Chapter 24

16 2 0
                                    

Yau kam gidan malam muhammadun cike yaki da murna gamida shirye shiryen tarban babbar bakuwa mai daraja ta 1, domin mahaifiyar malam muhammadun ce mai suna Maymunatu wato gogal ce zatazo daga garin Kano ta Dabo tumbin giwa zuwa garin na Maidugurin.

Ana ta gyara mata inda zata sauka, dama dafa abincin daza'a tarbeta dashi, wannan kuwa duk aikin Uwargida umma ne mai sanin yakamata da hangen nesa, mai neman lada ta kowace hanya.


Haka umma tacigaba da kaiwa da komowa, tana dafama uwarmijinta girki mai rai da lafiya,  inda tadafa mata Alkubus da miyar taushe wadda taji nama da tantakwashi, ga fish pepper soup yaji kayan kamshi, da lemon karas wanda yaji peak milk yadau sanyi, gefe kuwa ta soya mata doughnut mai dankaren taushi, kai madallah da Hajiya umma gwana wajen iya sarrafa girki mai sa kunnan mutum ya motsa don dadi.


Ana kiran sallan la'asar daidai babbar bakuwa ta iso, da sallamarta tashiga gidan bayan dan nata yana gaba yana mata jagoranci, malam muhammadun rike yake da kayan mahaifiyar tashi, suka shiga gidan inda umma tafito da sauri falon tana musu sannu da zuwa, kuma ta amsa kayan bakuwar ta shiga dashi, nan yamata iso ta zauna a falon, nan ta zube suka gaisa cikin fara'a da girmamawa, sannan umma tayima malam sannu da zuwa shima suka gaisa, nan yamusu sallama yakoma shagon sana'ar tasa bayan umman ta hadamai abincinsa a basket yatafi dashi, don yaba mahaifiyar tasa damar huta gajiya da sauke faralin sallolinta, dama cin abincin da aka tanadar mata.

Ruwan sha tafara kawo mata mai sanyi cikin Jug da cup a dan karamin flate, nan ta amsa da godiya ta tsiyaya tayi bismillah tasha, bayan tasha ta maida numfashi na wasu mintuna ne tace a nuna mata toilet zatayi alwala tayi sallah, saita zauna gaba daya, nan umma ta yimata Jagoronci zuwa dakin nata ta nunamata toilet din, sai dataga ta shiga sannan ta shinfida mata daddumar Sallah tafita a dakin takoma falo don gabatar da nata sallan.


Bayan mintuna 30 sai umma ta haɗa mata kayan abincin shaqe da katon try ta kaimata har masaukinta ta ajiye, ta tarar bata Idar da lazimiba, don haka ta ajiye tafito.


Bayan mintuna 15 tasake komawa ta tarar ta Idar da lazimin har ta ajiye charbin, amma bata zuba abincinba, tana zaune kawai, kunsan mutanen da akwai kawaici da kunya, musamman kunya tsakanin uwar miji da matar danta, sai kaga ana kawaici kamar dan fari, don haka Gogal din take dan kunyar Umman.


Nan suka sake gaisawa, umman tace naga baki fara cin abincinba, bari na zuba miki, nan ta zuba mata Alkubus da miyar taushe a Flate, tasake zubamata papper soup Kadan a dan bowl ta ajiye kusa da ita tasamata spoon aciki, tana kokarin zubamata lemon karas ne gogal din tace " a'a kibari sai nagama cin abinci sai nazuba nasha, don bana shan abu sai nagama cin abinci", umma tace "to", nan tamata sallama ta fita don tabata waje tasamu sakewa taci abincin.


Bayan fitan umma da wajen mintuna 30 sannan hamshaqiya amarya asabe ta isa dakin da aka sauke uwar mijin nata, duk da kuwa taji shigowarsu harda malam muhammadun, amma taki fitowa, sai yanzu dataga dama ta bushi iska shine tafito taje dakin don gaisheta.


Bayan tashigane ta zauna a gefe a darare kamar ta zauna kan kaya, fuskarta sam babu wani fara'a ko walwala, haka dai ta gaisheta kadaran Kadahan, ta amsa, sannan ta tashi tamata sallama takoma dakinta.


Sai karfe 6:30pm su maymunatu da salahuddeen suka dawo daga islamiyya, da sallamarsu suka shiga gidan, bayan umma ta amsa musu, nan suka gaisheta suka mata sannu da gida, ta amsa musu sannan suka wuce ajiye jaka da cire uniform, sannan sukaje suka wanke hannu da klin, bayan sun wanko hannunsu sune umma tace "to aje agaida bakuwa", yaran sukace " umma bakuwa mukayi? wacece tazo?" umma tace "eh, kakarkuce gogal tazo daga kano,", ai da gudu maymunatu tatafi da murnanta jin an ambaci gogal, tana isa dakin ko sallama batayiba tashiga don tsabar murna da farincikin daya lullubeta na zuwan kakartasu, tana shiga ta nufi Gogal din ta fada jikinta ta rungumeta, Gogal din ita farincikin ganin Jikar tata take, sai cewa tayi "ke ni dagani kada ki karyani", maymunatu tace "lale jabbama, usee e datal,  a warti jam?, Noy jama'are 'yankaba?", Sai lokacin Salahuddeen ya isa yayi sallama suka amsa sannan ya shiga, nan ya zauna kusa da Gogal din, suka sake gaisheta atare ta amsa da fara'arta, nan ta kuma tambayarsu ya makaranta da karatunsu, sukaita bata Amsa.


Nan maymunatu ta kara jindadi Kakarta tazo zasu cigaba da yin fulatanci kamar yanda suka sabayi shekarun baya datake zaune awajenta, Saboda gaskiya abbansu bayayi musu yaren fulatancin, kuma baima damu dasu iyaba, amma yanayi a waje idan Yahadu da Bafulatani, kuma yana yarawa da mahaifiyarsa ko yan uwansa, ita kuma umma bataji sosai kamar abba, don bata taso da iyayentaba, tataso gidan kakanni, kuma matsayinta Na Jikar fari a family ake jin kunyarsa, Shiyasa bata Iyaba sosai kuma batayima su maymunatu musamman saboda maymunatu ta kasance yar fari bata sakewa da ita saboda kunya da kara irin ta dan fari, bayan maymunatu ma dai bata iya koyama sauranba, don tariga tasaba da rashin yi tun akan maymunatu, ita kuwa maymunatu tarewarsu a flat din yabata damar yin fulatanci kadan, saboda makociyar su dake flat na 2 bafulatanace, don haka idan suka hadu da yaran matan sunayi, kasan abunka da yara idan suna tare da yara 'yan uwansu, kuma maymunatu hazikar yarinyace mai Son sai ta iya abu matukar tasa kanta saboda akwaita da juriya da jajircewa sosai.

Short Update, Ayi Hakuri Dani Don Allah 🙏🙏🙏

Kubiyoni a next chapter dina don jin wace wainar za'a toya?

Ya zaman bakuwa zai kasance da iyalan dan nata ???

Taku Har Kullum
Maymunatu Abubakar

Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

Love You All My Fans
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now