Chapter 6

23 3 0
                                    

Abba Kuwa Dakin Asabe Ya Shiga Bayan Fitarshi Daga Dakin Umma, Da Alama Bacci Ya Koma, Don Sai Wajen Karfe 10:00am Yafito Da Shirin Fita Shagon Sana'ar Shi, ta Saida Zuma da Sauran Kayan Islamic Chemist, Wato Dibbun Nabawiy, Anan Cikin Unimaid Campus, Shagon Na Jerin Rukunin Shagunan Dake Kallon Hostel 1&2 Na Mata, Kuma Kullum Karfe 10:00am Ake Budewa, A Rufe Karfe 10:00pm, Amma Watarana Idan Ba Customers Yakan Rufe shagon Bayan Isha ko Karfe 9:00pm Yakoma Gida...

Itako Asabe Ko Kallon Umma Batayiba, Balle Tayimata Barka duk da Abban Yara yafadamata Haihuwar Da Umman Tayi, kuma Tafito Ta Ga Ba Cikin jikinta, Amma Dan Bakin Hali ko sannu batacemataba, Itama Umma Cigaba Da Sabgar Gabanta Tayi, Chan wajen 12:00pm Saiga Murja da Hadiza Da Laure, Kannan Asabe Ne Sun Shigo da Shewa Da Dariya Kamar Marasa Hankali, Idan Ka Kallesu Wallahi Saikayi Dariya Har Cikinka saiya kulle, Saboda Sun Chaba Uban Kwalliya Kamar Daga Turu suka Fito, Ga Wani Uban Baki An danbara A gida, da Jan baki An lafta A Lebe, An Kuma Tsiro Dankwali Gaban Goshi irin Na Daso Ture Kaga Tsiya, kaida gani Kasan kyauyanci Yasamu Wajen Zama, Ga Jahilci Dake Damunsu Tunda Ba Arabi Ba Boko, Darajan Tallah Da Neman Kudi Kawai Suka Sani,...........

Domin Tallan Dafafiyar Masara Sukeyi Da Gyada Da Gujjiya, Idan Kuma lokacin Kayan Ganyene sukoma Saida Kabeji, Karas da kokonba, Haka Idan Lokacin Arahar Albasa yazo sukoma Siyarwa, A Bakin Gate din Unimaid, inda Student din  Staff School, Da Demonstration Secondary School, da Daliban Jami'ar Unimaid Idan Sun fito tafiya gida Suke Tsayawa Suna Siya,
Kokuma Su Shiga Cikin Unimaid Campus din, Su Zagaya cikin Gidajen Quaters din suna Tallah Asiya Amusu ciniki, kuma Suna Samu don wani lokacin Kafin sufito An Siye Duka Sai Dai Sufito Sutafi gida........

Babu wanda Bai Sansu A Arean Ba Kasancewarsu Fitsararru, Ga Rashin Mutunci, Ba Arabi Ba Boko, Basa Ganin kowa Da Gashi, Batsa Da Zagi kuwa ko Maguzawa Albarka, Haka Suka Wuni A Gidan Suna Tsula Iskanci Da Hayaniya, Sai Yada Habaici da Bakaken Magana Wai duk don umma Taji Ta tanka Ayi Bala'i,.........

Ita Kuwa Umma Batagaji Fadaba Balle Gayyar Haqoriba, don haka Ko Kallon inda Sukema Batayiba, iskar Data Debosu Ta Ajiyesu A Wajen Ma Bata Shaqaba Balle Tasan Da Wanzuwar Numfaahinsu, Tattarawa Ma Tayi Ta Shige Ɗakinta Abunta...Ranar Saboda Zuwan Kannanta, Da Wuri Tagama Abinci, Sukaci Suka Sha, Suka Saka Cassette Din Wakar Mandiri Suka Kure Volume Kamar Gidan Ubansu, Suka Chashe Da Rawarsu Son Ranasu, Sai Yamma Liqis Suka Tattara Komatsansu Suka Kara Gaba,

Umma Kuwa Zuw Kitchen Tayi Ta Dauko Food Flask Din Abincinsu, Da Flats Da Spoons Da Ruwa Takai Musu Daki, Tazuba Sukaci itada Abdurrahman, Sai Yamma Liqis Yan Makaranta Suka Dawo, Suka Cire Uniform suka Wanke Hannu Sannan Umma Tazuba Musu Abincin Sukaci, Suka Sha Ruwa Kowa Yace Alhamdulillah, Sannan Sukaje Wajen Kaninsu Sadeeq Sunamai Wasa, yayinda Shima Abdurrahman Yazo ya Tsaya Yana Kallon Jaririn......

Yau Kwana 6 Da Haihuwar Umman, Ana gobe Suna Kenan, Kanwar Umman Da suke Uwa Daya Uba Daya, Tazo da 'yarta A'isha Tana Goyanta, Da Yan uwan Umman Su 2, Aunty Binta Da Yaya Murja, Sunzo daga Kano Bichi Local Government, kasancewar Umman Haifafiyar Garin Na Bichine dake cikin Birnin Kano ta Dabo Tumbin Giwa...Umma Bata Taron Suna Amma, Idan Ta Haihuwa Kanwarta Da Yan Uwanta mutum 2 Zasuzo Mata sumata suyan Nama da Aikace Aikacenta, Sumata Sati Daya ko biyu Sannan Sukoma........

Wacece UMMA .....???????

Taku Har kullum
Maymunatu Abubakar

Don't 4get To Vote, Share & Comments 👏👏👏

Ana Mugun Tare Fans Dina 🤝🤝🤝💯

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now