Chapter 33

29 1 0
                                    

Washegari maymunatu ta tashi kafar ta kara kumbura ko takawa bata iyayi da kafar daman, gashi jikinta duk ciwo yakeyi mata, haka dai salahuddeen kadai aka kai school ranar, Maymunatu kuwa babu damar zuwa don haka zaman gida yakamata bata shiryaba, gashi suna 3rd term ne, har aka kusan fara jarabawa sannan Maymunatu tasamu saukin kafar ta, tafara zuwa school da sati 1 aka fara exams, haka tayi jarabawa, sai gashi batayi kokariba, maymunatu tashiga damuwa, har kuka sai datayi, masu jin dadin batayi kokari ba wannan Karan ba sunata murna.


Haka dai ta Shiga primary 6, sukayi 1st term suka Kammala sukayi hutu, hutu yakara suka koma 2nd term, bayan anyi rabin term ne aka shirya class Quiz, malamarsu Mrs Abdurrashid ce ta shirya, maza group A, mata group B, akayi Quiz group B sukaci, maza natajin haushi mata sunyi winning.


Kasancewar Maymunatu sune manya a school din, wato yan primary 6, idan za'a fita school taje wani program to su ake turawa, kuma maymunatu nacikin wanda ake zaba saboda kokarinta, hakama idan za'aje Quiz su suke zuwa itada sauran top students kamar Ahmad I Ahmad, Rosemary Oghunba, Fatima Ahmad, Usman A Ladan, da John Obeche, kuma idan Sukaje to suke cinye sauran schools, domin 1st position sukeyi a kowane irin competition, haka zasu dawo da gifts masu yawa, school ma ta sake raba masu gift na musamman.


Haka company din indomie suka kawo musu ziyara, sukace maths competition zasu hada su zabi best 3 students, zasuba kowane 3 students din gift, Suba school ma award, akayi competition cikin nishadi, Maymunatu ce tazo 1st position aka bata gift din indomie 3 carton, da exercise books and pencils, Rosemary ce tayi 2nd position, aka bata indomie 2 carton, da exercise books and pencils, Ahmad I Ahmad ne yayi 3rd position, aka bashi indomie 1 carton, exercise books and pencils, school kuma suka basu katon first aid box wanda yake da dukkan kayan bukatan treatment mai tambarin indomie company, harda calendar da memo na indomie, sai biro da marker duk na indomie company, students nata rera waka " indomie is good for you 'iya 'iya woo "! haka sukayi sallama da school headmaster suka tafi.


Gabda zasu fara exams din 2nd term ne aka sale shirya wani English competition din, wannan time din harda wani school din za'ayi wato Basic secondary school dake tudun wada, kuma 'yan staff school din ne zasuje Basic school din, dalibai 2 aka zaba, mata 2 maza 2, suka shirya suka tafi tareda rakiyar headmaster Alhaji Gimba Alfa, da Mrs Okunye, da Malam Abdullahi, a school bus suka tafi, driver malam habu ne yajasu yakaisu, makarantu 4 ne zasu fafata a English competition din, staff school, basic secondary school, great icon international school, sai merit academy school.


Akayi competition cikin natsuwa da tsari, anata farinciki aka kammala, Inda staff school sukazo 1st, sai Basic school sukazo 2nd, Merit Academy sukazo 3rd, sannan Great icon international sukazo 4th position, don haka Staff school da Basic secondary school ne akabama gift din 1st and 2nd, sukayi sallama kowa yakoma school dinsu da murna.


Haka akayi har suka har su Maymunatu suka zana common entrance exams, suka kammala primary 6, new session na zagayowa aka samama Maymunatu gurbin shiga Jss 1 a Demonstration secondary school dake cikin unimaid campus din, tasamu shifa JSS 1A, yayinda salahuddeen yashiga primary 6 a lokacin.


Maymunatu tafara.........?

Sorry a short Chapter

But To be continued

Koya rayuwar Maymunatu a makarantar gaba da primary Zata kasance ???

Shin ya batun kokarinta, ko Zata cigaba da kokari kamar da, kunsan an shiga level nagaba Wanda yafi karatun primary ???

Kubiyoni a next update Dina don jin yazata kasance ???


Taku Har Kullum
Admin Maymunatu
Garkuwar Mata Marubuciyar Al'umma

Don't 4get 2 Vote, Share & Comment

Ina Alfahari da Ku Masoya Na
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Allah Yabar Zuminci
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

RAYUWAR MAYMUNATUWhere stories live. Discover now