da Gudana, Da Dadi Daba Dadi, Cikin Rufin Asirin Ubangiji.....

Garin Kano A Unguwar 'Yankaba................

Bayan Su Malam Muhammadu Sun Koma Garin Maidugurin, Sun Bar Maymunatu Wajen Kakarta Gogal,.............

Haka Rayuwar Maymunatu Tacigaba Da Gudana, Inda Take Shagalinta Son Ranta, Kun San Rikon Hannun Kaka, Tayi Rigima Tayi Shagwaba, Amma Bazai Hana Tayimata Tarbiyya Ba, Tana Kwabarta Daidai Gwargwado, Amma Wani Bai Isa Ya Tabataba Zakasha Fada Kuwa, Sannan Ba'a Mata Magana Da Hausa Sai Fulatanci, Kasancewar Kakartata Asalin Bafulatanar Garin Na Maidugurin Ce, Don Haka Bata Yarda Al'adaba, Don ko Ita Indai Zatayi Magana Dana Gida Ko Dangi To Da Fulatanci Zatama Magana, Sai Dai Sauran Mutane Datake Hulda Dasu Ko Mu'amala , Don Haka Maymunatu Ta Koya Fulatanci Sosai Wajen Kakar Tata, Bazaka Taba Jin Suna Magana Da Hausaba Ko Da Baki Akayi,.......

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now