Garin Maiduguri............!
Yauce Takama Lahadi Ranar Karshen Mako, Kuma Ranarne Malam Muhammadu Yake Komawa Maidugurin Makaranta, Don Haka Tare Zasu Tafi, Sun Gama Shirinsu Tsab Tun Asuba, Don Tun Dare Sukama kowa Sallama, Asubar Fari Suka Kama Hanya Sai Garin Na Maiduguri, Dama Abba Yayi Shatan Motar Dazata Debesu da Kayansu, Kasancewar Kayan Nasu Bamasu yawabane sosai, Daga Kayan Amfanin Kitchen Muhimmai Na Amfanin kullum Sai Katifunsu Da Kayan Sawarsu, Su tabarmi, Da Kayan Shimfida Da Kayan Aikin Gida Na Umman wanda Zasu Bukata, Sauran Kayan Gado, Da Kujeru Dama Sauran Kayan Kitchen din Umman Barinsu A Kanon Sukayi Don Bazasu iya Daukansu A Lokacinba....
Tafiyan Ma Daga Umma Sai Abba Sai Salahuddeen, Aka Tafi Maidugurin, Itakuwa Maymunatu Anbarta A Wajen Kakarta Gogal, Tace Bazasu Tafi Dukaba A Barmata Takwaranta Daga Baya Takoma Maidugurin, Haka Kuwa Akayi Suka Tafi Suka Barta A 'Yankaba Cikin Karin Na Kano Suka Nufi Maidugurin.......
Isarsu keda Wuya Suka Wuce Anguwar G.R.A Dake Cikin Maidugurin, Gidan Alhaji Sunusi Abokin Nashi Dazasu Zauna Gidansa, Suka Sauke Kayansu, Sukaga Yara a Kofar Gidan Don Haka Malam Muhammadu Ya bukaci dasu Tayashi Shigar Da Kayan, Nan Suka Tayashi Kwasa suna Shiga Dashi, Dasuka Gama Ne Ya Dan basu Hassafin kudi Yace Suje su Raba, kuma Ya gode, Suma Sukace " Mungode ",.......
Sannan Sukayi Sallama Cikin Gidan, Flate Din Malam Sanusin, Inda Aunty Zinah Ta Amsa Sallamar Tasu, Tayi Masu Izinin Shiga Falon Nasu, Nan Aka Gaggaisa, Kasancewar Tasan Malam Muhammadun Saboda Abokin Mijintane, Kuma Yana Zuwa Gidan Cin Abinci Time To Time, Ko kuma Idan Yaje Wajen Abokin Nasa don su Tattauna Wasu Batutuwa Nasu, Nan Ta Kawo Musu Abincin Data Girka Musu Tunda Tasan Da Zuwan Nasu, Mijinta Yafadamata, Nan Tabasu Wuri Su Sake Sosai, Sukaci Suka Koshi Suka sha Ruwa, Kuma Sukayi Hamdala, Bayan Sun Kara Hutawane, Suka Bukaci Komawa Boys Quaters din Don Fara Gyara Kayansu Da Jera Komai A Muhallinsa,.......
Haka Kuwa Akayi Suka Gyara Ko Ina Kal kal Umma Ta Share kara Share Dakunan Da Falon Da Varander, Duk Da Aunty Zinah tasa Masuyi Mata Aiki sunyi Sharan Yana, Sun share Sun Wanke Dakunan, Tun Kafin Suzo, Bayan Umman Ta Kara Share ko'ina Sai Ta Kunna Turaren Wuta, Dakin Ya Dau Haramin Qamshi Mai Dadi.....Sannan Sukayi Wanka Suka Rage Gajiyan Tafiya Data Gyara Kaya, Shiko Salahuddeen Yana Zaune Yana Kallonsu, Don Shi Yarone Bamai Son Hayaniyaba, Baicika Wasaba, Balle Da Ba 'Yar Uwarshi Maymunatu Yayi Kewarta Sosai Wlh, Shiyasa Ma Walwalarshi Ta Ragu, Shiyasama Yakasa Zuwa Suyi Wasa Da Yaran Aunty Zinah Abba Da Intisar, Nan Ya Zauna Shikadai Abunsa...
Haka Rayuwa Tacigaba Kadaran Kadahan Cikin Rufin Asiri, Yau Da Shi Wadatacce, Gobe Babu Sai Maleji,, Maymunatu Kuwa Na Chan Kano Wajen Kakarta, Yanzu Salahuddeen Da Iyayen Maymunatu Har Sun Fara Sabawa Da Rashin Ta................ ...
Bayan Shekaru 2 Ne Sai Aka Maida Barrister Sunusi Aiki A Federal High Court Dake Garin Abuja, Inda Zaiyi Parking Yakoma Abujan Da Zama,..............
Haka Dai Cikin Damuwa Malam Sunusin, Yasamu Malam Muhammadu Ya Labartamai Abunda Ke Faruwa Da Halin Da Ake Ciki, Nan Jikin Malam Muhammadun Yayi Sanyi, Don Yanzu Baisan ya Zai Yiba Akan Maganar Inda Zasu Koma Shida Iyalansa, Tunda Maigidan Zai Tashi kuma Dama Shima Haya Yakeyi, Ai Dole Shima Malam Muhammadu Sutashi, Gashi Babu 'Yan Kudi Hannunsa, kuma Bai Fara Wata Sana'ar Ba, Karatun Kawai Yakeyi, Sai Yan Buga Buganshi Cikin Gari, Abunda Yasamu Yakawoma Umma Ta Sarrafa, Kuma Malam Sanusi Shike Basu Abinci Dama Wasu Abubuwan Bukatun Rayuwar Yau Da Kullum, Sai Dan Abinda Ba,'a Rasaba Na Sauran 'Yan bukatunsu Wanda Dole Malam Muhammadu Yayi,..........
Nan Malam Muhammadu Yatafi Cikin Campus Hayan Gida, Kasancewar Bashi da Kudin Dazai kama Haya A cikin Gari, Cikin Campus Kuwa Ma'aikatan Gidajen Quaters din cikin makarantar Suna Iya Bada Hayan Wasu Dakuna Daga cikin Gidajen Nasu Da Gwamnati Ta Basu su Zauna, Sai Susa Haya Suna Amsar kudi, Matukar Akwai Ragowar Daki idan Iyalan gidan Basuda Yawa, Shiyasa Shima Malam Muhammadu ya Shiga Cikin Quaters din binciken ko Zai Samu Hayan Dakuna Ko 2 Sukoma Da Zama Kafin Yasamu iko da yalwar Kama Musu Wani gidan Hayan idan Yasamu Kudi.............
Yanata Nema A Karshe Da Kyar Dai Yasamu Wani Gida,Inda Mai Gidan, Zai Bashi Hayar Sitting Room Sumaidashi Bedroom Sufinga Bacci Aciki, Da Wani Daki Daga Gefe Karami Guda Daya, Sai Toilet A Tsakar Gida, Da 'Yar Varander, Gaba Kadan Sai Kofar Fita Gidan....
Sai Dai Har Yanzu Sun Kasa Daidaitawa Da Mai Gidan Kan Kudin Hayar Gidan, Inda Mai Gidan Dan Mulki Yaki Rage Kudin Hayar kamar Yanda Malam Muhammadu ya Roka Kasancewar Bashi da Kudin Ne, Amma Sam Dan Mulki Yaki yi Musu Ragi ko lamunin Ya Amsa Kudin Nasu duk Da Basu Cikaba, Idan Yasamu Ya cikamai Daga Baya, Amma Sam Bawan Allah Nan Yaki, Gashi Malam Muhammadu Yabuga Yabuga Bai Samu Cikon kudin Hayar Ba, A Lokacin Duniya Na Kwance Kudi Akwai Albarka, Kudin Hayar Ma Dubu 6 ne, kuma Malam Muhammadu Yanada Dubu 4, Dubu Hudun Ma Dayake Dasu, Ragowar Kudin Da Abokinsa Malam Sunusi Yabashi ne, Sai Yafara Biyan Kudin Makarantar Shi, To Ragowarne Ya Rike Yake Neman Hayan Dasu, To Gashima Bazasu isaba,..
Barrister Sunusi Kuwa..........................!
Taku Har kullum
Maymunatu Abubakar
Love You My Fans 👌Don't 4get 2 Vote, Share & Comments 🤝🤝🤝
YOU ARE READING
RAYUWAR MAYMUNATU
General FictionThe Novel Is All About The Life Of A Decent And Innocent Girl Maymunatu, She Experience Many Challenges, Which Make Her Acquire Knowledge And Many Skill In Her Life, Which Also Make Her, Educated, Talented And Wanted In The Society..