Zumunci ya kullu tsakanin umma da makotanta, kasancewarta mai farinjini cikin jama'a, ga iya mu'amala da hulɗa zakaninta da mutane, kowa tana bashi girma da darajarshi yanda yakamata, bata wulakanci ko kadan, kuma tanada tausayi da jin kai, gason taimakon wanda baidashi matukar ita tanadashi to zata dauka ta taimaki mabukaci a lokacin daya kama, don haka ake saurin sabo da ita duk inda ta zauna, don haka a unguwar kaya ma tasamu makota nagari suna mutunci da zumunci a tsakani......!
Umma macece mai tarbiyya, tsoron Allah da riko da addini, don haka tana koyama yaranta tarbiyya daidai yanda yakamata ayima 'ya'ya, wannan tasa yarantama sukayi fice, suka zama abin Kwatance, don ko cikin yara sun fita daban, don ko baka sansuba kagansu cikin yara sai ka tantancesu, yanayinsu, tarbiyyansu dama natsuwarsu tafita daban tamkar wata cikin taurari, akwaisu da shiga rai kowa yana sonsu ko cikin yara sa'o'insu, musamman maymunatu don akwai baki kuma ita tana sakewa ta fahimci muhallinta, sabanin shi salahuddeen shiru shiru mara son hayaniya, don haka bai cika magana ba ma,...........!
Akwai wani gida jikin nasu maymunatu ta bangaren hagu mai flat 3, flat na farko maman ummi ce aciki, matar limamin masallacin dake kofar gidansu maymunatu, tanada kishiya halima, sunada yara dayawa...
Sai flat na 2 maman yahya, inda take zaune da mijinta da yaranta 2 Deeni da yahya....
Flat na 3 kuwa umma ce da mijinta baba zakari kanin malam sani limamin masallacin anguwar da yaransa 2 abdurrahman da malam malam.................!
Sai wani gida daga ɓangaren dama shima mai flat 2, flat na farko maman rukayya ce uwargidan malam bala mijin maman abida datake dayan flat din gidansu maymunatu, tana da yara 2 rukayya da Hafsa.....
Daga gabas gaban masallaci, wani katon gidane ana cewa **Gidan Mr Rabe** gidan dogo mai tsaho sosai, flat kala kalane dauke da dogayen bishiyoyin kayan marmari kamar su mango, guava, orange, banana, umbrella da fulawoyi kala kala......
Gidan Wani Baturene dayazo daga Yankin Asia ya ƙera gida ginin turawa mai kyau yake zaune ciki da matar shi mai suna Suzan amma basu da yara ko daya, kuma kasancewar ya dade a unguwar tunba mutane don shi ne yafara gina gida ya tare don haka suke gaisawa da magidantar anguwan daidaiku amma ba kowaba, don bai shiga harkan mutane, kunsan baturen mutum da rashin son hayaniya ko jama'a...........!
Sai masallaci madaidaici da ƙatuwar bishiyar mangwaro a kusa da masallacin......
Sai kuma Titi daya fita har cikin gari wanda zai kaika wurare dayawa....
Ta bangaren Kudu kuwa wani katon dutsene kamar dutsen zuba na abuja wanda yake a jikin Naira 100... dutsen yaza yafito da anguwar, mutane baki na yawan zuwa wajen shakatawa musamman da yammaci, mutanene kala kala ke zuwan kan dutsen don yin Al'amuransu, misali: yan Shaye Shaye da yan daba suna zuwa suyi shagalinsu, haka yan makaranta student sukan je da littafansu suyi karatu musamman idan suna jarabawa, haka daliban makarantar hadda suna zuwa yin muraji'a ko yin haddan karatun Alkur'ani, haka yan sport ma suna zuwa suyi exercise duk yamma, su hau da gudu su sakko da gudu, haka yan hausa film ma suna zuwa shooting film a kan dutsen musamman idan rawa da waka za'ayi, yan anguwar kam suna ganin yan film don suna yawan zuwa....haka ma masu tsinkan fure da bama fulawa ruwa ba'a bar su a bayaba don masoyama suna zuwa su sha fira Suci soyayyarsu........
Duk fa wadannan rukunin mutanen dana jero kowa da lokacin zuwansa ko rana, idanma sun hadu dai waje da fadi kowa kama inda zai zauna a natse yakeyi ya Parker gefe ya basar yacigaba da harkokinsa, ba ruwan wani da wani, idan ka gama abunda Kakeyi saika tafi........
Daga kasa kusa da dutsen anguwar kayan kuma, akwai wata ƙatuwar bishiya mai yalwan rashina mai cikar ganyaye da fulawowi ya kawata wajen da inuwa, anzagaye jikin bishiyan daga kasa da block an siminteshi anyi dakalin zama, gefe kadan ginin makarantar primary ne kasancewar wajen akwai yalwan waje da fili mai tsaho, makarantar nada ginin ajujuwa masu yawa, da staff rooms, da headmaster's office, da student toilet, da playing ground, Kai makarantar ta hadu, sunanta **GOOSE GUIDE NURSERY & PRIMARY SCHOOL**, makarantar mallakin wasu mutanene su 2 da Mr Okafor da Mr Aminu, mutanen sierre leon ne, gudun hijira sukayo daga kasarsu, anyi juyin mulkine suka kiyin mubaya'a shine akeso a kashesu, Allah yabasu Sa'a da nasara suka fito kasar ta barauniyar hanya suka gudo, shine har Allah ya ƙaddara zamansu a garin na Maidugurin kuma suka zamu muhallin zama a unguwar kayan, shine fa har zama yayi zama suka nemi izinin mai anguwar suka gina makarantar, kasancewar da dinbin arzikin su suka taho ma'ana tarin dukiya....
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..