💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖
💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖
ADAMAWA JIMEITA LOCAL GOVT AREAHaba Fateema maisa kike son bani wahala neh, fisabilillahi ana zaune kalau kawai sai ki hanani ganinki ai baki kyauta min ba kinsan yadda zuciyata take min radadi saboda rashin ganinki da banyi ba, Allah sarki habibina wallahi bahaka bane nace maka baffana baya son yawan fita neh, kuma na gaya ma idan da gaske kake kana sona why not ka iso gidanmu ka nima izinin baffana tunda daddy ya koma Canada, ajiyar zuciya yayi sannan yace Fateema na gaya miki matsalata but baki gane ba, haba masoyina ya za’ayi kacee ban gane ba, wallahi na gane amma na gayama wannan ba matsala bace baffa will understand and daddy mah yana son abinda nake bazai yi questioning dinka dayawa ba, haka kike gani, okay nextweek yayana zai dawo daga Abuja don yaje ganin wata sister din daddy dinmu, nima saboda kai ne banje ba don bana so nayi missing dinka, kuma anty dina ma tana ta complaining wai mai sa ba azo dani ba, da kyar yaya ya bata hakuri yace idan zai kara zuwa tare zamu zo, saboda haka ka gane na damu da kai sosai, saboda zuciyata tayi mumunar kamu da soyayyarka a farat daya, uhmmmm Fateema nema haka nake ji cikin zuciyata nafiso ace kullum ina tare dake…….
Fateema na’am ta amsa kiran da ake mata atsakar gida, kaga bari naje goggo na kirana zamuyi waya anjima koh. Sosai mah kuwa, sai anjima my dear.okay ta fada sannan ta kashe wayar.
SOKOTO
Kai ya bobby wallahi ni kadai na bana so, dariya yayi sannan yace ai mudin baki daina kirana da wani yaya bobby ba nima bazan daina ba, nifa ba yayanki bane yanxu ni husband neh yanxu, dariya tayi ta rufe fuska, kai kai wallahi ni ki daina jin kunyata ai ni zaki cuta, ni wallahi kunya kake bani, uhmmm nasan cewa kike azuciyarki daman wannan bawan Allah ya iya surutu haka, toh ki sani sonki yasa na koya hayaniya, dariya tayi kawai, sannan ya kara cewa yau dai ana min rowan magana kenan,a’a wallahi ni ba rowa nake ma ba, okay tunda kince haka barin gyara kwanciya naji labari, dariya tayi sannan tace yayana kenan murtuke fuska yayi, dariya tayi sannan tace barin baka wani labari mai dadi,ko kallonta baiyi ba,shi adole yayi fushi,murmushi tayi sannan ta cigaba da Magana, akwai wani saurayi yana matukar burge ni, da sauri ya juyo sannan ya zare ido, dariyar da take kunshewa ne ya kusa kufcewa amma ta danne, sannan ta cigaba wallahi yayana idan ka gnshi koh kaima sai yayi ma, yana da kyau sosai sannan,kafin ta karasa kawai taji ya kashe wayar, dariyarce ta kufce mata sai da tayi mai isarta sannan ta kara kiransa video call amma bai dauka ba,said a ta kira sau uku amma yaki daukawa, murmushi tayi sannan ta rubuta mai text kamar haka; haba ya ban gama baka labari ba zaka wani kashe min waya, duk da haka zan dai baka labarin, yauwa kamar yadda na gayama kyakyyawa neh son kowa kin wanda ya rasa, tun lokacin da na fara ganin shi zuciyata ta kasa sukuni na rasa abin da ke min dadi arayuwata,idan ban gansa ba bana jin dadi kwata kwata, harya kai lokacin da na fara rasa natsuwa ta, amma fa bazan gaya ma waye ba sai kayi picking call dina. Tana kai nan ta tura mai, bayan minti biyu ta kira amma sai yayi rejecting sai ga call dinsa ya shigo, hello ta fada amma shiru bai amsa ba, okay tunda baza kayi Magana ba sai na bari idan ka shirya,zata kasha wayar taji murya chan kasa ana fadar inajinki fa, na’am tace kamar bata jiba, gyarar murya yayi sannan yace waye wannan ya fada adakile, dariya tayi marasa sauti saboda ba ganinta yake ba, sunansa daya da kai sunansa Muhammad ,shine habibina muradin raina,diff ta ji an kasha wayar,dariya ta kwashe dashi, noor tace kiyi hakuri ki daina wahalar da kanina, anty noor barni dashi dai,nima fa na wahala wallahi ya noor koh kallona bayayi idan yazo gida,idan ana fira na sako baki sai yayi shiru kamar makiyarsa, na azabtu sosai, ni dai wallahi yana tambayata zan gaya mai cewar elham, ba tare dani za aba ya bob dina wahala ba, ai bawan Allah nan ya azabtu koh, haba wata biyar kina mai yawo da hankali anya kina da imani kuwa, dariya noor tayi sannan tace ita kuma ta shekara biyu tana dakon soyayyarsa, wayar elham neh ya katse musu ja’injan nasu, yauwa dan halas ka ki Ambato, sallama tayi bayan ta amsa kiran, yayana ka wuni lafiya kuwa, pls baby kiyi ma kawarki Magana wallahi na kusa kamuwa da hawan jini, ya bob ka daina kishi fa da kanka wallahi husna babu wanda take so face kai, duka husna ta kwada mata abaya, kambu wallahi ko zaki Burma min baya sai na fada, haba ai ya isa haka horon, bobby da bai gane maganarsu ba yace please elham explain ban gane ba, nan elham ta war ware mai zare da abawa, murmushi yayi sosai harda sujudil shukur, kai amma nagode kice mata ina nan zuwa gobe sannan ki fita harkanta don nasanta sosai yau kwanan fushinki zatayi,yayana ka barni da ita ni ne daidai ita ai, harara husna ta banko mata sannan ta tashi zata fita a dakin.
Da dai kin dawo saboda duk idan kika je sai na biki, haba kanwata yi mata ahankali please bobby yace,okay yayana bari na je na lallashe toh, yauwa koh kefa, toh yaya sai anjima.
YOU ARE READING
Mafarkinsa Nake 💞💞💞
RomanceNi wallahi kullum sai nayi mafarkinsa amma bana ganin fuskarsa, kullum ce min yake ni yake so amma yaki nuna min fuskarsa na gani wai sai rannan da nace ina sonsa kafin zai bayyana min kansa. Ni kuma tsoro nake kar nje na gaya ma aljani ina sonsa n...