To Ita dai baiwar Allah umma batasan wainar da ake toyawaba, don bata taba ganin wani alamar dazata fahimci wani abu ba, kuma bazata taba tunanin mijinta zai tsinci kanshi a irin bakaba.......
Har yanzu kuma tana kaimata tallah gida tana siya, kuma bata taba nunamata tana zuwa shagon malam har alakar soyayya ta kullu tsakanin malam da asaben ba.............
Kudin hayar malam muhammadun yakusa karewa, dama yanaso ya nemi wani gidan hayan a wajen campus din, yafiso ya fita daga cikin campus din, don haka yanemi gidan hayan, Chan a unguwar kaya yasamu hayan wani gida mai Flat 3, Amma Flat 2 akwai mutane aciki, don haka yakama flat din daba kowa, flat ne mai 2 bedroom, katon falo, sai kitchen da Varander, da gareji mai gate ta waje, da dakin samari a waje hade da bayi, dakunan duk akwai toilet suma,....
Nan yaje yaga gida, ya biya, aka bashi key aka rubuta shaida da kwanan wata, yatafi ya dauko yaran shagonsa sukaje suka yi sharan yana, suka share ko'ina, suka wanke tass harda Toilet din, Sai ga waje yadau haramin, bayan sungama sun koma shago,sai malam yasake turo malam Tasi'u da malam sabi'u, matasane daliban ilimi, mahaddata Alkur'ani wanda suke tayashi yin Rukiyya a shagon, don haka ya turosu suyi saukan Alkur'ani a gidan kafin ya tare da iyalansa, haka sukazo sukayi Saukan, sai 10:00pm na dare suka kammala, Sannan suka kulle suna shirin tafiya Saiga Malam muhammadun ya iso Wajensu dauke da kulan abinci yakawo musu, ya musu sallama suka gaisa yabasu abincin yace sutafi dashi suci, su amsa sukayi godiya, ya amsa key sukayi sallama suka tafi, shima ya juya ya koma gida...........!
Washegari ne suka fara Parking, inda malam muhammadun ya dau shatan mota, aka kwashe kaya sai unguwar kaya, tare da yaran shagonsa sukaje, nan suka tayashi sauke kayan suka shigar musu da kayan, na daki suka taya umma shigarwa dakin, na falo aka ajiye a falo............
Bayan sun isa Unguwar kayan, an sauke kayan ya sallamesu nan yaga lokaci yatafi yasan anata jiransa Customers sun taru, ya musu sallama yace yatafi shagon idan sun gama su sameshi a shagon, Sannan yatafi....
Suka karasa jera mata kayan, Sannan suka mata sallama ta musu godiya suka tafi,...........
Umma Kuma ta karasa gyara sauran kayan, ta ajiye kowanne a muhallinsa inda makamata, takarayin shara sannan ta kunna turaren wuta guda ya dau haramin kamshi, kunsan umma ma'abociyar tsabta da kamshi ce akoda yaushe...........
Nan tayi wanka sannan tayima abdurrahman shima, ta zuba musu abinci sukaci suka sha ruwa sukayi hamdala da Addu'ar kammala cin abinci ( Alhamdulillahil Lazi Ad'amani Hazal Da'am, Warazaqanihi Min Gairi Haulin Minni Wala Quwwa, Ma'ana : Allah Nagodemaka daka Ciyardani Wannan Abincin, ka Azurtani Dashi Batare da Karfinaba ko Dabarana ), Sannan ta zauna tana hutawa kafin su maymunatu su dawo daga islamiyya, yayinda Abdurrahman ke zaune yana wasa a kusa da ita..................!
Sai kuma ga makotanta na sauran flat din cikin gidan sun shigo an gaisa, nan kowacce ta gabatar da kanta aka danyi hira da wasa da dariya, sannan sukamata sallama kowacce ta tafi bangarenta.................
Sai a lokacin kuma malam shehu mai mashin yakawo su maymunatu sabon muhallin nasu, dama yasan gidan tunda Sunzo da malam muhammadun, don haka daya daukosu ya wuce dasu sabon unguwar tasu mai suna unguwar kaya, nan ya Saukesu sukamai sallama suka shiga gida, Sannan yatafi..............!
"Salamun Alaikum", sallaman su maymunatu da salahuddeen ce takarade kofar falon flat din nasu, dama umma na zaune a falo ita da abdurrahman, don haka ta amsa musu tabasu izinin shiga suka shiga, da fara'ar su suka gaida umman suka mata sannu da gida Kuma sannu da aiki, nan ta amsa da fara'a itama tana musu sannu da dawowa, suka ma abdurrahman wasa inda maymunatu ta daukeshi...........
Ummance ta nuna musu dakinsu da wajen Kayansu, dama duk abubuwan bukatunsu don karsuzo suna nema, nan sukayi godiya, sannan suka cire Uniform sukasa na gida, kuma sukaje suka wanke hannunsu da klin, sannan umma ta zuba musu abinci suka koma falo suka zauna Sukaci sukasha ruwa kuma sukayi hamdala..........!
Kiran sallah magriba da akayi a masallacin kofar gidan ne yasa Mikewa don yin alwala, ta umurci Salahuddeen yayi alwala yatafi masallaci, tace itama maymunatu taje ta dauro alwala tazo suyi sallah a falon kusa da Sadeeq don kar yaga an barshi shi kadai yafara kuka, nan suka tafi kowa yayi alwalan suka tada Sallan...
Bayan sun Idar ne umma tashiga kitchen domin dafa abincin dare, doya ta dafa tayi miyar kwai da Albasa, sannan tanada lemon mangwaro mai dadi, nan da nan ta kammala don duk abinci masu saukine, tagama tana gyara Kitchen din daidai lokacin ana kiran Sallan isha'i, dukansu sukayi haramar yin Sallah............
Bayan sun Idar sun zauna ne take tambayarsu koda mai homework, sukace Babu, tace "to", Nan ta kishingida tanajin radio ana wani program na (Dare Mahutar Bawa a Queen FM Zaria), yayinda su maymunatu suke gefe suna fira da wasa da abdurrahman............
Tambayarsu tayi ko zasuci abincin daren ?? Sukace 'Eh, amma kadan", nan tazubo musu, sukaci suka sha ruwa sukayi ma Allah godiya, lokacin har abdurrahman yayi bacci,
umma ta daukeshi takaishi daki ta kwantar dashi da hannun dama, bayan ta tofeshi da Addu'o'i yanda yakamata,Nan suma su maymunatu umma ta umurcesu dasuje kowa yayi wanka susa Kayan Bacci, suyi alwala sannan su kwanta baccin kasancewar gobe a kwai school..............
Sai lokacin umma tasamu daman sake yin wanka, sannan ta shirya cikin kayan baccinta, tayi dadaidaicin kwalliyar ta, ta feshe jikinta da turare, ta shafa humra, kuma ta feshe dakuna da falon da Roomfreshner mai Kamshin Swiss Rose na Company A.B.C don tarban Mijinnata........
Karfe 9:30pm malam muhammadun yadawo daga shago, nan yashiga da sallamarsa, umma ta amsa, tamai sannu da zuwa, ta amshi food basket din dayashigo dashi wanda yatafi da abinci Aciki, takai Kitchen, Sannan taje ta hadamai ruwan wankan sa, yashiga Toilet din, yayinda umma taciromai kayan baccinsa, ta feshesu da turaren WHITE OUD, ta Dauramai busa gado sannan tafita daga dakin...
Kitchen tanufa ta hadomai kayan dinner dinsa a kan katon try, don tasako komai dazai bukata, nan taje ta kunna Cassette Din Wa'azin Sheikh Isa Ali pantami, inda yake Tafsirin Suratul Zumar, nan ta zauna tana jiransa kafin yagama ya fito falon cin abinci.....
Bayan wasu Mintuna, sai ga Malam muhammadun tsab cikin shigar kayan baccinsa yana tashin kamshi, yamata sallama ta amsa, sannan ya zauna kusa da ita, nan ta zubamusu abincin daidai yanda zasu iya cinyewa, nan sukaci suka kora da lemon mangwaro Mai sanyi da dadi, sukayi hamdala, Saida suka dan taba hura mai dadi a tsakaninsu, sannan umma ta tashi ta kwashe kayan takai Kitchen ta gyara Komai, suka kashe kayan electronic din da hasken falon, malam muhammadun yasa karatun Alkur'ani inda kira'ar Sheikh Ghamidy yake tashi cikin suratul Bakara, yasa volume yanda zai Karade duka gidan, sannan suka nufi nasu makwancin..............asuba tagari 👌
Yaya zaman iyalan malam muhammadun a sabuwar unguwar dasuka koma ??
Ya alakar umma da makotanta dama sauran mutanen Anguwar ????
Yaya rayuwar su maymunatu zata kasance ????
Yaya batun soyayyar malam muhammadun da Asabe ???
To don samun amsoshin tambayoyin nan kubiyoni a next chapter...........!
Taku Har Kullum
Maymunatu AbubakarDon't 4get 2 Vote, Share & Comments
Love You Always My True Fans, Akwai Amana A Tsakanina da ku...!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..