🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
Fitowa take daga airport tana jan jakarta hannunta rike da hangbag dinta da waya,kalle kalle take idan zata hango mamy,ji tayi ta bige mutum wayar hannunta ya fadi kasa,Ooops my baby,tayi fuskar tausayi sannan ta tsuguna ta dauki wayar,tana dagowa taga screen dinta duk ya farfashe duk da screen guard din,daga kai tayi ta kalle mutum da ya tsaya kamar kungi yana kallonta,waving hannunta tayi afuskarsa sannan tace bawan Allah lafiya,ajiyar zuciya yayi sannan yace mata Dan Allah kiyi hakuri ina sauri neh zan kama flight dina zuwa lagos in the next twenty minutes kwata kwata ban ganki ba,murmushi tayi sannan tace babu damuwa kayi sauri karka rasa flight din,murmushi ya mayar da mata sannan yace,okay toh thank you ,har ya kama hanya zai wuce ita kuma ta tsaya saka wayar cikin jakarta ta fito da karamar don kiran mamy,Baiwar Allah baki gaya min sunanki ba sannan dan Allah ko zaki iya ban number dinki,kallonsa tayi nah kusan second ashiri ba tace komai ba tana nazarinsa kafin tace sunana rahma,sannan ta basa number dinta,cewa yayi ya gode tare da gaya mata sunansa ismail,kafin ya wuce yana sauri sauri kallonsa tayi sannan tayi dariya tace bari dai kaje ka karya kafa,juyawar da za tayi kawai sai taga mutum agabanta,ba karamin tsorata tayi ba,jikinta duk akame yake,dariya ya fashe dashi,ita koh ahankali ta fara bude ido ta zuba su akan fuskarsa,tsaki tayi sannan tayi ajiyar zuciya kafin tace wallahi sai na gaya ka da mamy,dariya ya rinka mata suna tafiya yana jan jakarta,daman wani iyayi yasa ka wani zo daukata ta kara fada tana murguda baki,dariya yayi sannan yace nah you sabi,data ga ya mayar da ita mahaukaciya ma banza dashi tayi sannan ta cigaba da danna wayarta,msg ta gani daga unknown number,shiga tayi taga wasika aka turo mata kamar haka....
Salama alaikum yake maabociya kyau,naso da ba a irin wannan circumtance din muka hadu ba,but naji dadin dana same ki da saukin kai,sannan ina fatan zaki bani daman sake ganinki da kuma saninki sosai.
.........Ismail turaki........Murmushi tayi sannan ta girgiza kai kawai,kallonta mukhtar yayi sannan yace yadai,banza dashi tayi don har yanxu haushinsa take ji,wayarta neh ya fara ruri,dagawa tayi ta ga junainah neh,ooooh ni rahma tace sannan ta amsa da sallama,bayan junainah ta amsa neh ta kuma dora wa da cewa wallahi ni babu ruwa na dake,,,,,,,katse ta umma tayi da cewa sannu sarkin korafi,wato ke baki rasa abin fada koh wallahi kin fiye hayaniya haba,kuma dai menene cewar nainah,ai kinsan baki da gaskiya neh sai sa,dariya umma tayi sannan tace Allah ya huci zuciyarki mata agidan doctor sadeeq,murmushi nainah tayi sannan tace uhmmmm dont try to manipulate me kam,domin fushi nake,ki dai yi hakuri zanzo gidanki ranan monday idan na gama registration da sauri,okay Allah dai yasa ameen kawai umma tace don bata son jan zance da yawa,murmushi tayi bayan ta kashe wayar sannan tace wannan matar big case ce,ajiyar zuciya tayi kawai,shima dai mukhtar din bai amsata ba don yasan ba dashi take ba,ko yayi magana ba amsa shi za tayi ba,dan Allah ya mukhtar tsaya coldstone na siya ice cream,tsayawa yayi don shi kam sulhu yake nema,tare suka jera suka shiga,ice cream ya siya mata four cups kuma different flavour,sannan suka karasa gida,mamy neh ta rugumeta da ta fito daga motar tana mata sannu da hanya sannan suka karasa cikin gida suka bar mukhtar da akwati,zama sukayi suna ta fira kaman sun shekara basu hadu ba sannan daga baya ta shiga daki tayi sallar magrib kafin ta shiga wanka,tana fitowa ta shafa lotion dinta da turarukan jiki kafin tayi sallar isha don har an kabbara a masallancin layin tana taji,bayan ta idar neh ta wuce falo sukayi dinner,tana ci tana santi tana cema mamy tayi missing gida domin chan sai wani abincin larabawa ake,ita kuwa baza ta iya cin wannan kayan jagwalgwalo ba,dariya Abba da mukhtar suka rinka mata,mukhtar na cewa matsalar kai yan kauye birni kenan,dariya tayi taje eh taji,haka suka ci abincinsu cikin jin dadi daga baya kowa ya tafi dakinsa,barin ma umma da ta gaji,tana zuwa dakinta alwala tayi sannan ta hau saman gado,wayarta neh ya fara kara,Allahu akbar,wanene wannan neh,tashi tayi ta dau wayar tare da amsawa,amincin Allah ya tabbata agareki tare da ni'imoninsa,murmushi tayi azuciyarta tace wannan wani dan sabon dan kakale ne nasamu,ameen tare da kaima ta fada ataikaice,nasan baki gane wa ke magana ba,ni sunana ismail turaki,murmushi tayi sannan tace okayyyyyyyyy nah tuna kam yanxu,yaaa ka isa lagos din lafiya,lafiya lau Alhamdulilaah,ya gida ya iyayenmu ya tambaya, duk lafiya tace masa,masha Allah nasan barci zakiyi don kin gaji so bari nah barki ki kwanta daman dai ina son naji muryarki neh kafin nima dai na kwanta.Murmushi tayi sannan tace ta gode sai da safe ta fada ataikaice kafin ta ajiye wayar,addua tayi ta shafe jikinta sannan ta kwanta barci.
YOU ARE READING
Mafarkinsa Nake 💞💞💞
RomanceNi wallahi kullum sai nayi mafarkinsa amma bana ganin fuskarsa, kullum ce min yake ni yake so amma yaki nuna min fuskarsa na gani wai sai rannan da nace ina sonsa kafin zai bayyana min kansa. Ni kuma tsoro nake kar nje na gaya ma aljani ina sonsa n...