CIGABAN LABARI !
Bayan anyi sunan **Sadeeq**da kwana 2, Abdurrahman yafara rashin lafiya, nan hankalin iyalan malam muhammadun yatashi suka shiga damuwa, nan umma da abban yaran suka dukufa tofamai Addu'o'i, sanya karantun Alkur'ani, malam muhammadun yakawo ma umma man habbatussauda tashafamai don zazzabin jikin ya sauka, kasancewar al'adar malam muhammadun ne ba'a zuwa asibiti a gidan shi, sai dai ayi maganin musulunci, haka dai suketa fama jikin yayi zafi ya sauka.
Bayan kwana 2 jikin yayi tsanani da ciwo, ga wani farin abu daya fitomai a baki musamman kan harshensa, baya iya cin komai koda ruwane baya iya sha, sai dai umma ta dura mai saboda kada ya zauna baisa komai a cikin saba, ga ciwo idan babu cin abinci ai baza'a Warke da wuri ba, don haka take mai duren koko ko shayi ko kuma ruwa, sai kuka dayake yawaita yi koda yaushe, ga ciwon kai mai tsanani da zazzaɓi mai zafi, ranar kwana sukayi basuyi bacciba, don Abdurrahman fisge fisge ya dingayi yana zabura cikin daren, nan malam muhammadun ya zauna yanamai karatun Alkur'ani dakansa, sai gab da asuba suka samu jikin ya lafa har bacci ya daukeshi, umma ta kwantar dashi ta rufeshi kadan.
ALLAHU AKBAR! ALLAHU AKBAR!! ALLAHU AKBAR!!! A Safiyar ranar ne wacce tai daidai da kwana 11 da haihuwar Sadeeq, wajen karfe 10:00am, Allah yayima abdurrahman rasuwa, Ubangiji ya amshi kayansa, haqiqa rasuwar yaron ta taɓa zuciyar iyayen nasa dama mutanen Anguwar kayan makotan arziki, musamman maymunatu saboda bayan umman abdurrahman yafi sakuwa da yayar tasa maymunatu, kasancewar itace mai rainonsa Indai tana gidan, bayama yarda da umman wani lokaci, Indai maymunatu na nan a gida itace mamarshi ta 2..
Maymunatu taji mutuwar kaninnata, saboda tsananin shakuwar datayi dashi, a lokacin daya rasun, suna makarantar boko, kasancewar ranar ranar juma'a ce, yasa malam muhammadun yakira malam shehu yafadamai idan 12:00pm tayi yadauko su maymunatu yakawosu gida anyi rasuwa, Kaninsu abdurrahman ya rasu, malam shehu yace "to Malam, Allah yajikan rai" malam muhammadun yace "Ameen, nagode",.
Nan umma ta sanar da makotanta dasuke flat daya wato maman anas da maman abida, shima malam muhammadun yafita yaje gidan malam Muhammad Sani wato limamin masallacin Unguwar ya sanar dashi anmai rasuwa, malam muhammad yace " to tunda yau juma'a sai atafi ayi Sallan jana'izar a masallacin juma'a idan an Idar da sallan juma'ar", malam muhammadun yace "to Allah ya kaimu", nan sukayi sallama kowa yatafi.
Bayan liman yashiga gidane yake sanar da matarshi maman Ummi, nan yace ta shirya taje koda wani abu kuma tayima maman salahuddeen gaisuwa, tace "to, nan ta shirya tafita",
Maman ummince tayima abdurrahman wankan gawa ta shirya shi cikin likafanin da malam muhammadun yaje ya siyo, don umma bazata Iyaba tana cikin alhini da tashin hankali, nan suka zauna suna ta jimami, ana jira lokacin Sallan Juma'ar tayi a tafi masallaci da gawar.
Ita kuwa maymunatu tunda suka dawo suka iske rasuwar kanin nasu abdurrahman, ta ganshi kwance a Falo cikin makara an samai likafani ba rai, ta rikice taketa kukan fili dana zuci, amma ba ihu takeyiba, sai dai kaga kwalla wata na bin wata a fuskarta, sannan idanunta sunyi jawur dasu saboda tsaban kuka, ga wani zazzafan zazzaɓi daya rufeta nan take, shima salahuddeen kukan yakeyi, kuma shima idonsa yayi ja sosai, dukansu suna cikin tashin hankali, alhini da jimami, sai ajiyar zuciya kawai salahuddeen yakeyi, gani sukeyi rasuwar kamar a mafarki, domin suna tunawa sai da suka ganshi da safe Yanata kuka Kafin Sutafi, don sai da umma ta matsa musu sannan suka tafi don tausayama Kanin nasu ko Breakfast Kasa tsayawa sukayi suyi, haka suka tafi bayan umman ta zuba musu abincin a lunch box, to dasuka dawo suka tarar da rasuwan sai suka shiga tashin hankali sosai, yanzu haka ko Uniform salahuddeen da maymunatu sun kasa cirewa don ba natsuwa a tare dasu.
Ko ruwa ba wanda ya iya sha cikin maymunatu da salahuddeen, balle batun cin abinci, kowansu rakubewa yayi gefe yana shashshekar kuka, sun kasa yima kowa magana.
Wajen karfe 1:00pm na rana, malam muhammadun da limamin Unguwar, da sauran mazan Unguwar suma, dama kusan haduwa sukeyi su tafi masallacin juma'a tare, sai dai wanda baya unguwar lokacin, don haka yanzuma suka dunguma suka dau gawar abdurrahman suka tafi sai masallacin juma'ar kofar doka wato **Ni'imat Juma'at Mosque**, bayan sun isane suka sanar da hukumar masallacin akwai sallan jana'izan daza'ayi idan an Idar da sallan.
Bayan Idar da sallan juma'ar ne liman ya amsa loudspeaker ya sanar, mutane su tsaya za'ayi sallan gawa anyi rasuwa, don haka mutane suka tsattsaya, akayi Sallan jana'iza, akayi Addu'o'i, dama akwai makabarta batada nisa daga masallaci, don haka a kafa aka dau gawa aka dunguma sai makabarta, nan aka haka kabari shaqqu, aka binne Abdurrahman, sai dai muce Allah yasa mai cetone, kasancewar ruwaya tazo a cikin Hadisi cewar "duk yaron daya rasu baikai lokacin da alkalami yahau kansaba, to zai kasance cikin makarantar Annabi Ibrahim a lahira, kuma zai ceci iyayensa", wallahu ta'ala A'alam, niba malamabace Allah ya yafemin idan nayi kuskure.
Ita kuwa maymunatu da kawarta Ummi da salahuddeen suna kofar gida tunda aka fito da gawar abdurrahman za'a tafi masallaci, suna tsaye kan dakalin kofar gidan kusa da gate din garage din dake flat din su maymunatu, har lokacin kuka maymunatu da salahuddeen sukeyi, kwalla wata na bin wata a fuskokinsu, ummi kuwa nata aikin rarrashinsu da basu hakurin cewar, su dena kuka addu'a zasumai.
Suna nan tsaye har yan masallaci suka dawo daga masallaci, malam muhammadun ne ya hangosu nan inda ya barsu, kiran su yayi yace sukoma cikin gidan su cire Uniform su Zauna, nan suka amsa suka shiga cikin gidan dukansu.
Bayan sun shiga sun samu waje a falon sun zauna, Ummi dai kara basu hakuri takeyi tana rarrashinsu, amma tana matukar tausayamusu sosai, da kyar maymunatu ta iya daina zubar da hawayen ta koma kukan zuci, salahuddeen kuwa sai ajiyan zuciya da numfashi yakeyi kawai.
Bacci barawo, amma ranar badai a gidan iyalan malam muhammadun ba, don duk wayo da dabaran bacci yakasa nasaran koda sace mutum daya daga cikinsu, don hata jariri sadeeq dan kwana 11 yasan anyi rasuwa, don shima rigima da kuka ya wuni yi har daren, kuma har shi baiyi bacciba sai chan wajen karfe 2 na dare, Yasamu yayi Baccin, amma sauran ahalin gidan kuwa babu wanda ya runtsa don kwana sukayi sallah da karatun Alqur'ani suna rokon ALLAH yajikan Abdurrahman yasa mai cetonsune, Sannan yabasu hakurin jure rashinsa.
Shekaran Sadeeq daya da rabi amma baya tafiya don ko rarrafe baya iyawa, kasancewar yayi nauyin kafa ne, iyayen kuwa duk sun damu, amma dai sukacigaba da mai addu'a, musamman umman datafi damuwa sosai, daga zama sai zama yakeyi, idan Zatayi aiki kuwa akwai kujerar yara datake zaunar dashi har tagama aikinta sannan ta daukeshi, kwatsam rannan data ajiyeshi tana kitchen Tana girki, sai jiyoshi tayi ya tsandara wani uban kuka, ai da gudu tafito daga kitchen din ta nufi wajensa, nan ta tarar ashe fadowa yayi daga kan kujeran tamkar an jehosa, nan tadagasa ai sai taga bakinsa ya fashe yana jini, kuma sai razana yakeyi yana fisge fisge, nan ta shiga karantomai Addu'o'i tana tofamai, amma yaro bai natsuba, nan dai taga abu na neman yafi karfinta, ta dau waya ta sanar da malam muhammadun, aikuwa cikin mintuna 20 sai gashi yashiga gidan da sallama, nan yaga abun da Sadeeq din yakeyi, aikuwa yayi saurin dauro alwala, ya shinfida daddumar Sallah ya amsa Sadeeq din ya rikeshi a hannu yayi bismilla yafara mai karatun Alkur'ani a kunnen dama, sannan ya mikoma umma ruwan zamzam yace ta zuba a kofi, ta tofa addu'o'i ta fara shafa mai a jikinsa gaba daya, nan ta amsa tayi yanda yace, sannan ta koma Kitchen don karasa girkin data bari kan risho kafin yakarasa yima Sadeeq din karatun.
Bayan tagama tafito daga kitchen din tadawo gurin Abban Yaran da Sadeeq, bayan wasu mintuna ya kammala karatun dayake masa, sannan ya juyo yacema umma yayi bacci don haka taje ta kwantar dashi, idan ya tashi tamai wanka tabashi abinci yaci, kuma ta shafamai man habbatussauda idan tayi addu'o'in aciki, kuma Aljanune suka bigeshi shine sanadin fadowarsa daga kan kujeran, nan tashiga al'ajabi da damuwa, tashin hankali ya bayyana ƙarara a fuskanta, nan malam muhammadun yace "karta damu, In sha Allah zai samu sauki da wuri, karya damu tamai addu'a kawai, nan ta amsa da to, sannan yamata sallama yace ya koma shago, ita kuma tacigaba da harkokin ta cikin damuwa da tunani a zuciyarta.
Turkashi to ga dai rasuwar abdurrahman, kuma ga rashin lafiyar Sadeeq, ko ya Iyalan malam muhammadun zasu tsinci rayuwa a gaba, koya maymunatu da salahuddeen Sukaji da kewa da tunanin Kanin nasu ???
Kuma mai zai faru nan gaba ?
Ku biyoni a next chapter Dina....
Comments dinku is highly needed my lovely fans. Ana mugun tare.
Taku Har Kullum
Maymunatu AbubakarDon't 4get 2 Vote, Share & Comments
Love You All And Always
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..