Chapter 23

16 2 0
                                    

Bayan shekara da haihuwar umma itama asabe ta haifi diyarta mace, yan gidansu nata zuwa yimata Barka don bata tafi wankan gida ba.

Ran suna kuwa akasama yarinya **Aishatu**,duk da malam muhammadun baya taran suna, amma asabe ta kekasa kasa tace wallahi sai tayi taron suna, don abun gorine gareta cikin 'yan uwanta ace haihuwar farko batayi taron sunaba, yace shi dai ba ruwansa, bazai tanadi komai na abincin dazasuci ba, tace ita dai saitayi, haka dai ya shirya yatafi shagon sana'arsa..

Aikuwa yana fita mutane suka fara hallarowa, kaman daman jira suke malam muhammadun yafita, nan ta shiga Kitchen ta diba komai dazasu bukata na girki suka girka abincin sunan su, dama sun taho da zobo da jinja da kunu daga gidansu.

Suka Sha Taron Sunansu sai yamma mutane suka watse, suka bar kannanta su hasana, murja da hadiza, sukam dama kwana zasuyi a wajen yar tasu asabe.

Da dare kuwa malam muhammadun yadawo, nan ya tatar da barnan kayan abincin da amarya asabe tayi da kayan abincinsa, dama yasan ba lallai ta hakuraba, shiyasa yana dawowa yatafi Kitchen ya duba, aikuwa yaga abunda yake tsammanin yafaru, amma saboda kin gaskiya da rashin adalci, maimakon yama amarya asabe fada tunda itace tayi laifi, sai yatafi dakin umma yana yimata fada wai "meyasa tabar asabe ta dibar mai kayan abinci sukayi girkin suna?" Aikuwa tace ita ina ruwanta, ai bece ta diba ta ajiyeba, kuma baice idan asabe zata diba ta hanataba, kuma meyasa dazai fita shi bai diba ya boyeba yanda bazata diba ba koda bayanan, don haka yaje yama asaben fada ba Itaba, nan dai yakaraci fadan rashin gaskiyarsa yafita.

Idan maye ya manta ai uwar 'ya bazata manta ba, bayan kwana 2 sai umma batayi girki ranar ba, tunda taga tayi sati 2 don haka Asabe ce zata karbi girki kamar yanda suka tsara sanda Umman ta haihu kwanakin baya, amma sai asaben taki yin girki.

Bayan malam muhammadun yadawo karfe 9pm, nan yayi wanka yasa kayan bacci yafito ya zauna a falon, nan ya bukaci umma ta kawomai abincinsa, tace " ai girkin asabe ne don yau sati 2 da haihuwar ta", nan ya tashi yatafi dakin asaben, yake tambayarsa ina abincinsa, tace "a'a maman fatima bata bakabane?, Yace "eh tace girkinkine banataba" asabe tace " to aini bansaniba, don haka banyiba",

Ran malam muhammadun yafara ɓaci iya matuqa, yafara cewa " wai mekuke nufi dani ne?, naje tace girkinkine, nazo kince girkintane bakiyiba, to ya kukeso nayi?, asabe tace "to nidai banyiba", malam muhammadun yace ma asabe, "tasameshi falo" sannan yafita zuwa dakin umma, itama yacemata "tasameshi a falo", nan yakoma falon yana jiransu.

Bayan dukansu sun isa falon sun zauna, yafara magana, yanzu su fadamasa wacece da girki? umma tace "ita dai ba ita bace da girki don yau sati 2 da haihuwar asaben, don haka asaben ce zata amsa girki kamar yanda suka tsara tun farko",

Ita kuwa asabe tace "tabdi, Allah ya kashe ya raya kuwa bazata girki ba, don batada lafiyan dafa abinci, sai dai Umman ta amsa girki zuwa nayi 40, idan nayi kwana 40 nasamu lafiya sai na amsa.

Nan malam muhammadun yace to umma kece babba, kuma kinga batada lafiya, sai ki amsa girki kicigaba kafin tayi 40 tasamu sauki.

Umma kuwa cewa tayi bazatayi girkiba, tunda ai yarjejeniya sukayi, kuma ita asaben ne tace kota haihu kar tayimata girkin bayan sati biyun, don haka tashi ma tayi tabar musu falon, tayi shigewarta dakin nata.

Kasancewar ranar daren larabace za'a wayi gari alhamis, shiyasa umman ta tashi karfe 3:00am tayi Qiyamul Laili, tayi Addu'o'i sannan karfe 4:00am tatafi kitchen don hada abinda zatayi sahur dashi, tana cikin hada Tea malam muhammadun ya sameta a cikin madafin, yace tahado komai na sahur din dashi,tace "to".


Nan tahado Tea ta dumamo ragowar jallof din shinkafar data dafa musu da daren sukaci da ita da yara, ta kawo falo suka zauna sukayi sahur din, amma fa babu maiyima wani magana acikinsu, suka gama ta kwashe komai takai kitchen ta nufi Ɗakinta don yin sallan asuba saboda anfara kiraye kirayen assalatu, shima malam muhammadun yakoma dakin asaben.

Hajia umma baiwar Allah mai tsananin biyayyar aure, haka taci kukanta, ta roki Allah yakawo mata dauki da agaji akan matsalolinta da damuwarta.

Washegari kuwa tayi shirin cigaba da girkin har kwana 40 din, haka dai rayuwar gidan malam muhammadun tacigaba da gudana, babu wata zamantakewa mai kyau tsakanin iyalan nasa.

Yayinda Umman take gudun magana, ita kuwa asabe sai jan magana, tsula rashin mutunci, da hada fadan babu gaira babu dalili, shikuwa uban gayyar ya karkata bangaren hamshaqiya amarya asabe, sai abunda tace za'ayi acikin gidan.


Umma tayi girkin Ragowar sati 2 yakai kwana 40 din, sannan amarya asabe ta amsa girki.

Ran da amarya asaben tacika kwana 40 din, tun safe ta shirya tayi sammako tatafi gidansu yawon arba'in zata je gidajen 'yan uwanta, sai yamma liqis ta dawo ta daura musu girkin dare.

Haka lamura suka cigaba da gudana, kwanaki nata tafiya, watanni na Shudewa, shekara na zuwa su wuce tamkar ana yanzu da hanzari.

Gaskiya asabe kazamace ba'a magana, kasancewar tana jegon 'yarta A'isha, idan safiya tayi tafito da kayan fitsari yarinya bazata wankeba, sai dai tajikasu tatafi makarantar Imamu, idan ma tadawo bazata bi takansuba balle ta wanke sai dai tayi haramar daura girki, sai yamma liqis zata wanke ta shanya, sanda zatayima aishar shinfida da dare kayan basu bushe ba, kasancewar ba'a wanke an shanya da wuriba, idan ka taba da sauran danshi, amma don rashin tausayi da imani da rashin kula da lafiyar yarinyarta haka zata dauka tamata shinfida ta kwantar da ita ahaka, sannan bata gama abinci da wuri, amma ko karfe nawa na dare tagama to saita tashi aishar tabata abinci taci, sannan zata kara kwantar da ita.

Abunda yasa bata dawowa da wuri kuwa shine: idan suka tashi daga makarantar Imamu, saita biya shagon malam muhammadun ta kusan wuni a Chan, dama kunsan tasaba zuwa ta dade tun kafin ya aurenta sanda tana kai tallah, don haka yanzuma tacigaba da zuwa, kuma Chan take bata lokaci, don tun 12:30pm ake tashi amma idan tabiya shagon sai karfe 3:00pm ko 4:00pm idan anyi la'asar take komawa gidan idan itace da girki, idan kuwa akayi sa'a ba itace da girkiba, to sai an ganta, sai dai idan ranar da tasan zatayi baki shine zata dawo da wuri.

Abunka da yara baka hanasu wasa a tsakaninsu, don haka aishar nason zuwa bangaren umman tunda tafara rarrafe don tana ganin fadimatu don tayimata wasa, duk da fadimatun ta girmeta da shekara, amma sai kaga asaben tazo ta janyeta tanata fada, ita kuwa yarinya ma batasan me ake cikiba, idan umma tama asaben maganar don me zata hana aishar wasa da 'yar uwarta fadimatun? Sai tace ina ruwan Umman, ai 'yartace ita tasan zafin haihuwar abarta, don haka ba ruwan umman koma mezata ma aishar, umma kuwa sai dai tace "Allah ya kyauta kawai".


Yau kam iyalan gidan malam muhammadun suna cike da farinciki kasancewar zasuyi.......

Kubiyoni a next page dina don Jin maize faru? Kuma wace wainar za'a toya ??

Taku Har Kullum
Maymunatu Abubakar

Don't 4get 2 Vote, Share & Comments

Love You All My Fans
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now