Barister Sunusi Kuwa da Iyalansa Sungama Parking din Kayansu Tsab gobe sai kwanan Abuja Inda Sha Allah...
Bangaren Malam Muhammadu kuwa Abun Duniya Ya Ishe shi, Yabuga Ya Buga Amma Bai Samo cikon kudin dazai biya Kudin Hayan Gaba Dayaba, Cikin ikon Allah Yana Zaune A Kan Varander cikin Campus Din Unimaid Din, Yabuga Tagumin Rashin Sanin Madafa da Hannun dama Ya Jingina Da Bango,....
Sai Ga Daya Daga Cikin Lecturer Malam Muhammadu yazo Wucewa, Sai Ya Tsaya Suka Gaisa Yake Tambayarshi " Lafiya ka buga Tagumi kuma Alamun kana Cikin damuwa ? Nan Malam Muhammadu Ya Labartamai Halin dayake ciki, Malam Idris Yabashi Hakuri yace Bashi da Kudin dazai cikamai yanzu, Sannan Gidanshi Bashi Da extra Room ko wajen zaman dazai iya bashi, Amma Yanada Wani ƙaramin taimako dazai masa kafin Allah yahoremai cikon kudin yakama Hayan, Nan Yace " Zai Bashi key din Office Dinsa,Su dinga Kwana da Daddare zuwa Safe, Saboda Office din Room And parlour Ne, kuma Cikin Ba Kaya Sosai A Palour yake zama da Kayan Office Dinsa komai Da Komai, don haka yace zai basu ciki su zauna zuwa Yasamu kudin, Amma Kasan cewar Gurin Aikine, Sai dai Su zauna kullum Da yamma, su kwana zuwa safe karfe 7:00am, Amma Akwai Toilet Acikin office din, Kuma dole suyi wanka su shirya da wuri zuwa 7:00am din, sai su kulle su fita Saboda Lokacin Time din Aikine har zuwa karfe 4:00pm...........
Washe Gari Tun Da Sanyin Safiyar Ranar Allah Yaba Barrister Sunusi Da Iyalansa Sa'ar Barin Garin Na Maiduguri Sai Garin Abuja Mai Villa...Bayan Sunyi Sallama da kowa, Wannan Kenan.............
Shikuwa malam Muhammadun Komawa Office din Malam Idris din Don Samun mafaka, Haka Sukayi Wannan Zaman Cikin Office din Malam Idris din, da umma da Abba da Salahuddeen, Sunada Electric Cooker Akai Suke Girki, Dama sauran Bukatunsu....
Idan Sun Gama Shiryawa, Shi Malam Muhammadu Lectures Zaitafi, ita Kuma Umma Cikin Campus take Tafiya Gidan Wani Abokin Mijinta Da suke karatu, Sun Saba Sosai, Chan Umma Da Salahuddeen Suke zuwa Su Wuni, Sai Karfe 5pm sai Su dawo Su Tarar da Malam Muhammadu A Office din, Dayake Idan Malam Idris Yatashi Daga Aikin sai yaba Malam Muhammadu keys din kafin gobe Da Safe idan Yazo Ya Amsa............
Bayan kwana 2 Ya Shirya da Dan kudin Hayar dake hannunsa Dabasu isaba yayi kudin mota Yatafi Kano Unguwar 'Yankaba Wajen Mahaifiyarsa don yafadamata Halin dasuke ciki, Allah Yasa Tana Tara Dan kudin ta Idan Tayi cinikin Saida Abincin ta, Haka Ta Dau kudi masu Yawa Tabashi, Sai Daya Kwana Washe gari, Sannan Ya musu Sallama ya kama Hanyar komawa Maiduguri................
Isar Malam Muhammadu Maiduguri Keda Wuya, Ya Wuce Gidan Dan Mulki Yasa Ayi Mai Sallama Dashi, Aikuwa Yayi Sa'a yana Gidan, Bayan Yafito Ne Suka Gaisa Sannan Yabiya kudin Hayar Lakadan Ba Ajalan Ba, Dan Mulki Ya Amsa Kudi Sannan Yace Su Shiga Yakara ganin wajen, Suka Shiga Suka Gani, Nan Yadau mukullan Dakunan Yabashi, Yayimai Godiya Yace Zaije Yadawo shida Matarshi Anjima Yace "Badamuwa", Sannan Yamai sallama yatafi....
Sai lokcin Yasamu Farinciki, Natsuwa Ta Ziyarceshi yayi Ajiyar Zuciya Kuma Yayi Hamdala Yagodema Ubangiji dayabashi Mafita Cikin lokaci iyalansa Basu Tagayyaraba.....
Isarsa gidan Abokin Nasa kenan, Yasa Sa Amai Sallama Da Uwargida Umma, Tafito Tasameshi, Da Fara'arta Suka Gaisa Tamai Sannu Da Dawowa, Sannan Yamata Bayanin Yanda Ake ciki, Aikuwa Tayi Murna Tamai Addu'ar Fatan Alkhairi Allah Ya Kara Horewa Ya Kara Rufamasu Asirin Zaman duniya Da Asirin Lahira...Nan Yace to Tashiga Tamasu Bayani, Ta Dauko Salahuddeen Sannan Suzo su Tafi Su Gyara Gidan Suyi Shara, Umma Tace "To", Haka Takoma Cikin Gidan Tayi yanda Abban Yace, Sai Gata Tafito tare da Salahuddeen, Nan Ya gaida Abban Nasa Suka Tafi Gidan Dan Mulki................
A Gidan Dan Mulki......................!
Don't 4get 2 Vote, Share & Comments 👏👏👏
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..