Gidan Dan Mulki........!
Bayan Sun isa Gidanne, Malam Muhammadu Ya Ciro Dan Mukullin Acikin Aljihunsa yabude suka Shiga, Sai A Lokacine Umma Ta Tuna Ashe Babu Tsintsiyar Shara, Sai Tace Ma Abban Yaran " Bari Na Aromana Tsintsiyar Wajen Matar Gidan", Yace " To", Nan Ta Shiga Cikin Gidan, Tanayin Sallama, Aka Amsamata Sallaman, Matar Ta Fito Daga Daki Tana Daura Dankwali A kanta, Suka Gaisa Ta Fadamata " itace Sabuwar Makociyarta Sunzo Sharane Amma Basu Taho Da Tsintsiyaba saboda Badaga Gida Sukeba basu Dauko Kayaba, Don Allah Tabata Aron Tsintsiya Da Abin Kwashe Shara", Nan Matar Gidan Wacce Ake kira Da Maman Maryam, Ta Daukomata Tabata, Nan Tayi Godiya Ta Koma,.............!
Tsintsiya 2 Tabasu don Haka Suka Raba Suka Fara Sharan Itada Abban Yaran, Nan Da Nan Suka Share ko'ina Tas Tas, Suka Kwashe Sharan Suka Zuba A Dust bin din Dasuka Gani a Tsakar gidan Kusa Da Kofar Fita, .............Sai Umma Tace " Bari Ta Maidamata Tsintsiya Da Parker" Abba Yace "To", Ta Maidamata Sannan Tayi Godiya, kuma Tasake Aro Musu Tsumma da Bokiti da Ruwa Aciki Data Taro A Fanfon Tsakar gidan, Tashiga Dakin Takecema Abban Yaran "Ai Babu Omo", Yace "To Bari Nafita Na Siyo tunda Akwai Shaguna A Kusa", Nan Yaje Ya Siyo Yadawo, Umma Ta Amsa Tayi Godiya, Sannan Ta Zuba Acikin Ruwan Takada, Ta Goge Ko'ina Kal Kal, Ta Wanke Tsumman Ta Sanya A Kan Igiyar Data Gani A Tsakar Gidan.........
Misalin Ƙarfe 5:00pm, Malam Muhammadu Yacema Umma " Yanzu An Tashi Department, Bari Naje Nasamu Yara Su Tayani kwaso Mana Kaya" Tace "To", Nan Yafita Yatafi, Umma Kuma Ta Zauna Tana Hutawa Kafin Yadawo,......
Isarshi Office Din Malam Idris Kenan, Yasamo Yara Almajirai masu Yawo cikin Unimaid Din, Yace Su Tayashi Daukan Kaya, Sukace "To", Nan Su 3 suka Rugo Suna Rige Rigen Son Daukar Kayan, Malam Muhammadu Yace, Don Allah Ku Dakata Karku Zubarmin Da Kaya, Sukace To Zamu Dauka A Hankali,.............
Nan Ya Raba Kayan Gida 4, Su 3 Kowa Ya Dauka, Shima Yadau Kaso Daya, Suka kulle Office din Sai Gidan Dan Mulki, Da Isarsu Sukayi Sallama Suka Fara Dire Kayayyakin, Malam Muhammadu Yana Biye Dasu, Bayan Ya Sauke Nashi Kayan Sannan Yace " Yawwa, Sannunku da Kokari" , Sukace " Yawwa", Nan Yaciro Naira ₦60, Yace Suraba 20_20, Suka Amsa Sukace " Allah Ya Karba" Suka Fita Dagudu Suna Murna Da Farinciki Daga Gidan,.............
Nan Umma Tace "Sannu Abban Yara", Yace " Yawwa, Bari Na Tayaki Gyara Kayan", Umma Tace " A'a Daka Barshi Ka Huta", Abban Yaran Yace " A'a Ai Gwanda Nakarasa Ladana, mun fara Tare Mugama Tare", Tace " To ",........
Nan Suka Hadu Suka Karasa Gyara Kayan, Kowanne Akasashi inda Yakamata Ya Zauna, Sa Labulayene Ya Rage, Nan Abban Yaran Yace " Wannan Aikin Mazane, Bari Nayi, kinsan keba Tsaho ne Dakeba Sai Kin Hau Kujera Kada Kizo ki fado, kinsan Kin sha Aiki Kin Gaji ", Tace " Dama Bazan Iyaba Sai Kai ", Umman Tace " To Ni Bari Naje Namana Wankin Bayi Kafin Kagama ", Yace " To ", Nan Ya Hau Ya Buga Kusoshi Yasaka Musu Labulaye A Winduna 4Da Kofofin 2 Tunda Daki 2 Ne Daban Daban........
Bayan Tagama Wankin Toilet din, Ta Dauro Alwala, Kasancewar Anata Kiraye kirayen Sallan Magriba, Sai Data Fito Ta Tarar Da Abban yana Jiranta, Nan Shima Yayi Alwala, Yakira Salahuddeen Shima Yayi Alwala, Suka tafi Masallaci, Umma Kuma TaShiga Daki Don Yin Sallah itama,...............
Haka Rayuwa Tacigaba Datafiya, Wataran Asamu, Wataran Babu, Haka Dai Iyalan Malam Muhammadu Suke Hakuri Da Rayuwa A Yanda Suka Tsinci Kansu Aciki, Har Allah Yasa Malam Muhammadu Ya Kammala Deegree Dinsa Na 2, A Fannin Islamic Law, Kasancewar Shi Gwarzon Dalibinsu Mai Hazaka, Hakan Tasa Yanemi Aiki A Faculty Of Law Din, Kuma Suka Daukeshi Aikin, Kasancewar Sun Sanshi Sosai, Sai Gashi Ma'aikaci A Department Din Kuma Cikin Lecturers Dinsa...Haka Yafara Zuwa Aiki Cikin Sava Da Nasara Da Kwarewa,.....
Ba Laifi Yanzu Yana Samun Kudin Albashi Don Haka Iyalansa Sunfara Samun daukaka Da Karin Rufin Asiri, Inda Umma Kuma Take Dauke Da Ciki Haihuwa Ko Yau Ko Gobe.........!
Wannan Kenan.........👌
Don't 4get To Vote, Share & Comments 🤝🤝🤝
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..